dacewa pg 42-43

7.6K 486 16
                                    

*_DACEWA_*
     _(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*_Viawattpad@mamuhgee_*

*42-43*

Koda taji maganar komawarsa a bakin ummi yitayi kamar batajiba aganinta meya dameta da tafiyarsa tun da can bare yanxu dayake da mata.

Shareta shima yayi duk da yaso ya tsaya harsai ya gudanar da bincikensa akan Ahmed da duk wasu abokanan aikinsa koma su waye amma zai bari saiya dawo.

Sarai ummi ta lura da yanda neesah ke 'daure fuska idan ayeesha ta shigo saidai tayi murmushi sbd da zarar ta tambayeta zata iya tada rigimar itadai a raba aure,
Ita babban burinta da adduarta shine Allah yasa neesan tasamu ciki ko ta saduda ta daina maganar raba auren.

Ranar da zasu wuce qin fitowa tai ko palon sbd ko ganinsu bata buqatar yi.

Wanka tayo tana fitowa ta zauna gaban mirror ta fara Shafa cream 'dinta na jarggens,
Tana cikin fesa spray yashigo 'dakin da sallamarsa iya maqoshi.

Qin juyowa tayi bata kuma 'dagoba taci gaba da abinda take.

Tsayawa yayi bayanta tareda harde hannuwa yana kallonta ta cikin mirror.

Aje turaren tayi ta miqe zata bar gurin ya towel 'dinta
Tai saurin dafewa tareda 'dagowa rai a6ace zatai magana  saijin tayi bakinta ya sauka kan nasa sbd fuskarsa dake daf da tata.

Zaro idanuwa tayi tareda matsawa baya da sauri tareda tamke fuska sbd wani lazy smiling dayake sakar mata yana kallon tsakiyar  idanuwanta zuwa pink lips dinta.

Qara tamke fuska tayi ganin kallon nasa na neman sauyawa.

Wardrobe ta bude ta jawo doguwar riga tana juyowa still sai a jikinsa sbd ya kuma matsota sosai.

Ahankali ya shigar da ita jikinsa ya rungumeta tsam tareda sakin ajiyar zuciya a ciki.

Qoqarin qwacewa takeyi amma ta kasa saita lafe itama tanajin faduwar gaba da tsoro na shigarta Wanda ta rasa gane na meyene.,

Hawayen datake 6oyewa suka gangaro mata batasan sanda tasa hannu ta qanqamesa ba.

Rintse idanuwa yayi tareda shafa kanta haka kawai shima yakejin fa'duwar gaba da damuwa mai tsanani na shigarsa.

Murya can qasan maqoshi yace,

Am going back neee,
Do you need or want sumthing?

Batace komaiba saima hawayenta dasuka 6alle.

Shafa kanta ya qara tareda 'dago fuskarta yana kallo ta rintse idanuwanta hawaye na cigaba da gangaro mata.

Saukar light kiss taji a lips 'dinta tareda sakinta ya fice 'dakin da hanzari.

Koda ya fito ayeesha na motar Ahmed na jiransa ya fa'da suka wuce xuwa airport.

Zubewa tayi bakin gado tareda toshe baki kukanta na fita ahankali sbd haka kurin tsoro da fargaba ke shigarta.


**********
Tunda suka tafi ta qara zama wata iri sbd ta rage zaman gida sosai kullum a school suke yini ita zeey sbd yanxu su zeey babu wani tuggu tunda kusan sun samu yadda suke so sbd ayeesha na can tareda Jamaal 'din.

Plan 'daya suka tsayar shine suna dawowa zasu ha'da mata wannan tarkon da dole Jamaal zai tsaneta had abada bazai kuma ko kallon mai sunantaba.

A 6angare 'daya tsananin tausayi da qaunar Ahmed ke shigarta sbd gaba 'daya ya susuce baida wata damuwa saitata,
Baya iya koda cin abinci duk ranar dayaga damuwa ko hawaye a fuskarta,
Duk wani farin cikinta shine nasa hakama kullum cikin kyautata mata yake duk ya rame sbd a 'yan kwanakin wata irin wuta da ciwo dayakeji suna cin zuciyarsa akan neesah amma yaqi yake sosai da zuciyarsa ganin bai furta mataba ko nuna mata alama sbd Sam bazai juri ganin damuwa a fuskarta ba dan yasan tabbas zata shiga wani yanayin matuqar ta gane.

Ummi ma sosai take tausawa 'danta sbd tana lure da komai kuma tana hango tsananin damuwa daciwo a idanuwansa
Duk lokacin data zaunar dashi ta tambayesa meyene damuwarsa saidai ya kwantar da kansa kan cinyarta yafara hawaye yace ummi kiyimin addua  qila mutuwa zanyi sbd nikaina banajin da'din komai a duniyar yanxu.

