dacewa pg 56-57

7.6K 555 19
                                    

*_DACEWA_*
     _(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*_Viawattpad@mamuhgee_*

*56-57*

Washe gari mamy tayi shirin komawa Jamaal yakaita airport ta wuce dama neesah a matse take da mamy takoma sbd sam batason su ayeesha su cutatar mata da ita.

Yana dawowa ya tararda yusuf a gidan..mamaki yayi sosai yana kallonsa sbd koda safe sunyi waya amma bai fada masa zaizoba.

A palon ummi suka zauna suna Yusuf 'din na fira da ummi kafin Jamaal 'din yashiga 'dakin neesah don fito da ita Yusuf ya dubata.

Zaune gaban  mirror hawaye take sosai sbd kewar Ahmed data taso mata.
Half rubber gown ce ajikinta sky blue mara hannu sai gashinta da ummi ta 'daure mata tsakiyar kai.

Kallonta yayi sosai yanajin wata muguwar kewarta na cinsa sbd rabon daya ganta in one 'dinta tun kafin cikin ayeesha ya zube.

Danne 6acin ranta da tsanarsa tafara qoqarin yi tareda miqewa taje bakin window ta tsaya tareda folding hannayenta.

Matsowa yayi ahankali tareda kai hannunsa ya riqo nata.

Ajiyar zuciya ya sake tareda lumshe idanuwansa.

Rintse idanuwanta tayi sbd jitayi kamar wutar lantarkice ta jata.

Sakinta yayi tareda bude wardrobe ya 'dauko dogon hijab yasa mata tareda riqo hannunta suka fito palon.

Zaunar da ita yayi kusada ummi.

Kallonta tsaf Yusuf yayi tareda yimata sannu da jiki batace qalaba saidai idanuwa data bisa dasu.

Ummi ce ta miqe tashiga 'dakin khadija Jamaal kuwa wayarsa datai qara ya 'daga sbd ganin dady ne.

Fakaitar idonta yayi ya karka6a handkerchief 'dinsa ka'dan..

Tari tafara sosai Jamaal yayi saurin katse wayarsa yana kallonta Yusuf yayi saurin miqa masa glass cup cikeda ruwa yace,

Bata tasha zata samu relief.

Kar6a tayi da sauri tasha sbd sosai taji mugun tarin kamar maqoshinta zai fita.

Tana shanye ruwan ta aje cup 'din tareda miqewa ta fa'da bedroom 'dinta.

Sake kiran dady Jamaal yayi Yusuf ya fakaici idanuwansa ya 'dauke cup 'din da neesah tasha ruwa ya jefa cikin briefcase 'dinsa.

'Dakin khadija suka shiga nanma saidaya samu ya fakaici idanuwan kowa ya samu ya 'dauke remote 'din Ac da mama ta kunna ta aje.

Sosai yakeson Tom print 'din khadija amma ba dama can idanuwansa suka hango masa wayarta gaban mirror batareda kowa ya luraba ya zurata aljihunsa suka fito palo ya 'dauki remote 'din palon da ummi tai amfani dashi.

Harzasu fita ya bude murya yace,

Inna Rabi empty cup zanje dashi masaukina zanyi amfani dashine.

Kallon mamaki Jamaal ya aika masa amma baice komaiba suka fito daidai ayeesha zata shiga gurinsu ummin.

Dariya Yusuf yasaki yana cewa,

Amaryar captain kinsamu kinshigo kota kanmu kindaina bi.

Cikin sakin fuska tace,

Wlh aa hankula ne wlh sunqi su kwanta shiyasa,,yaushe kashiga garin namu.

Yau 'din nan nashigo wani aiki amma insha Allah zuwa nextweek nagama aikina nakoma sbd aurena nima dayake gabatowa.

Kallonsa Jamaal yakumayi sbd shi Sam baisan da wata maganar aurensaba.

Wata waya ya fitar ya miqawa ayeesha yace kinga matata dazan aura.

Kar6ar wayar tayi tareda duba hoton tace,

Eh tanada kyau Allah yabada sa'a.

Ameen yace tareda kar6ar wayar suka wuce.

Key 'din motar Jamaal 'daya Yusuf yakar6a har zai shiga saiga zeey tashigo gidan sanyeda dogon hijab
Kallo 'daya Jamaal yayiwa gefen ya 'dauke kai.

Yusuf kuwa kallonta yayi dakyau yacewa Jamaal wannan tana yawan zuwa nan gidan ne?

Yes and why did you ask?

Nothing I just want....kawai bari na tunkareta.

Matsawa yayi da 'dan hanzarinsa ya tareta yana murmushin yace,

Yan mata naganki ne kuma nakasa hkr sbd zuciyata ta kamu yanxu dai ina sauri  rubuta min number ki I will call anjima saimuyi mgna.

Cikin mamakinsa ta kar6i pen 'din dayake bata ta rubuta masa ta wuce.

Yana barin gidan direct asibiti ya nufa  a office 'din Dr sulaiman ya fito da komai suka hau aiki akai.

Tashin farko tomprint 'din zeey yayi matching dana jikin syringe 'din.

Shiru sukayi na tsawon lokaci kafin Yusuf yakira Jamaal yace,

Pls Jamaal that lady Dana hadu da ita 'dazu dazan fito yatake a gidan.?

Close friend 'din neesah ce kaga karfa ka dameni da silly questions idan sonta kake kasameta karka dameni.

Kashe wayar yayi qwaqwalwarsa na qara 'daurewa.

Fita Dr sulaiman yayi yabarsa sbd kiran gaggawar da akai masa a emergency Ward.

Wayar khadija ya 'dauko tareda kunnawa sbd yaga last calls nata a ranar da abin yafaru.

Mamartace takirata last,,

Nazari yafara akan dalilin dayasa zeey 'din zatai mata haka...kodai taganta tana aikata wani Abu kokuma tanada abinda batason asani khadijar tasani.

Wayar yashiga yafara duddubawa..

Wani malalacin murmushi yasaki lokacinda yagama ganin videon.

Wani yakuma gani a ranar da cikin ayeesha ya xube.

Zama yayi tareda crossing legs yana yana jinjina kai cikin sauqi yagano komai batareda yasha wuyar daya tsammata ba.

Tattara kayan yayi tareda result 'din yasaka cikin jaka yafito tareda fadawa mota ya nufi  hotel 'din daya sauka barin jakar yayi cikin mota yatafi room 'dinsa.

Zeeey dake bibiyarsa sbd tun fitowarsa hankalinta yakasa kwanciya tabiyosa.

Murmushi tasaki tareda nunawa leloh  motar tace,

Leloh ka tabbatarda jakarcan batabar hotel 'din nan ba shikuma shegen zanji dashi.

Sauka leloh yayi ita kuma taja motar tabar gurin.



Mamuh💋


🌲 *R H F W F*🐄

_Don't forget to vote, follow and comments_

DACEWA✅Where stories live. Discover now