(19)

23 2 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Saturday, 6th September, 2020.

(19)

Ta taya ta zige rigar suka fito.suna zuwa suka baiwa diyan Nan alewa sannan suka zauna.shi dai Maina se ya koma dakali yayi zaune Yana kallon su.kayan sun wa Mairo kyau fiye da zato..

Sallama akayo wata yarinya da zatayi sa'ar Hasi ta shigo .. ko kafin ta fadi abunda za'a bata har ta fara yaba kayan Mairo da Hasi..ce take .."Kai wannan kayan Sallar ku ne Amman ..gaskiya wannan kayan sun yi .."

Nan ta gama zancen ta ta siyi abunda zata siya.futar ta keda wuya se ga yara suna ta tururwar kallon kayan Mairo da Hasi.ita ko Hasi se buda hanci take irin sunyi daban din nan..

Abunka da kauye ,har wata ya taje ta fasa wa uwarta kuka ,kan lallai tana son irin kayan Sallar su Mairo na gayu.nan uwar ta yabo wani ragargajajjen hijabi ta fado gunsu Mairo taga kayan.kai ba yaran ba ,hatta ita da zata samu irin kayan da ta kere wa sa'a a cikin faccalolin ta da kishiyoyi..

Maina dai be gama Shan mamaki ba ,seda wata yarinya ta shigo tace .."Mairo,wai inji Babar mu inkin cire Zaki bamu aron rigar ki?"

Maina ya sau baki,Hasi kuwa tayi charaf tace .."Ah ah bammu bada wa .."

Maina kawai se yaga toh ya gwada baza kayan ya gani ko za'a siye su Mana,Kiran Mairo yayi daki yace da ita ,ki zabi Wanda kike so ,ki Kara wa Hasi se na Hansai da salame ,sauran Zan daura Miki igiya muga ko zasu saidu..

Nan Mairo ta zabar musu ..kan kuce mi har Maina ya Nemo igiya ya kulla a jikin tiredar ya baza kala biyar yace gashi nan Mairo na Saida su suma Duk me so,wallahi Kamar wasa aka ruga fadowa bako sallama ana daukan riga,da Dan siket ,Kai kan kwabo har an fara fada akan wata riga..

Maina ya koma daki ya irga rigunan kaf sannan ya sake fiddo biyar,wallahi kafin kwana biyu har hayin gaban gabari an San da maganar kayan gayu na babban gida ..

Allah ya Sanya wa kayan Albarka sosai har fiye da zato,dole Maina ya zauna a gaban kayan ,su Mairo suna ji da shagon su ,Maina naji da kayan gayu.

Naira tamanin tamanin komai a kullin..haka kan sati biyu Kaya sun kare..

A cikin rigunan Mairo ,da wadda take da Yar 🧸 a gaban rigar,daga bayan keyar teddy din Kuma aljihu ne,kawai ta balle Yar bebin Kamar yadda take fada ,shine ta lura da aljihun..tana budewa se taga wata sarka ta yara harda zilin ta..se kawai ta Sanya a wuyan ta.

Maina baya nan dama,yaje gun Ubale da ya aiko a Kira sa.dan haka yaci Karo da Mairo da wannan sarka a wuyan ta,kallon sarkar yayi yaga a idon sa ta dauki idanun sa.se yace da ita .."Mairo a Ina kika samu wannan Yar wuyar?"

Kallon wuyan ta tayi tace .."yo ba a tsintuwar jikin rigar gayu ta bane ?"

Cewa yayi "Ciro muga?"

Ciro wa tayi ta Mika Mai,Bata tsaya bi ta kanta ba tayi gaba abun ta..

***************

Kimanin mako Ukku da dawowar Maina,shiru make hi be ko Kara magana akan gidan sarki ba.ubake yayi magana ,Innaji tayi,Inna Mari ma tayi,Duk Wanda yayi magana se yace mako hudu yazo yi ai..

Haka Nan yake ta cin Karen sa babu babbaka,sedai Ila me kura ya kawo balas kullun Maina ya amshe ya Sanya a asusun sa..

Rana batta karya,a dole sadda ya cike mako hudu ya hada Kaya ya yayi jiki se Garin Burum,ba yadda ya iya ,haka Nan ya nufi gidan sarki,Amman tun da wuri se yayi bangaren Dan sarki ,Chan kuwa ya iske shi kwance ba lafiya,Nan ma ne yaji cewa ai wanchan karon ma kwanciyar yayi shi yasa ya dade a tsare,Nan Maina yayi ta yan tambayoyi har yace ze koma gida ze Taya da magani..

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now