part 2 page 51-55

259 25 2
                                    

*LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*

Part *2*

Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*

🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writer's*

Dedicated to *My lovelly Mum*



*51-55*

don't Forget to vote

Da dare akai dinner inda yan mata sukai ankon wani pink material.

Amarya kuma ta saka golding kala, ango ma golding shadda ya saka.

Asama'u kuma ta saka Dark blue din material sosai tayi kyau.

Sir Sabir ma Blue shadda ya saka sai ya fito shima kamar angon Asma'u.

Anci ansha an yi liki, duk wanda yaga Asma'u sai ta burge shi dan komai nata da banne ga kyau ga jikin yana dauka.

Samarin wajen sun yaba da ita. Sir Sabir kuwa sai kareta yake.

Sai da sukaje suna liki ne, kuma sai kuka taga ga Mami ga Yaa Buhari gata ammn ba Dady.

Sosai ta sa mutane da yawa kuka a wajen.

Anyi taro lafiya an tashi lafiya.

Inda washe gari aka dau amarya aka kai ta gidan mijin ta dake rijiyar zaki.

Gida ne katon gaske dan Dady ne ya gina masa shi.

haka nan an zubawa Zainab kaya sosai. Sai da angwaye suka je sanna suka taho Asma'u na zolayar Zainab

Gida su Asma'u suka tafi da su Maimuna da Maryam.

Aka bar amarya da ango su kadai a gida.

A gida ma wasu dayawa duk sun tafi dan daga Momy sai matar Uncle Abubakar da Uncle iliyasu da Mama binta da zasu tafi gobe.

Washe gari da safe Mami ita ta aikawa da amarya da ango kayan kari.

Su Asma'u kuwa suna tare da kawayen ta. Lokacin su Hafsat da Maimuna sun shirya kayan su zasu tafi.

Sosai Asma'u ta hada musu kayan biki har da turmin atamfa.

Har gun Mami ta raka su sukai mata sallama.

Mami ta ce, a sa driver ya kai su gida. Haka ai kai kuwa.

Driver sshi ya kai ko wacce har gida. Gidan ya rage daga Asma'u sai Maryam da Nusaiba da ta ce baza su tafi ba.

Sai karfe daya suka shirya suka tafi gidan Amarya.

Suna zuwa suka tadda Amarya a falo taci kwalliya, sai kamshi take fitar wa.

Tana ganin su ta taro Asma'u sai da suka zauna kuma sai ta bata fuska.

Kallon ta Asma'u tayi ta ce,
"Lafiya?"

"Wallahi sis baki kyauta ba wai sai yanxu ni nayi zuciya."

Ta fada tana komawa gefen Maryam tana tambayar su ya gajiyar biki.

Dariya Maryam tai ta kalli Nusaiba ta ce,
"Yo ai ke zamuyi wa ya gajiya ko?"

Nusaiba ta ce,
"Lallai kam amman sai naga kamar ba ai komai ba."

Dariya Asma'u tayi ta ce,
"To ku ina ruwan ku."

Zainab ta ce,
"To waya fada muku sai kun gane anyi ko ba ai ba. Kowa da yanayin jikin sa haka nan wani yaji zafi wani bazai ji ba. Wani ya fitar da jini wani bai fitar wa. Wani tafiyar sa ta canja wani ba haka ba. Ke duk abinda zaku ji ana fadi ma wani vai san anayi ba. dan haka nidai baku jin baki na anan."

Rayuwar  Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔Where stories live. Discover now