dacewa pg 66-67

10.4K 657 12
                                    

*_DACEWA_*
      _(when east meets west)_


_By_
_Mamuh geee_

*_Viawattpad@mamuhgee_*


*66-67*

Shafo fuskarta yayi idanuwansa a lumshe sbd qoqarin danne buqatarsa dayakeson yayi duk da yanayinda yake ciki bayason kusantarta tana cikin wannan yanayin na damuwa.

Shiga jikinsa takuma yi sosai tana qara qanqamesa numfashinta na sauka ahankali sbd zazza6in daya fara sakinta..,

Duk iya yanda yaso dannewa kasawa yayi sbd zuciyarsa dake galabaice da kasancewa tareda neesar..,

Shinshinarta yafarayi tareda zame towel 'din jikinta ya jefo qasa yana ware jajayen idanuwansa kan qirjinta,,,

A galabaice ta bu'de idanuwanta ta sauke fes afuskarsa tareda girgiza masa kai sbd batada qarfin magana ko qwacewa daga abinda taga yana shirin aikata mata,,

ahankali yakai mata kiss a baki tareda lumshe rinanun idanuwansa...........

Wani mugun zazza6i ne ya rufeta mai qarfi jikinta ya'dau rawa banda wahalallen numfashi ba abinda take saki
Hawaye ma tuni suka qafe mata sbd ba qaramin azabtuwa tayi a hannun Jamaal ba.,

Zazza6in shima yakamasa sosai bayan yagama making love 'din ya qanqameta jikinsa na rawa yana sauke numfashi  har tsawon wasu seconds kafin yaji 'dan sauqin yanayin ya 'dauketa cak yakaita toilet...

Wanka yayo mata sbd  ita har time 'din zazza6ine sosai ajikinta ko hannunta bata iya 'dagawa..

Canza bedsheets yayi ya kwantar da ita tareda rungumeta ya lullu6esu bayan ya rage musu qarfin Ac..

Da asuba da qyar ya lalla6a yakuma wani wanka ya nufiMasallaci ya nufa yanajin wata nutsuwa,haske da kwanciyar hankali na shiga zuciyarsa,,

Har gari yayi haske baidawoba kai tsaye barrack ya nufa sbd kai qarshe da matsalarsu ayeesha sbd kiran da akayi masa qafar zeey ta ru6e sun yanke itakuma ayeesha suna sakaran qwaqwalwarta tasamu matsala sbd banda sambatu ba abinda take,,

Qarfe tara ta tashi daqyar ta lalla6a tasaka hijab 'dinta fuska a kumbure ta nufi cikin gida.,

Bakowa a Palo ta shige bedroom 'dinta tafada toilet tayo wanka tayi sallah ta saka doguwar riga tareda shirya kayanta tsaf a akwatinanta ta zauna bakin gado tareda rafka tagumi siraran hawaye suka gangaro mata
Ta rintse ido tana tunano yanayin daren jiya 'din.,

Miqewa tayi ahankali ta nufi bakin window ta tsaya tareda rungume hannuwanta ta rufe idanuwa tana qoqarin manta komai amma takasa saima zafi da zuciyarta tafara sbd tuno shi'dinfa tsohon mijin wata ne kenan ragin ayeesha ne ita zata samu,,,rintse ido tayi sabbin hawaye masu zafi suka gangaro mata zuciyarta na zafi.,

Ummi da mamy ne suka shigo tajuyo ahankali batareda ta goge hawayenta ba.

Kallonta mamy tayi ummi kuwa akwatinan dake tsaye ta kalla tana cewa,

Baby lafiya kuwa naga kaya a tsaye?

Matsowa tayi ta Riqo hannun ummin murya a shaqe tace,

Ummi mamy zanbi zankoma abuja I need s.....

Katseta ummi tayi cikeda damuwa a fuskarta tace,

Baby barina zakiyi kema kamar Ahmed ga Jamaal shima komawa zaiyi,ga khadija itama ta tafi tabarni...

Hawayen idonta ta mayar tareda sakin murmushin qarfin hali tace,

Idan na hanaki tafiya banyi miki adalciba Dan haka kije idan kin huta sai Jamaal yazo yadawo dake.

