part 1 page 6-10

719 45 0
                                    

*ASMA'U HUSNAH*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾



Page *6-10*



*Ummu nah* Abar alfahari na ina son ki da yawa Allah bar min ke. Allah ja da ranki farin cikina.*



*MANZON ALLAH (SAW)*
*Yace Kada kayi sallah a makabarta
Kada ku zauna akan kabari*




************
Tana shiga dakinta! Ta shige bandaki tayo alwala. Kayan jikin ta ta cire ta saka kayan bacci.

Sky blue din riga da wando ne, wanda suke hade da hular su.

Kan gadonta, ta haye tana me yin Bismillah.

Wayarta ta sa hannu ta zaro daga karkashi filon ta.

Kunna ta tayi, Ido ta zaro, tare da daura hannun ta akan bakin ta, missed call din shi ta gani guda biyar.

Murmushi tayi tana girgiza kanta.
Tana kokarin kira sai ga kiran sa nan ya shigo.

Murmushi tayi, ta dauka.

Shiru sukayi ba wanda yace kala. Sun dauki wajen minti goma a haka, Sai numfashin su dake tashi kawai.

Ido ta lumshe, Tana me tunanin kyakyawar fuskar sa.

"Baby nah!"
Yayi maganar da wata irin murya. Dan numfashin ta dake tashi ji yake kamar a jikin sa dumin sa ke sauka.

Kiran sunan ta da yayi shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.

"Na'am!"
Ta amsa da wata murya me rikita me sauraron ta.

"Baby na ina kika shiga, duk na rikice. Gashi number su Mami na kira duk sunki shiga."

Numfashi ta sauke,
"Ayyah Yayana Dan Allah kayi hakuri, ina wajen Dady nah ne."

Ajiyar zuciya ya sauke,
"Dady ya dawo kenan."

Itama ajiyar zuciyar ta sauke, tare da yin murmushi.
"Eh!"

"Ki gaishe shi."
Ido ta lumshe,
"Zai ji."

Murya ya kara yin kasa da ita,
"Baby na son ki zai haukatar dani fa."

Ido ta bude da sauri, tare da zaro su ta mike zaune.
"Ya Salam Yayana tayaya?"

Wata ajiyar zuciyar ya sauke dan duk lokacin da *Asma'u* na magana tana kashe masa jiki ne.

" *Husnah* son ki yayi mun kamu sosai. Baki ji yadda naji dana kira bakya nan ba. wallahi *Husnah* nasan bazan taba daina son ki ba."

Murmushi tayi, tare da sauke ajiyar zuciya.
"Shine kuma zai haukatar da kai."

Tayi maganar cikin shagwaba.
"Baki ji yadda naji a time din bane."

Kai ta girgiza tana murmushi.
"To am sorry Yayana Banyi dan na bata maka ba."

"Kar ki damu nasan da haka. Nasan yanzu kuma ana gun Dady mantawa nayi na neme ki."

Murmushi tayi. Ta lumshe idon ta, dan yana da saurin fahimta da bawa mutum uzuri.

"Nagode da fahimta ta da kayi."
"Nagode da son da kike min."

Sukayi murmushi a tare.
"To Baby kije kiyi
alwala kiyi addua ki kwanta."

"Toh!"
ta fada tana tashi daga zaune da take. A speaker ta saka wayar ta wuce ban daki.

Rayuwar  Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔Where stories live. Discover now