part 2 page 131-135

348 30 0
                                    

*LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐

Dedicated to *My lovelly Mum*



*131-135*

Alhamdulilah jiki Alhamdulilah wallahi sai godiyar ubangiji. Nagode da addu'ar ku fans musammam yan group din Zama na Amana 2 da khaleesar haidar. Nagode Allah ya bar zumumci Ameen

 Wannan shafin nakune na duk mai suma Hauwa'u, Jidda, Yasmeen kuyi yadda kuke so dashi duk dan sbd da jin dadin Autar mu
Hauwa yasmeen

Tin daga ranar Aslam bai kara kiran ta ba dan yai fushi sosai duk da yana son yaji ta sai dauriya da yake sai dai ko ya bugi cikin Momy ko in suna waya yana musu labe.

Sosai Asma'u ta damu, amman kuma tana cikin jin dadi da kula da hutu.

Mami bata barin ta da kadaicin da zata zzauna tinani.
Ba abinda take a gida daga wanka sai bacci. Ko yaran sai zasu sha mama ake kawo mata su.

Gyara kuwa da wanka sosai Mami ke mata dan jkin ta har ya saba gashi Mami ta ce wata ukun nan sai an mata wanka dan haihuwar fari ce kuma ya'ya biyu dole a gyara ta in ba haka ba faba zata ji jiki.

Sai anan ta gane manufar da akace sun ka je gida. Dan ta godewa Momy da tace lallai lallai sai ta zo kano,
Tana shan gyara banda cima da Mami ta canja mata.

Sosai ake kula da ita. Kuma akai akai Zainab da Nusaiba da Maimuna suna zuwa duba ta.

Sai dai tausayin Aslam da take ji dan ta san waye Aslma bama akan bukatar sa. Baya iya jure rashin ta gashi wai sai tai wata uku abin da kamar mamaki tasan yanzu yana can yanda takura.

Abinda yafi tsaya mata ma arai kar yaje yai auren da yace zai yi da ya zatai zatai sharing din sa da wata in ta a har kuka tkeyi.

Aslam kuwa yana can yana ta lisafin arba'in.
Ranar da sukai Arba'in a ranar ya dauki waya ya kira ta dan a lokacin ya huce.

Tana dagawa, ya farai mata sururai na irin murna da yake zata dawo.

Shiru tayi a ranta ta ce,
"Bayan ance sai nayi wata uku "

"Ba kyaji nane?"
Y fada.

"Uhmm ina ji."
"Amman kikai shiru. Kiyi hakuri ban daina kiran ki dan komai ba sai dan gudun kar na shiga wani hali in na kira ki. Wallahi da kyar nake iya bacci ina missing naki Husnah."

Ajiyar zuciya ta sauke. Ta ce,
"Sai hakuri, tinda kaga su Momy sunce sai nayi wata uku zan dawo. Ka kara hakuri nima ina kewar ka."

Ido Aslam ya zaro, ya ce,
"Wata uku."

Kai ta gyada. Wayar ya kashe a ransa ya ce,
"Wallahi bazan iya ba matata zan dauko."

Baiwa Momy maganar ba ma ya fara shirin tafiya kano.

Yau ya dira a Kano. Gida yayi kai tsaye.
Mami bata nan taje unguwa gida ya rage daga Asma'u dake dakin ta tana bacci ita da yaran ta. sai mai kula da yaran a kasa.

Yana zuwa suka gaisa ya tambayi Mami aka ce bata nan.
Sama ya hau dakin Asma'u ya shiga. Tana kwance, tana bacci tana sanye farin less dinkin riga da siket

Rayuwar  Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔Where stories live. Discover now