dacewa pg68-69

11.9K 701 52
                                    

*_DACEWA_*
      _(when east meets west)_


_By_
_Mamuh geee_

*_Viawattpad@mamuhgee_*


*68-69*

Ranar kamu tun safe sukeje _blue rise beauty pal_,,
Tunda suka isa neesah taga robar furar habib yoghurt a hannun wata kyakkyawar budurwa agurin taji duk hankalinta yatashi furar take kwadayin sha..

Kallonta siyams tayi taga ta tsuke fuska murya qasa qasa tace,

Nee yayane naga sai yamutsa fuska kikeyi?

Qaramin tsaki taja ahankali tace,

Kamar karnaga furar nan naji yunwa nakeji sosai..

Asmy ta kalleta tareda 'yar daria tace,

Kai nee yaushe muka gamacin abinci muka fito kuma nagama sosai kikaci abincin dan ni har tsoro kika bani.

Murmushi amirah da akewa gyaran kai tayi batareda tace komaiba sbd itadai taga abinda ta hango..

Daqyar taga angama musu komai suka fito gurin da kanta ta kar6i driving daga siyams kai tsaye Habib ta nufa dasu tana parking tafita da kanta tashiga saigata ta fito da robobin kusan guda shida.

Kallon mamaki suka bita dashi ta miqawa siyams key takoma baya gurin asmy sbd amirah ce a seat 'din gaba.

Kafin sukai gida ta shanye roba biyu a mota 
Suna isama bayan taci abinci saidata kuma wasu biyun..

Cikin tsoro siyams tace,

Neesah wannan furan mai zaqi bakya gudun gurin period kisha wahala?

Asmy na tu6e rigarta tace,

Nima dai haka nagani after all kuma she's not used to all this things barema da yawa haka.

Shiru tayi tareda aje robar furar dake hannunta zuciyarta na tsinkewa dan saida asmy tayi maganar period ta tuna da bataiba last month da this Month.

Kallonta amirah tayi cikin tsokana tace,

Iyye neesah I think you're pregnant,,

Furar bakintace ta sarqeta a gigice tasaki tari tareda miqewa ta fa'da toilet sbd kamar harda amai zatayi.

Kallo suka bita dashi gaba 'dayansu tareda sakin dariyar farin ciki da tsokana.

Kasa aman tayi ta tsaya gaban madubin toilet 'din tana kallon fuskarta gabanta na tsananta bugu dan har wata rawa jikinta yakeyi.

Hawaye keson gangaro mata ta danne idanuwanta na kad'awa jajir,,

Da gaske cikine da ita?
Cikin Jamaal a jikinta???
Cikin qaninta??

Girgiza kai tafarayi da qarfi tana cewa,

Bazai yiyuba,,bazan bari kowama yasan da wannan abin kunyar ba agareta,,zubar dashi zanyi batareda ma ansan dashiba dan wlh bazata zauna da sauran mijin wataba..but how can i be pregnant in just one go..

'Daure fuska tayi tafito toilet 'din tareda ficewa bedroom 'din batareda takulasuba ta nufi bedroom 'din momyn amirah dan tun jiya suka dawo gidan sai angama biki kamar yanda sukayi lokacin bikinta.

Qarfe biyar aka tafi gurin kamu biki yayi dadi yayi kyau tareda tsari hakama 'yan matan Amarya ba qaramin burgewa sukai ba sbd kowacce ka kalla bazakaso 'dauke idanuwanka akantaba.

Neesah kuwa kusan ma tafi burge kowa duk da jikinta a sanyaye yake da zancen cikin dan idan ta tuno gabanta mummunar faduwa yakeyi.

Da daddare ma kafin su kwanta saidata kira nasir a waya yasiyo furar yakawo mata tasha kafin tasamu ta iya bacci.

DACEWA✅Where stories live. Discover now