dacewa pg 70

21.1K 944 102
                                    

*_DACEWA_*
      _(when east meets west)_


_By_
_Mamuh geee_

*_Viawattpad@mamuhgee_*


*70*

Gurin 'daurin auren Yusuf yayita yimasa iskanci yayi banxa dashi dan shi yamatsu a 'daura yakoma dan jiyake fatarsa na ra'dadin son kasancewa da tata fatar.

Sha biyu aka 'daura auren   gurin reception ne ma ya'dan jima sbd tsayawa dayayi yabada komai na tafiyarsu dan so yake su wuce daganan.

Zaune take tana kallon wata diramar India a zeetv tanashan robar qarshe data rage mata ta furarta dan ta shanye biyu da safe.

Sanye takeda purple handless gown iya cinya Wanda itacema mai sauqi cikin kayan daya siyo mata.

Kallonta yayi tareda sakin murmushi ya ware mata hannuwa
Ta 'dauke kai taci gaba dashan furarta.

Qarasowa yayi ya zauna kusada ita tareda jawota jikinsa ta 'dago ta kallesa ya 'daga mata gira yana cewa,

How is my gorgeous doing?..

Lumshe ido tayi batareda ta amsa tana qara lafewa cikin jikinsa.


**********
Kwanansu uku a Kaduna suka wuce UK bayan yayi waya ya sanardasu ummi da mamy,

Soyayya da shaquwa ce mai qarfi tashiga tsakaninsu duk da kumbure kumbure da 'daure 'dauren fusriga
a yana nan saiyaci maganinta ya iya bida ita yanda takeso duk da ya lura da kawai rigimarta kesata yin hakan dan wasu lokutan mantawa take ta sake suyita soyayyarsu duk da taqi yarda da son mijinta yakamata.

Rayuwar jin da'di da wayewa suke a qasar dan dama irin rayuwar takeso wadda ko a ina mijinta zai iya nuna mata soyayya ba takura.,

Gashi ashe dama duk wayewa da ajin Jamaal acan bakomai suka ganiba sai anan  take ganin mamaki dan kusan kowane time fita yawo suke ko a ina suka maqale da juna tana cikin jikinsa
Nan take suka canza su duka dan harwata qasunbar kyau da kwanciyar hankali ya tara taqara masa wani kyau da kamala.

Ahankali cikinta ya'dan fito kadan duk da har lokacin bai gama tantace cikine da itaba..

Yau tun safe ya fita aiki dan anyi masa wayar ana  nemansa prison 'dinsu inda aka kawo su zeey aka rufe 'daurin rai da rai.

Sai 6 yadawo gida,

Zaune take tanashan milkshake sbd shi yayi mata replacing furarta.
Blue jins mini skirt ne a ajikinta wanda iyakacinsa qwatan cinyarta da farar handless rubber top ta kame gashinta gefen kanta ta nabba'a tana kallon wani series _the originals_ a tashar cwtv.

Qaran doorbell yasata miqe ta nufi qofar da cup a hannunta.

Jawota jikinsa yayi yana cewa,

God I love this gorgeous so much..

Zamewa tayi tareda juyowa ta kallesa tace,

Ina kaje kafita so early and you came back late.?

Kiss yakai mata abaki kafin ya nufi bedroom yana cewa,

Work.

Zamanta tayi a Palo taqi binsa taci gaba da kallonta..

Wayarsa daya bari a palon ta'dau ringing harta share ta amma ringing 'din ya dameta duk da bamai hayaniya bane.

'Daukar wayar tayi da niyyar kai masa taga sunan Yusuf ne saita  'daga kafin tayi magana yarigata da magana cikin dan takaici.

"" Jamaal how can you meet with that crazy ayeesha bayan nafada maka karkaje inanan zuwa cikin week 'dinnan I know how to handle yan iska irinsu now gashinan tafara blabbing nonsense wai she thinks she's 4 months pregnant and u are the fathe.....

DACEWA✅Where stories live. Discover now