Khadija ma dai ciwo ya tsanantar mata kuma Dr ya tabbatar mata da ciwon zuciyane yai mata mugun kamu dan haka yanxu a 6oye take siyan magani tanasha a 6oye amma Sam baya aiki sbd kullum da sabuwar qiyayyar matar jamaal ayeesha da hassadar neesah take kwana take tashi.




****
Tunda suka iso qasar ta rasa gane komai sbd Sam bayada time 'din zama gida kullum yana gurin aiki ga wani irin sabon miskilanci dake cinsa yanxu,

Abin na damunta amma daga baya data gane kukane bayason kuka tausaya mata yake idan ta fara saita koma kullum saitayi kuka
Tunda ga time 'din ya rage komai yana zama ya 'danyi wasan soyayya da ita har shopping da sauran guraren shaqatawa suna zuwa tare dan haka tuni yayi wani fresh sbd amarci da angwancewa da yayi duk da dai ba wani dacewa yayi ta hanyar making love da ita sbd Sam bata cikin jerin mata masu ni'ima duk da takawo budurcinta.

Haka suka cigaba da zama kwatsam saiga ciki ya bayyana.

Tashin farko da Dr ya sanar da ita tanada ciki yanka masa mari ne kawai batayiba sbs baqin ciki dan idan da akwai abinda ta tsana bayan neesah da Ahmed to yara ne bare ace wai ita da kanta zata haifesu.

Baro asibitin tayi bayan ta biya wani babban pharmacy ta siyo *****pills 3 sachet sbd batajin zata iya qara koda kwana 'dayane da cikin bare har Jamaal yasan tanada wani banxan ciki.

Tana isa gida kiran zeey nashigo wayarta saidata 'zauna ta 'daga wayar murya a cunkushe.

Lafiya dai Mrs cpt?

Saidata qaramin tsaki tace,

Inafa wata lafiya yanxun nan daga asibiti nake, can you imagine wai nice da ciki?
Wlh yau baqar ranace agareni dan Allah ji nake kamar na zaroshi na watsar a zinc.,

Cikin yanayin takaici itama zeey tace,

Gskia kam yanxu wayaketa wani ciki alhalin ko 'duwawuka baki gama bajewa a gidanba tunda haryanxu tsinanniyar na nan.,
To yanxu me kika yanke akan hakan?

Na riga na siyo magani zubar da sh***ge kawai zanyi yau 'din nan basai gobeba.

Kafin zeey tayi mgn taji qarar doorbell ta miqe ta bude masa tareda 'dan hugging 'dinsa kafin ta juya ta shiga bedroom suka cigaba da waya.

Zama yayi a palon yana qoqarin zame takalminsa ya hango envelope da sunan asibiti ajiki cikin hanbag 'dinta data bari palon.

Wat ya fada da qarfi cikin wani mugun farin cikinda baita6a yi ba arayuwarsa lokacin daya gama karanta result na cikin datake 'daukedashi.

'Dakin yashiga ba zato taji ya rungumeta tareda bata wani lafiyayyen  kiss sbd nan take wata irin muguwar soyayyarta da abinda ke cikinta sukai masa muguwar shiga.

Zamewa tayi tana masa kallon mamakin farin cikin dake fuskarsa dan rayuwarta bata ta6a ganinsa cikin farin ciki hakaba.


Result 'din ya nuna mata yana qara kai mata kiss a wuya yace,

Thank you my eshaa.

Qaqalo murmushi tayi tareda zamewa baqin ciki cikin ranta kamar ta rufesa da duka.

Miqewa yayi yakoma palo yana cewa,

Lemmi share this happiness wit my ummi sbd nasan abinda take farin cikin samu tuntuni kenan.

Yana fita ta 'dago wayarta ta mayar kan kunne sbd har lokacin zeey bata kasheba.

Wani shu'umun murmushi mai sauti  zeey tasaki tareda cewa,

Qawata lakacin dawowarku yayi sbd wannan damace dazamu jefi tsuntsu biyu da dutse 'daya.

Tunani ayeeshan tayi tareda sakin wata muguwar qaramar dariya tace,

Tabbas ciki zai zube neesah zata kar6i igiyoyin aurenta uku a hannunta.

Dariya zeey tasaki tace,

Hahhhhh lokacin damuka da'de muna jira gashi yazo a cikin sauqi domin matuqar cikin nan ya zube ba Jamaal ba ka'dai har ummi saita tsaneta hmmmnn wat a great and best plan.





Mamuh💋


🌲 *R H F W F*🐄

_Don't forget to vote, follow and comments_

DACEWA✅Where stories live. Discover now