dacewa pg 50-51

9.4K 516 16
                                    

*_DACEWA_*
     _(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*_Viawattpad@mamuhgee_*

*50-51*

Gudu take sosai tana kallon gefensa dayake kallonta da idanuwansa dake qoqarin rufewa yana murmushi jini na zubowa daga bakinsa.

Hannuta 'daya ta miqa ahankali ta kama nasa tana hawaye murya na rawa tace,

I love too Ahmed,, ina sonka har cikin raina so mai tsanani so am begging you not to leave me pls Ahmed., ina sonka...

Saukar harbi taji cikin motar tasu ta 'dago da sauri taga motarsu zeey ce taredasu leloh ta figi motar ta qara gudu.

Harbin motarsu suke tako ina inda ayeesha ta fixge bindigar hannun leloh ta saita kan neesah tana cewa lets finish this today.

Harbowa tayi Ahmed ya yunquro da 'dan qaramin kuzarinsa ya tare bullet din ya sauka a tsakiyar bayansa.

Wani wahalallen nishi yasaki tareda zubewa jikinta.

Sakin motar tayi tareda rungumosa tana rintse ido tace,

Let's die together my Ahmed.

Daji motar tafara gangarawa dasu Wanda hakan yafara Jan hankalin motocin dake wucewa suka fara tsayawa da sauri su leloh suka tsaya daga nesa dan kar agane su suka biyosu.

Wani qaton rami motar ke qoqarin fa'dawa bayan tafara kamawa da wuta Ahmed ya tattaro wani qarfi ya tura 6an6areta jikinsa tareda turata waje da qarfi ta window riqe hannunsa tayi tana ihu tana kiran sunansa ya kalleta a wahalce yace,

Neeees'''bai qarasaba sulbin Jinin hannuwansu yasa ta sulbuce daga hannusa ta ganngara gefe kanta ya daki wani qaton dutsi nan take ta sume motar ta fa'da tareda kamawa da wuta sosai.

Ajiyar zuciya suka sauke kusan duk  atare ganin yanda wuta kecin motar sun tabbatarda bamai Rayuwa tsakanin neesah da Ahmed.

Kallon zeey ayeesha tayi cikin samun wani cikakken kwanciyar hankali tace,

Finally I got all I ever wanted.

Cikin taya aminiyarta farin ciki tace,

Well then lets all wish you a happy married life wit your captain,,you alone.

Juya kan motarsu sukayi suka bar gurin hankalinsu a kwance.

Aliyu mamman aliyu shine babban aminin Ahmed yana kawowa gurin yaga daidai lokacinda motar ke qoqarin fa'dawa rami yakuma tabbatarda motar neesah ce ya fito motarsa da sauri amma kafin ya iso motar ta fa'da tareda kamawa da wuta amma yaga lokacin da neesah ta gangaro ta daki dutsi.

Gurinta ya qarasa da sauri ya 'daukota yana kallo motar ta cinye tas da wuta ga amininsa aciki duk da kuka yake sosai kamar qaramin yaro.

Motar police ce tareda tasa suka 'dauko gawar Ahmed daya qone qurmus bayan an kashe wutar tareda neesah dake sume kamar gawa suka nufo cikin gari.

Asibiti suka fara kai neesah tareda barin 'yan sanda biyu gadinta kafin suka nufi gudansu Ahmed da gawarsa Wanda isarsu yayi daidai da isowar dady daga tafiyarsa.

Koda aka ciro gawar gaban dady aka bu'de saura qiris ya zube saida aliyu yayi saurin tarosa daidai fitowar Jamaal sbd jiniyar dayaji tashigo har cikin harabar gidan.

Gabansane yayi mummunar sarawa yayi saurin dafa motar sbd mahaukacin jirin daya 'dibesa.

Xubewa yayi gaban gawar tareda dafe kansa hawaye suka gangaro daga idanuwansa a karo na farko arayuwarsa  tun tashinsa baita6a koda hawaye ba bare kuka sai yau dayaga gawar Ahmed.

DACEWA✅Where stories live. Discover now