part 2 page 111-115

382 26 2
                                    

*LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

?? *HAJOW* ??

Dedicated to *My lovelly Mum*



*111-115*

Da dare da wuri ta mishi girki kafin ya dawo, ta shige d'aki tana gama sallolinta tayi shirin kwanciya, doguwar riga ta saka iyakar gwiwa pink, mai santsi dabin jiki, tayi kyau sosai, mukulli ta saka ta rufe d'akinta ta haye gado tayi addu'a ta kwanta.

Aslam kuwa tinda ya fita da yamma yaje gidan Momy. Tambayar da Asma'u tayi ya amsa da tana lafiya.

Daga nan Asibiti ya biya, sai da akai magariba ya taho gida.

Yana driving ne amma zuciyar sa na can tunanin halin da Asma'u take ciki.

Bai son damuwar ta bai son bacin ranta. Dole ya san yadda zai  dawo mata da farin cikin ta.

Sanda ya isa gidan kamar yanda ya zata, tayi barci ko motsinta bai jiyo ba, d'akinshi ya shiga ya watsa ruwa yayi shirin kwanciya sannan ya fito ya zauna yaci abincin data girka mishi, hankalinshi duk naa wurinta harya gama.

A hankali ya murd'a Kofar d'akinta, jinta yayi a rufe, kamar yadda ya zata. komawa dakinshi yayi ya dauko makullanshi yazo ya bude a hankali ya tura kofar ya shiga.

K'arasawa yayi inda take, kasa d'auke idonshi yayi a kanta, a fili yake furta,
"Alhmdlh, Allah nagode maka da ka mallaka min Asma'u. Ya Allah ka nunamin ranar da Asma'u  zata gane irin son da nake mata," tsugunawa yayi saitin fuskarta yana tunanin yanzu da suna zaman lafiya ne zai kwanta da ita ne a kirjinshi yanajin lallausar fatar ta, shi kadai yasan yanayin da yakeji idan yana tare da Asma'u. Abinda ya dade yana fatan ya faru kenan.

Hannunshi yakai ya shafi fuskarta, ya d'aura hannunshi saman lebanta, bakin sa ya kai kan nata ya dan sumbace ta.

Mikewa yayi ya rufe kofar ya koma dakin sa.

Alwala ya kuma yi. Dan Kusan kwanan zaune yayi yana fad'ama Allah damuwarshi.

Washe da wuri ta gama masa duk abinda zai bukata sannan ta koma daki.

Sai da ta tabbata ya fita sannan ta fito ta gyara gidan

Daki ta koma tai wanka tai ado sosai a jikin ta da fuskar ta.

Bata san dalili ba yau dai ta tashi da farin ciki da son yin kwalliya.

Ta zauna ta karya. Kitchen ta shiga ta fara hada hadar abincin rana.

Fried rice tayi wacce ta wadata da hanta, tayi farfesun naman kaji, tayi cislow.

Cake ta kwaba tai baking sannan ta yi meat pie.

A daining ta jere su tayiwa wajen ado mai kyau.

Kitchen ta koma ta hada lemon kwakwa da madara ta saka dabinoi ta sa a firij.

Wanka ta kara tai Kwalliya sosai kamar amarya. ta saka wani papper less mai kyau da tsada wanda duk jikin sa stones ne da suka kara masa kyau sai daukar ido yake..

Red and black kala. Sosai tai kwalliya ta feshe jikin ta da turare mai kamshi sosai.

Dan kunne da sarka ta saka jajjaye, Babban falo ta koma ta zauna tana kallo.

Wajen karfe uku ta jiyo sallamar sa, amsawa tayi ba tare da ta dago ta kalle shi ba.

Shi kuwa tin da ya shigo ya zuba mata ido, dan yaga tai masa kyau.

Karasawa inda take ya zauna a gefen ta. Dagowa tayi ta zura masa manya manyan  idon ta masu dimauta shi, kallon sa ta tsaya yi, sosai yayi kyau.

Yana sanye cikin Sky blue din shadda yai kyau da shi.

Rayuwar  Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔Where stories live. Discover now