(3)

119 11 0
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

1st june. 2020

(3)

______________________

Haka dai da duk abun da ya sawwaka,duk dai dan a taru a rufawa juna asiri..

____________________

Bayan fitar Mairo bata tsaya ko ina ba ,se gidan karban sadaka ,nan gidan wani me hali a garin me suna ..Alhaji sale mai robobi..

Chan ta tarar da su Talan (Talatu) kawar ta yar gidan Abuwa ,ta tsarar mata layi daga gaba gaba,kamar dai yadda suka saba,duk wadda ta ruga zuwa zata tare wa kawar ta layi,kuma ba Wanda ya isa ya kwace,ko da ma dai a gun Talan ne kawai baya kwatuwa,Amman Mairo kam! Inaaa,yo ita ma ji take da kanta, dan Mairo irin yaran nan ne masu shiru shiru ,gashi batta da karfi ko na minti guda,batta da kazar kazar ,haka nan dai take salalo salalo..

Mairon ma dai Hasina ke tare mata fada,ko Talan din ,yo ina ma ita ina Jan fadan wai?

Ai ko fadan ne ya hada da ita, kowa ya San cewa tsokanar ta akai,dan ita bata ma kula mutane sosai..

Daman ma fadan baya wuce in samarin bakin layi sun tare ta suna so,shine fa zata fara kwalla ko ma kuka,toh duk ta kuskura ta fada wa Hasina (kanwar ta me bi mata) haka zata tafi ta tsare wanda ya kula mata addar ta Mairo ..

Se dai fa Inna tayi ta faman zabga wa Hasina fada,dan kuwa ita Hasina Jan wuya ce,batta da daukar raini ko kadan,ga azabar masifa.

Har inna kance.. "Yo ke Hasi ina ne wai kikai wannan gadon na masifa?,yo wai ke fada baya miki wahala?"

Ita dai Hasi sedai ta bawa inna Hakuri,kuma tana fita wani ko wata ta sake tabo ta tayi fadan ta,gata da karfi,dan dai irin ta da wanda suka dan fita, yanzu zata murkushe mutum ta haye kan shi ta mai bugun kashi.

A takaice ma dai,yan gidan su basa tabuwa kodan Bala'in Hasi ,sedai kuma wanda tsautsayi ya biyo da shi ,me Rabon shan bugu kenan..

___________
Gidan karban sadaqa

A chan layin be jima ba ya zo kan su Mairo,Dan haka suna karba suka izo kayan su a kawunan su suka wuto gida..

A hanya ne Talan tace wa Mairo .."yo ban fadi maki ba,dazu muka hadu da Maina,naje Hayin su,diba nan ki gani, harda murtala ya ban yace in sai Dan Suluf"..

Tana yar dariya take nuna wa Mairo naira ashirin din da Mainan ya bata, wadda a habar yakunannan gyalen ta ta kwanto ta,hallau kuma ta sake since habar zanin ta tana cewa .."Ke kuwa Murtala biyu ya ban yace in baki  hallau kuma yace yana gaida ki..."

Kallon Talan din Mairo tayi tana ,.. "Allah Talan,ince kin ce mun gode? "

Cewa Talan tayi .."iyy man,godiya buhu buhu ma ..ungo nan anshi naki ,su Hansai sun samu na siyan Dan suluf din suma .." (Da yake su Mairo sun shaku sosai da yan uwan ta,ko cingwam dayan su ya samu ko a ina ne se ya raba da sauran,koda dan minini ne za'a raba shi..

MAIRO

Girgiza kan ta tayi ..Sannan tace.."Ai  banni ansa ,yo so kike Innar mu ta mun bugun tsiya inna ansa?"

Ci gaba tayi da fadin "se dai in ke ki adana su a gun ki,inna gaya wa innar mu ta yadda se mu sayi Dan suluf din .."

Washe baki Talan tayi tana cewa .."Ai harda awarar Fiddau ma.."

Da haka suka ci gaba da tafiya suna yan hirarrakin su ,har suka iso gida ana gab da kiran sallah.nan kowa ta shige gidan su ..

_____________

WAI SHIN WAYE MAINA ?

Maina Ubale,Da ne ga Malam Ubale sa'idu ,wanda suke mazauna Burum din,dan gaba daya Matan Malam Ubale ma yan nan cikin kauyen Burum ne ,Tunda yayi aure aure sakamakon rashin samun haihuwa..

Se daga baya sannan Allah ya nufe shi da auren Macen da ta sha fama sannan ta Haifa wa Ubale yaro namiji,wannan yaron shine Maina,kuma tun daga kanshi ba macen da ta sake ko da batan wata a gidan Ubale..

Yanzu haka Matan sa biyu suka rage ,sakamakon guduwa da Matan keyi suce shi Ubale baya haihuwa ..

Innar Maina me suna Inna Mariya ,ake ce mata Inna Mari,se kuma Inna Salmai ,sune Matan Malam Ubale Wanda suke zaune a Hayin gwarmai ,gidan su gida ne na Gandu,dan yan uwan Malam Ubale da iyayen shi duk wuri daya suke zaune..

Ko da yake ba laifi ana dan zaman lafiya,se dai kun San duk inda taron mata yayi yawa,kuma aka hada da kishiyoyi da faccalolin wannan,se an samu dan kyashi ne ,hassada ce,bakin ciki da dan gutsuri tsoma ..

Toh hakan dai ce ta kasance a gidan su Ubale,kar ma azo batun kyashin Maina da mafi yawancin yan gidan suke yi..dan maina dan gata ne sosai a gun Iyayen shi da kakannin shi.

Yo da ne kwalli daya kamar naman miya,kuma ballaifi Ubale yana da yar rumfar sa a bakin kasuwa,toh yana samu ballaifi,hakan ne kuma yasa shi Maina yake samun gata da jin dadin da har ya janyo mai sa ido da hassada hadi da kyashi,

ko da yake ma a bayan fage suke yin abun nasu su masu nuna kyashin,kadan ne wanda basa iya boyewa.

Tunda Malam sa'idu na nan da rai,wato Uban shi Ubale kenan ,kuma kakan Maina.matar Malam Sa'idu kuma Inna Gaji sunan ta,ita kuma Babar Ubale kuma kakar Maina..

Kakanin Maina suna son shi kuma suna ji da shi sosai,yo jikan nasu kwalli daya daga gun Ubale,in basu soshi ba wa zasu so?

__________

Maina Ubale dogon saurayi,kyakkyawan bafillace ,dan Uwar shi Inna Mari irin kyawawan fulanin nan ne ,cikin hikimar Allah se gashi Maina yayo kamar innar sa sak,dan yama fi kama da mata,se dan fadin jiki na uban shi Ubale da ya yo..Dan ita Inna Mari irin siraran Matan nan ne ..

Maina ya kasance dan gata ,Amman duk da haka be zauna haka nan ba,dan ko a yanzu da gatan nashi yana zama a rumfar Ubale ,sannan yana tura kurar ruwa a zagayen Hayin su zuwa Hayin kasa ,kuma Alhamdulillah yana samun yan kudin shi wanda yake Tara wa..

Dalilin tura kura ya sanya jikin shi yabi ya murmurde kai kana ganin shi kaga mai suffar karfi kuma hakan ba karamin kyau ya mashi ba..

Maina Ubale kenan ..

Se kuma mun hadu a kashi na gaba ..

Kuyi vote,kuyi like kuyi comment sannan kuyi sharing . .... .

TBC...

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now