part 2 page 76-80

258 15 2
                                    

*LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writer's*

Dedicated to *My lovelly Mum*

*76-80*

*Na gaida ke sisto nah. Barrister Sadiya. Ina kaunar ki yar uwa. Allah ubangiji ya kara basira. Allah kawo miji na gari. Ameen*



Suna fita Aslam na shigowa gidan.
Parking mota yayi sannan ya kira Buhari.

Buhari da baya gida ya ce, Ya shiga zai sanar da Zainab.

Haka akai kuwa dan Zainab da kanta ta zo ta shiga dashi sai sannu da zuwa take masa.

Kan kace kabo an cika masa gaba da kaya sha da ci
Mamaki yake yadda take masa sai ya tuna Pretty yadda take ma abokan sa.

Har takai ta kawo ba mai zuwa gidan sa.
Zama tayi suna hira sama sama har Buhari ya dawo.

Da saurin sa ya kara sa gun sa yana masa barka da hanya.

Sai da suka gaisa yake tambayar sa ina Aiman.
Zainab ya tambaya Zainab ta ce, masa sun fita da Asma'u.

Sai a sannan Aslam ya ce,
"Buhari magana nazo muyi akan Husnah!"

Buhari ya ce,
"Ina ji."

Aslam ya ce,
"Wallahi Bro duk abinda ya faru ban san taya akai suka faru ba. Wai ni na guji Husnah yarinyar da bana tunanin zan iya rayuwa in ba da ita ba."

Kai ya dago ya kalli Buhari idon sa jajir ya ce,
"Ka taimaka ka shawon kan ta please."

Kai Buhari ya jin jina ya ce,
"Yaa Aslam kafi karfi komai a gun mu. To amman Asma'u ma dai gobe za'a kawo laifen ta nan da sati biyu biki."

A zabure ya mike, yana dafe kai da yaji yana masa lilo kamar zai fadi.

Buhari ne ya mike ya kama shi ya zaunar.
Kan sa ya jinjina da kujera, yana jin zuciyar sa kamar zata fashe.

Ya jima a haka sannan ya mike ya fice. Bin sa Buhari yayi yana kiran sa.

Amman ina bai ma san yana yi ba. Mota ya bude zai shiga Buhari yai saurin kamo shi.

Ciki ya maida shi dan ya fuskanci baya cikin haiyacin sa.

Daki ya kai shi ya ce ya kwanta. Tinda ya kwanta ya rasa me ke masa dadi.

Komai ya tsaya masa. Tayaya zai iya cigaba da rayuwa ba tare da Asma'u ba.

Kai ya tabbata itama Asma'u na son sa. Bari ta dawo yaji ta bakin ta.

Haka yai ta saka da warwara. Ji yake tamkar a mafarki duk abinda yake faruwa.

Wai shine zai rasa Asma'u anya kuwa.
Haka dai.

A bangaren Sabir kuwa Asma'u ya dinga bi dan yaga ina zata.

Gidan Maimuna yaga ta dosa. Shima duk da ta shiga sai da yai awanni sannan ya juya ya tafi.

Sai magariba sannan ta dawo gida.
Tana shiga kuma taji wata faduwar gaba.

Motar da bata sani ba ta gani. Kai ta dauke ta ce,
"Baki mukayi kenan."

Aiman ta dauko tana tafe tana masa wasa har ta shiga falo.

A falo suka baje dan anan suka tadda Zainab a zaune.

Kallon Zainab tayi ta ce,
"Momah da son dinta kun dawo."

"Mun dawon Momyn Dady ya gidan?"
"Lafiya."

Rayuwar  Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔Where stories live. Discover now