Part 1 page 131-135

427 21 0
                                    

 *LABARIN RAYUWAR*

*Asma'u Husnah*


Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*


🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*


Dedicated to *My Lovelly Momy*





*131-135*




Asma'u kuwa sai Magariba ta tashi. Tana tashi taji kafar ta saki.

Mikewa tayi ta haye sama tai alwala tai sallah. Tana idarwa Yaa Aslam ya kira ta.

Kafar ya tambaye ta ta ce,
"Ai Yaa Aslam sai da aka kara gyara min ashe bai gyaru ba."

"Ayyah sorry my dear da zafi ko. Sorry."
"Yaa Aslam ai zafi har ba'a magana."

"Sannu toh!"
Daga haka suka cigaba da hirar su.

Yau takanas Maimuna ta wanko.kafa tazo gun Asma'u.

Dawowar Asma'u kenan daga Asibiti aka zo akace ta yi bakuwa.

Sakowa tayi. Wa zata gani in ba Maimuna ba. Cikin shigar ta, ta riga da zani sai hijab din ta iya gwiwa.

Asma'u da murna ta karasa wajen ta ce,
"Lallai yau Maimuna ce a gidan namu."

Maimuna tai murmushi ta ce,
"To ina kewar ki ba dole na zo mu gaisa ba."

Gaisawa sukai sannan Asma'u ta kawo musu abinci suka ci suka koshi.

Wajen Mami ta kai ta suka gaisa sannan tace tafiya zatayi.

Dubu biyar Mami ta bata tana mata godiyar ziyar da ta kawo musu.

Har waje ta rakata dan sai da ta hau Napep sannan sukai sallama ta juya gida.

Wata mota ta gani wacce kwanan nan kusan kullum sai ta ganta a layin ta rasa motar wace, ga bakin glass da take dashi.

Motar ta kuma kalla ta shige gida abinta. Sabir dake cikin motar ya yi murmushi ganin ta kallon da ta tsaya yiwa motar.

Ya tabbata ta fara gane da zaman motar a wajen.

Motar ya tayar ya bar unguwar ransa fari tas yaga abinda yake son gani.

Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah. Yau gashi sauran wata uku su Asma'u su kammala karatun su.

Yau ma kamar ko da yaushe da yake asabar ce suna zaune, a falo ita da Dady

Dady ne ya kalle ta ya ce,
" *Husnah* ba abinda kike bukata a kara siya miki."

Kallon Dady tayi ta ce,
"Dady da sauran lokaci fa."

"Haka ne, amman na fison komai na gama shi da wuri dan bamu san me lokaci zai bayar ba "

"Haka ne Dady. Amman ni bana bukatar komai."

"Kin tabbata?"
"Eh Dady."

"Shikenan na miki transfer din kudi ta account din ki kingan su."

Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah!"

"Ki duba wayar ki, zaki gani. Dan haka ki ajiye in lokacin bikin yazo in kina bukatar kudi ki huta ba sai kin hau tambayar Mami ko Yayun naki ba."

Murmushi tayi ta ce,
"In ban tambaye su ba ai ina da Dady ko?"

"haka ne! Kina da Ni amman in ina nan ba."

Murmushi tayi ta ce,
"Dady tafiya zaka yi ne?"

Kai ya girgiza ya ce,
"Ko daya in na mutu nake nufi."

Rayuwar  Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔Where stories live. Discover now