(35) The end

89 6 1
                                    

WATA KADDARAR

           BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD @Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

Monday, 16th November. 2020

(35)

***************

Dakin taro ne na shaharraren TV station dinnan me suna "T.N.A". wanda su suke daukar wannan program din Wanda ake yin shi live.

Tambayoyi ake Mata akan littafin da ta wallafa,da dalilin da yasa ta wallafa shi.

Ga yadda tattaunawar ta kasance ..

"Assalamualaikum masu kallo da Kuma sauraren mu,barkan mu da sake kasancewa da ku cikin wani sabon Shirin ku me farin jini,wato shirin *"Madubi"*..

Kamar kullun sunana Ummkulthum Ahmad wadda na saba gabatarwa.

A yau komar mu tayi babban kamu,Dan ta kamo mana murubuciyar  shaharraren littafin nan me taken "How to change your thinking"..ba tare da na cika ku da zance ba,Bari muji ta bakin Hajiya.

"Hajiya Barka da zuwa .."

"Barka dai",Mairo ta fada tana dan murmushi.."

*T.v*{ "Da farko dai zamu so jin cikakken tarihin bakuwar tamu.."

*Mairo*{ ."Assalamualaikum warahmatullah,nidai sunana Mairo iro dan fillo,an haife ni a shekarar (      ),Kuma Haifaffiyar Jihar (.     ) A can cikin Kauyen Burum,na fara primary a chan Kauyen Burum,Amman saboda yanayin rayuwar mu,ban samu na karasa ba,daga Nan nayi aure,Ina da shekaru 13 a duniya,shekara kamar (biyar) da aure na,muka bar Kauyen Burum nida me Gidana,muka kamo hanya ta zuwa inda bamu ma sani ba ,munyi tsaye tsaye a garuruwa da yawa ,daga karshe Kano ta dabo,ita ce madakatar mu,anan mukai rayuwa,har nayi secondary School na gama, sannan nayi jami'ar Bayero unibasiti kano,inda na karanci bangaren ilimin kimiyar siyasa  wato Political science ..a iya cewa wannan shine takaitaccen tarihina .."

*T.v*{ ."Toh me sauraro zeso yaji yadda akai har kika kirkiri wannan littafi,Wanda ya dauki hankullan al'umma ,Kuma kika wallafa shi,Duba da cewa naga ba bangaren karatun ki bane ba,wala'allah inda ya danganci harkokin siyasa,se ace ai Daman nan ta karanta,shin ya ya abun yake?"

*Mairo*(.."Eh tabbas wannan ba bangaren da na karanta bane,Amman ai shi rubutu misali,ra'ayi ne,Kuma dai ya danganta da dalilin da yasa har zuciya taji tana bukatar yin rubutun.."

*TV*("Toh ko zamu san mene ne asalin abunda yaja hankalin ki har kika rubuta wannan littafi?"

Mairo ce ta kalli Maina Wanda yake zaune cikin kayatattun kayan sa ,ya cika ko ina Malam,se daukar ido yake.wani salihin murmushi yayi Mata wanda dole ta maida mishi,wannan murmushin ya kashe zuciyar jama'a masu kallo da yawa,ga wanda suke ganin cewa Maina yayi musu,kishi ma ya cika zuciyar su.

Dan gyaran murya tayi tace.."Dalilin da yasa na rubuta wannan littafi shine,duba da irin yanayin rayuwar mu da muka taso na talauci da duhun Kai,tunda bamu taba hqngo cewa akwai irin wannan rayuwar ba seda Allah yayimukq fito daga Kauyen mu,da wahalhalun da muka tsinci kan mu ciki a rayuwa,ga rashin wayewa ma tunda daga wata jiha muke,chan kauye ne,Kuma Kauyen kayayau ma, wanda muka zo inda rayuwa ta bambamta.amman Duk da haka muka jajirce bamu karaya ba,Haka mukai ta faman bi da kan mu duk yadda rayuwa tazo Mana.

Sana'a ba irin wacce me gidana beyi ba Ina kallon shi,Kama daga Turin kurar ruwa,siyar da rake,gurji,agwaluma,yalo,Kama daga kan,wanki, kaninkanci,lebura zuwa kwasar bola.duk seda yayi da Wanda ban samu da ar fado su ba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 12, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WATA KADDARARWhere stories live. Discover now