Part 1 page 1-5

1.8K 83 1
                                    

*ASMA'U HUSNAH*

BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


🌐HAJOW📝🌐

👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾

*don't forget to follow and vote @ Msindabawa*


Page *1-5*



Da sunan Allah mai rahama da jin kai duk kan yabo ya tabbata ga Allah da kuma annabin sa Muhammad (SAW).

Ina godiya da Allah da ya bani ikon kammala *Koma kan mashekiya* Ya bani damar fara wani sabon littafi *ASMA'U HUSNAH*

To Alhamdulillah ina godiya ga rabbil samati wal ardi. Kuma ina rokan Allah ya bani ikon farawa lafiya tare da kammalawa lafiya
*Ameen*

Ya Allah ka jagorance ni wajen mika sakon da nake son mikawa. Allah ka shigen gaba.

Allah ka sa mu gama lafiya.
*Ameen!*

Wannan labarin kagage ne, ni na kirkire shi in kag yayi dai dai da rayuwar ki/ka akasi aka samu.

Da fatan zzai nishandar ya kuma fadakar da masu karatu.

*Nagode*

*Asma'u Husnah* littafinne da ya shafi soyayya, akwai abubuwan tausayi, da zalunci da yan matan suke da yawan yin sa nabin wajen malamai.*

*Banyi alkawarin baku posting kullun ba amman in lokaci ya samu zaku samu da yaddar Allah.*

Bari dai mu shiga daga ciki dan jin abinda ke ciki.

*THE WHOLE BOOK*

*DEDICATED TO MY LOVELLY MOMY*

Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana. Ameen Ya Allah.




Kwance take akan gadon ta. Katone, dakin ma kasan abin kalla ne.

Komai na ciki ruwan hoda ne. Gefen gadon durowa ce katuwa, sai mudubi, sai wani table dake gefe.

Littafai ne a cike akai. Gefen dama littafan isilamiyya daya gefen kuma na boko. Sai wata sofa dake gefe guda.

Sai wajen takalman ta, da jakun kuna, dakin sai kamshi yake ko ina a gyara tsab.

Sanyin AC ya ratsa shi, ga dadadan kamshi. Gefe wata kofa ce guda biyu daya wacce zata sada ka da cikin gidan ce. Daya kuma ta bandakin ta ne.

Idon ta a lumshe sai zuba murmushi take.

Baka ce, amman bakin ta me kyau ne irin sune black beauty. tana da hanci da idanu, da yar haba, sai kumatun ta dake a lubawa sanadin murmushin da take.

Girar ta cike take da gashi wanda yake a kwance ke kace gyara ta akayi ko zane akayi ma. Gashin kanta har gadon baya. Leben ta me kyau da taushi. Pink colour.

Magana take kasa kasa cikin zagin muryar ta mai dadin sauraro wacce duk wandan ya saurare ta sai yaso kara saurara ta.

Kunne na kasa dan jin me take cewa.
Muryar ya me sanyi da zaki naji tana cewa,

"Haba Yayana ai nima ka riga da ka dauken tawa zuciyar dan ban da wani abinda nake so da kauna da ya wuce kai."

Fulon dake gefen ta, shi ta ja jikin ta, ta rumgume shi. Tana sauraron maganar da ake fadi daga can ban garen.

Murmushi ta sake saki wanda ya har sai da hakoran ta farare masu kyau, wanda yake dauke da wushirya ya bayyana.

Magana ta fara cikin shagwaba kamar zatayi kuka.
"Wallahi, nima haka."

Rayuwar  Asma'u Husnah 1 & 2 Complete ✔Where stories live. Discover now