Dacewa pg 20-21

7.7K 582 10
                                    

_*DACEWA*_
     _(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*Viawattpad@mamuhgee*

*20-21*
Wani sahirtaccen murmushi yasaki yana cewa,

     She is unbelievable.

Fitowar dady ce tasashi qarasowa gurinsa suka nufi masallacin jikin gidan nasu dan sallar magrib da ake qoqarin tayarwa.

'Dakin ummi tashiga dan gabatarda sallah sai ganinta tayi zaune gaban mirror tana Shafa mai tafito wanka fuska a hade.

Cikin kulawa tace,
    Baby yaushe kika dawo?
      Kuma maiya sameki naga duk ranki kamar a 6ace.

Danne takaicinta da 6acin ranta tayi tace,

     Ummi nidai ki tara kowa na gidan nan kice kowama ya fita harkata dan gskia ummi bazan yarda anai mini kallon wulaqanci ba idan ba hakaba zan tattara nakoma hostel da zama.

Murmushi tasaki ahankali domin ta fahimci inda zancen ya dosa idan ba kuskure tayiba to lallai Jamaal ne ya ta6a ta,
Sarai tasan Jamaal zai iya hardai idan ya fahimci bataso ta tabbas ya dingi yi mata kenan harsai yaga tana neman zaucewa kan masifa.

Shafa kanta tayi tana cewa,

     Baby kyale koma wayene ni zanyuwa tufkar hanci saki ranki babu Wanda ya isa ya 6ata ranki a gidan nan indai ina nan.


********
Washe gari tunda safe ta shirya ko breakfast bataiba ta fito cikin adon Riga da skirt na coffee atampha da 'dan qaramin gyalenta kitchen ta leqa tacewa inna Rabi tabata Apple biyu.

Riqeda apple 'din da handbg 'dinta ta fito ta nufi part 'din Ahmed.

Zatai knocking saigasha yafito a gaggauce shima tace,

    Na 'dauka baka tashiba oya bani key 'din motana ina saurine.

Zaiyi magana wayarsa tai qara yaduba da sauri ya 'daga yana cewa,

     Ya Jamaal wlh inada test ne yanxu da safen nan amma idan nadawo zan kaima.,
Ok to ngd.

Kallonta yayi yace,
     Sorry Anty neesah wlh bankai wankin motar takiba amma muje atawa mana.

Harara ta sakar masa tareda cewa wlh bazan bika ba sbd daga can akwai inda zani.

Juyawa tayi a fusace takoma cikin gida tana qoqarin shigewa 'daki ta hango key 'din mota a saman center table batai wani dogon tunaniba ta 'dauka ta fito dan duk tunaninta motar ummi ce.

Kodata fito tuni Ahmed ya wuce dan haka kai tsaye ha'daddiyar sabuwar motar ta nufa dan dama tayita kwadayin hawanta amma anqi wanketa sai yanxu dataji ummin na maganar zata bikin auren 'yar qawarta.

Da mugun speed tabar gidan dan saura mintota ka'dan su shiga test 'din.

Baki maigadi yasaki yana mamakin yau wani yahau motar Jamaal akaro na farko bayan Ahmed dashima sai idan zai kaita wanki yake hawa.

Guraren 11 yafito cikin shirinsa na qananan kaya sai qamshin turaren oriflame signature dake tashi ajikinsa.

Palon yashiga cikin siririyar sallama.

Ummi ce kawai zaune a palon tana kallon tashar TLC entertainment.

Kallonsa tayi tana amsa gaisuwarsa kafin tace,

       Dadynku yayita jiranka baka fitoba and you switch off your phone harya fita.

Na manta ne ban kunna wayana ba bayan sallar asuba I will call him yanxu idan na fita.

DACEWA✅Where stories live. Discover now