part 1 page 76-80

279 20 0
                                    

 *LABARIN RAYUWAR*
*ASMA'U HUSNAH*


By *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*

Dedicated to *My Life. My momy*


76-80

*Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa: *"Kuyi Aiki Domin Kowwa Ana Saukake shi ya Zuwa Abinda Aka Halicceshi Donshi ne"* (Bukhari da Muslim).*



Ranar alhamis da wuri ta gama komai ta shirya tayi dakin Dady.

Karfe takwas da arbain ta gama komai ta shiga dakin Yaya Buhari.

Gaisawa sukai kawai ta fita duk dan kar ta makara.

Shi kansa yau yasha mamakin ganin Asma'u bata tsaya jan magana ba.

Baba ma da ya gama shiryawa ita kawai yake jira tana shiga ya tada mota suka nufi makaranta.

Suna cikin tafiya motar ta tsaya. Fita Baba yayi Ya taba motar ya dawo amman shiru.

Sai da yafita sau uku ana hudun Asma'u ta ce,
"Baba me ya samu motar."

Baba ya ce,
"Asma'u kinsan ance karfen nasara bai da tabbas motar nan lafiya muku fito amman kinga ta tsaya taki tashi."

Fitowa tayi ta duba agogo tara saura minti biyar.

Waya Baba ya dauka ya kira mai gyara motocin gida ya fada masa inda yake

Kallon sa Asma'u tayi ta ce,
"Baba bari na hau napep dan na makara gashi zanyi submitting aasignment "

"To bari na tsayar miki da Napep din.'

"Aah Baba na gode."
Ta fada tana dan matsawa.

Mamaki take ganin karfe tara amman ji yan makaranta sai zirga zirga suke bama maza yan makarantun gwamnati.

Duk Napep din da zai zo a cike yake zuwa.

Wata Mota ce ta tsaya a gaban ta. Matsawa Asma'u tayi.

Kara binta akai ta kuma matsawa. Fitowa yayi daga cikin motar.

Wani hadaden saurayi ne ya fito. Fari ne, yana sanye da Ash kalar shadda kafar sa da bakin takalmi haka hannun sa daure da bakin agogo.

Kansa bbabu hula sai gashi dake kwace luf luf. Yana da idanu, haka nan hancin sa dogone har baki.

Karasawa yayi gun ta cikin nutsuwa ya ce,
"Assalamu Alaikum."

"Wa'aikulum salam!"
Ta fada tana dan matsawa daga wajen.

Kara bin ta yayi ya ce,
"En mata ina zaki?"

Ko kallon sa batai ba ta fara tsaida wani Napep.

Bai tsaya ba sakomakon cikar da yake.

"Naga kamar makaranta zaki kizo na rage miki hanya."
Dagowa tayi ta watsa masa wani irin kallon sannan ta matsa wajen wani napep da ta tsayar.

Kallon ta yayi har ta shige ciki sannan yayi murmushi ya shiga motar sa ya tafi.

Tana zuwa ta tadda har an yi submitting ga wani malamin yana musu lacturrle.

Kuka ta saka. tana zaune har lecturer ya fito.

Ta shiga ajin ta kifa kanta a benci tana cigaba da kuka.

Zainab ta matso gun ta tana bata hakuri sai ga. sir Sabir nan.

A haka ya shigo har ya gama lecture Asma'u bata dago ba.

Sai da zai fita ya dan matso gefen ta ya ce yana son ganin ta. Sannan ya tafi.

Rayuwar  Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔Where stories live. Discover now