A'a""mamy tace tareda 'dorawa da fadin,

Ko ina baxataba tunda inma ta tafi mezatayo acan 'din ga gidan mijinta.,,

Kallon mamy neesan tayi tareda girgiza kai idonta na kawo sabbin hawaye tace,

Mamy kibarni naje wlh zuciyata batada sukuni yanxu ina buqatar matsawa daga nan 'din koda na qanqanin lokaci ne.

Badan mamy tasoba dady yace abar neesar taje kafin Jamaal yakuma dawowa.

Sosai mama taji damuwa da kewar tafiyar neesah sbd ganinta na 'debe mata kewar khadijarta,,

Harsuka isa airport idanuwanta a lumshe suke zuciyarta na tsananta zafi sbd har lokacin baidawoba haka zuciyarta ta nasa mata gurinsu ayeesha yaje kenan haryanxu itace a gabansa..

Takaici da baqin ciki suka shigeta ahankali na yanda yasamu damarta ya kusantu da ita.

Da yamma jirginsu ya sauka  abuja naseer yazo 'daukarsu harsuka isa gida batai maganaba saima ciwon kai da zazza6in dake neman rufeta na zuciyarta data kasa sukuni  har lokacin.

Tsaf bedroom 'dinta yake sbd asiya mai aikinsu data gyara matashi kafin isowarsu,

Wanka tayi bayan tayi sallah tafito taci abinci ka'dan tazauna Palo saigasu amirah sun iso nan dai suka koma bedroom suka hau hayaniya dukda Sam takasa sakewa sbd yanayin rashin qarfin jikinta dakuma damuwar zuciyarta.

Da daddare abbanta daya dawo tare sukaci abinci a dining cikin farin ciki,,

Anan amirah takwana tana lalla6ata sbd Sam takasa sukuni sbd zuciyarta dake mata raye raye akan Jamaal da ayeesha..

Hardare bai gantaba yakasa sharewa ya nufi bedroom 'dinta yaga alamar batanan yafito Palo ummi takallesa tana zama tace,

Baby tabi mamy abuja munyita kiran wayarka akashe shiyasa dadynku yace taje idan kadawo afa'da maka.

Kallo 'daya yayiwa ummin ya fice yana fiddo wayarsa dake ringing a aljihun wandonsa cikin zafin zuciya na yanda za'a bari tatafi batareda anbari anji ra'ayinsa.

Da shirin bin jirgin safe na zuwa abuja ya kwana amma saiga urgent emergency call daga UK badan yasoba dole ya wuce UK batareda ko waya yasamuyi da itaba sbd ko num baida.

**********

Almost three months kenan da dawowarta abuja kuma tsawon lokacin bata sakashi a idoba bare ko muryarsa,,

Sosai abin ke cin zuciyarta sbd zuciyarta data riga ta ayyana mata ya dawo da matarsa sunacan suna sha'aninsu.,
Takaicin da baqin cikin hakan yasa ta daure ta watsar da tunani da alamarinsa saidai tayiwa kanta alqawarin bazata zauna dashiba sbd tafi qarfin ragin wata kuma qarin abin haushima qaninta..

Ta ware sosai sun shiga harkokin gabansu itadasu amirah har mantawa take da wani aure
Tayi wani mugun fresh da haske mai qyalli,
Fatarta harwani yellow yellow tayi hakama ramarta ta 6ace dirinta yakuma fitowa sai yanga da Jan aji ya qaru Dan tuni takoma neesarta ta dah.,

Mamy dasu amirah har  mamakin haske da qyau da kullum takeyi suke amma kasancewar hutu da kwanciyar hankali yakamata saisuka cigaba da alamuransu.

Wasu lokutan tunaninsa nacin zuciyarta saita share duk da amirah kullum  cikin maimaita mata zance 'daya take """ _neesah kishin Jamaal ke wahalar da zuciyarki_..

Zancen na qona ranta shiyasa take qoqarin watsar da duk wani tunaninsa da alamuransa bawai Dan taciresa aranta ba.

Bikin amirah da Yusuf ya matso sosai sun duqufa gurin sha'anin hidimar bikin Dan bikine na wayayyun 'yan bokon angwaye da amare.


Mamuh💋

RHFWF

DACEWA✅Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