part 1 page 126-130

225 17 0
                                    

 *LABARIN RAYUWAR*

*Asma'u Husnah*


Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*


🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*


Dedicated to *My Lovelly Momy*

*126-130*

An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace: “ *Manzon Allah(ﷺ)* Ya Hana Mutum Riqe Kwankwasonsa a Cikin Sallah”. *(Bukhari da Muslim)* a Lafazin Muslim: *“Shine Mmutum Ya Sanya Hannunsa a Qugunsa”.*_



Satin Yaa Aslam daya ya juya da shirye shiryen bikin su.

Dan yana komawa yasa Momy a gaba dole suje dubai su hadu kayan lefe.

Momy ta ce, ya bari lokaci ya kara karatowa. 'Ki yayi ya ce shidai su tafi.

A satin da ya dawo a satin suka tafi hado lefe.

Siyayya mai yawa da tsada sukayo. Duk abinda yaga ya burge shi ya ce a dauka. Haka nan Momy itama da ta iya zabe kaya masu kyau da tsada ta dinga siya.

Kaya sai da suka hada set akwati uku amma basu isa ba.

Sosai Momy ta hado mata kayan kwalliya da english wears dan ta san irin shigar da Asma'u take kuma tasan Asma'u yar gayu ce.

Haka suka dawo gida da niki nikin kaya. Shi Dady da ya gani ma cewa yayi sunyi kadan.

Kudi ya bayar a dado kayan da gwala gwalai. Har da Mota Dady ya ce a hada mata.

Momy tace,
"Dady ai ba yanzu za akai kayan ba."

Dady ya ce,
"Me za'a jira to. Kunga akai kaya ai sa rana kawai komai yazo daga baya."

Momy ta ce,
"To Dady in haka ne, ai kune masu kai kayan dan na fison maza suyi komai. Mu masha biki daga baya."

Dady ya ce,
"Zan fadawa su Alhaji Aliyu da Ahaji Abubakar da Dadyn Asma'un ma. Amman ni ban ga amfanin ajiye laifen ba akai musu kawai a huta."

Kai Mami ta gyada ita ma dai gara akai musun kawai. Amman kuma abu kusan shekara guda.

A cikin satin akai wa su Dady magana kan za a kawo kaya.

Dady cewa yayi baiyi wuri ba tinda abinda saura.

Amman Dadyn Aslam ya ce gara a kawo ai kamar yau ne.

Rana suka saka aka kai komai da komai. Aka sa ranar auren su nan da shekara daya.

Sai kayan lefe da aka kai. Kayan sosai Mami tayi fada wai sun zubo kaya da yawa.

Momy ta ce, to in bata kashewa Asma'u kudi ba wa zata kashe wa. Ta ce,
"Amina kada ki manta fa haka kawai ma kaya nake siyawa Asma'u bare kuma yanzu. Ki daina nuna min ke kika haifi Asma'u to wallahi ji nake kamar ni na haife ta. Kinsan dai uwa daya uba daya ba wasa bane."

Mami ta ce,
"Haka ne Yaya amman kun kashe kudi da yawa."

Momy ta ce,
"Akwai kayan fitar bikin su ma da za a aiko dan haka ki zuba idon zuwan su. Suna gun dinki na bada a dinka mata su."

"To Yaya angode Allah kara girma."

"Ameen! Zancen kayan kitchen kuma na gama da komai."

Haka suka gama wayar Mami na kara duba kayan da aka kawo.

Asma'u kuwa duk ji take kamar a mafarki wai kayan lefen ta ne.

Ji take kamar wasa kamar ba zata auri Yaa Aslam ba.

Rayuwar  Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔Where stories live. Discover now