Part 1 page 31-35

459 28 0
                                    

 *LABARIN RAYUWAR*
*ASMA'U HUSNAH*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*

🌐 *HAJWO* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

*Gidan Hakuri da juriya, tare da kawar da kai.*

Facebook @ Indabawa Hausa Novel
Wattpad @ Msindabawa
instagram @ Maryam S Indabawa



*31-35*

DEDICATED TO *MAMAH NAH* Allah kara miki lafiya da imani yasa ki gama lafiya.
*Ameen!*


*Manzon Allah (SAW) Yace "Kuyi sahur domin a cikin sahur akwai albarka"



Kamar ko yaushe tin asuba da ta tashi bata koma ba, bare yau da tasan suna da Sir Sabir.

Da wuri ta sauka kasa ta gama duk abinda ya kamata tayi. Ta dawo dakin ta tayi wanka ta shafe jikin ta da mai.

Durowar ta ta bude, ta tsaya kallon ta tayi minti Biyar a wajen sannan ta samu ta zaro wata bakar doguwar riga.

Hannun rigar an masa irin dinkin babbar riga da wani yadin material me multicolour (Kaloli daban daban.) Sai gaban rigar da aka masa ado da stone (duwatsu) aka jere wasu manyan jajayen stone (duwatsu) guda takwas suma.

Dago rigar tayi tana kare mata kallo, Ya Aslam ne ya siyo mata da yaje dubai. Juya ta ta kara yi, sannan ta dire akan gado.

Wani jan skin tied ta dauko sai jar bra da pant, saka su tayi a jikin ta. Sannan ta dauko rigar ta saka ta daure ta, ta ciki.

Jan hijab ta dauka wanda iya kar shi saman kirjin ta. Wani jan sandal ta dauko tasaka a kafar ta.

Sai bakar jaka da ta zuba abin da take bukata. A kan gado ta ajiye jakar da wayar ta.

Dakin Dady ta nufa, sai da yasa ta ci abinci sannan ya barta ya tafito.

Jakar ta ta dauka, sannan wayar ta.
Sakon Ya Haidar ta gani, budewa tayi tana murmushi.

" *Assalamu Alaikum*
Da fatan Baby na ta tashi lafiya, yasu Mami da Dady da Buhari. Ina fatan duk kuna lafiya.
Daman zan fada miki ne ina kan hanyar Kaduna, ina bukatar addu'ar ki, in na isa zan kira dan nasan yanzu ba kya kusa."

Murmushi tayi sannan ta nemi waje ta zauna.

Sakon fatan alheri da isa lafiya tayi masa sannan ta tura masa.

Ta jima tana tunani sannan ta tuna fa makaranta zata tafi.

Da gudu ta fita tayi dakin yayan ta. Bacci sa yake kamar kullum, gadon ta fada.

Da sauri ya mike,
"Ya Salam!'

Ya fada yana dafe kai. Murmushi ta saki,
"Ina kwana yayanah."

Harara ya wulla mata, ya mike ya shige ban daki. Zama tayi jiran sa.

Wayar ta ce tayi kara, ta dauka.
" *Asma'u* tara saura minti goma dai."

Ido ta zaro waje tana mikewa,
"Dan Allah da gaske,"

"Duba agogo ki gani."
"Innalillahi wainna illahir rajiun. Gani nan gani nan."

Ta fada tana nufar kofar ban dakin.
"Yayah! Yayah!"

Banza yayi mata. Kuka ta fashe masa dashi.
"Yayah!"

Ta fada cikin kukan. Shiru ya kara yi mata. Ya cigaba da cuda jikin sa.

Sai da ya gama sannan ya dauro shawul ya fito. Tana jikin kofar a tsaye.

Kallon ta yayi ya dauke kai ya fara goge jikin sa. Yana zama a gaban mudubi.

Rayuwar  Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔Where stories live. Discover now