Dacewa pg 18-19

7.5K 666 2
                                    

_*DACEWA*_
     _(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*Viawattpad@mamuhgee*

*18-19*
Tunda neesah taji maganar dawowar Jamaal ta rage zama sosai a gidan
Kullum tana school sai yamma sosai take dawowa data dawo kuma zatai shigewarta 'daki.

Ummi na lure ta qyaleta gudun rigimarta,
Ahmed ne kawai yake samun ganin fara'arta harsuyi fira.

Khadija kuwa sosai take al'amuranta cikin tsananin farin ciki.
Kowa yayi mamakin sabon yanayin nata amma sukai shiru itama batareda sunce komaiba.


Ranar Wednesday tun guraren 8:00 ta tafi school sbd Sam takasa samun sukuni cikin gidan,.

Duk wata hidimar tarbonsa inna Rabi da khadija ne suka yita.

A da inna Rabi ke gyara 6angarensa idan zai dawo amma wannan karon khadija ce taje ta gyare komai ta kunna aircon tareda kunna fridge 'din dake palonsa bayan taje ta 'dauko ruwan Eva katon 'daya da drinks ta jera aciki.
Rufo qofar tayi takoma 'dakinta tayi wanka tareda zaunawa gaban mirror har zatai kwalliya saikuma ta fasa gudun kada agano manufarta,

Riga da skirt na maroon atampa tasaka tareda 'daura 'dan siririn gyale akanta tadawo Palo tazauna tana charting da wayanta cikin walwala sbd tuni Ahmed yatafi airport 'daukosa.



A nutse yake tafiya hannunsa 'daya na cikin aljihun black fanfuego trousers 'dinsa sai 'dayan hannun yana waya da ayeesha dayake dakatarwa akan kadatazo 'daukarsa Ahmed yazo daukarsa.

Kyakkyawar fatarsa dake sheqin Hutu da kyau Ahmed ya tsaya kallo harya iso gabansa daidai gama wayarsa da ayeesha ya kalli Ahmed 'din yana saka 'dayan hannunsa cikin pocket 'din wandonsa.

Murmushi Ahmed yasaki yana cewa,
       Gskia Yaya zanzo na nemi Hutu kwanan nan natafi gurinka sbd nima nasamu lafiyar fata kodan nima na riqa jawa husna aji.

Murmushi kawai yasaki batareda yace masa komai akan abinda yafadaba yace,

     Idan ka gama shirmenka kasaka kayan a mota ka kaini gida coz I desperately wanah see my mummy.

Shigewa yayi  motan shikuma Ahmed yayi saurin
Saka kayan mota suka nufi gida.

Tun a mota ya kashe wayarsa sbd yasan Sam yanxu ba Hutu ayeesha ta dinga kiransa kenan..

Suna isa gida Ahmed ya nufi part 'dinsa kai masa kayansa shikuma ya nufi palonsu ummi kai tsaye.

Cikeda tsananin farin ciki ummi ta tarbesa zama yayi kusada ita yana riqo hannunta yace,

     Ummi da fatan na sameku lpia?

Lpia klau Jamaal,
Ya hanya?

Kasalallen murmushi yasaki yana cewa,
    Alhamdulillah.

A ladafce khadija ta taso har gabansa cikin sanyin murya  tace,

       Ya Jamaal barka da dawowa.

Batareda ya kalletaba ya qaqalo murmushi yace,

       Yawwa khadija,
Ya studies naki?

Tana 'dan qaqalo fara'a itama tace,

     Alhadulillah.

Da haka ta juya tabar palon jiki a mace sbd rashin ganin fuska a gunsa Wanda dama hakan suke tun farkon fari.

Inna Rabi kam kasa zama tayi sai hidimar kawo masa abubuwan sha take cikin farin ciki dan har cikin ranta Allah yadora mata qaunar Jamaal tun yarintarsa.

Murmushi yasaki har fararen haqoransa suka bayyana cikin kulawa sosai yace,

    Innah,
Inna kibarshi hakanan bana buqatar ci ko shan komai yanxu Am ok,
     Saidai zuwa anjima may b.

To Jamaal amma mutum yayo tafiya yace ko ruwa bazaisha ba.

Inna kadaki damu anjima zanci kuma ke zaki bani da kanki dan nasan yanxu ummi ta canzani batada time 'dina.

Cikin so da qaunarsa ummi tace,

     Jamaal bani kadai na ajekaba kowama har inna 'din sbd kanada mata yanzu and all kulawanka da 'dawainiyanka yana kanta yanzu.

'Dauke wuta yayi fuskarsa na 'dan canzawa sbd gaba 'daya ya manta da zancen auren da neesah.

Anyways baida matsala da ita tunda bason auren takeba afterall bayajin zai iya zama da duk macen da bazata iya respecting 'dinsaba tabasa girman daya kamacesa amatsayinsa na mijintaba koba komai baida time 'din mata irinta.

Miqewa yayi daidai shigowar Ahmed bai kallesaba yana ficewa yace,

     Ahmed take my car out to man-u car wash I have important place to go anjima.

Sashensa ya shiga kai tsaye bedroom ya nufa saidaya kunna wayarsa yakira dady sun 'dan 'dau time suna mgn kafin ya kashe yafada toilet yayo wanka.

Koda yafito dogon wandon Judhench black yasaka tareda rigar blue rugbay shirt sbd shi mutum ne mai yawan jin sanyi komai qanqantarsa.

Kwantawa yayi sbd sosai yakeda buqatar hutawa.


Bata dawoba saida maraice shi 'dinma sbd kawai ta gaji ne sosai hutu kawai take buqata.

A galabaice tashigo gidan tana parking ta fito motar riqeda handbag dinta,
Doguwar rigar turkey straight gown ce ajikinta databi jikinta ta kwanta kalar ja sai 'dan siririn red Vail data yane kanta dashi.

Sam bata lura dashiba shiyasa kai tsaye take tafiyar kamar wadda kwai ya fashewa aciki.

Kamar ance ta 'dago takalli gefenta

Tsaye yake a varandan qofar palonsa ya zuba hannayensa cikin aljihun dogon wandonsa daya canza ga alama wani wankan yayi bayan yatashi bacci,

Kafeta yayi da ido batareda wani sabon yanayi ya sauka a fuskarsaba Wanda hakan ya tabbatar mata da kallon raini ne da tsantsar wulaqanci yake mata.

Ranta ne yai tsananin 6aci ta 'dauke kai a fusace taqarasa cikin Palo ko inna Rabi dake jera abincin 'dare a dining bata kallaba tawuce 'daki tana fadin,
    
      Wlh bazan yarda da kallon wulaqanci ba bari ummi tazo.


🌲 *R H F W F* 🐄

Mamuh💋

_Dont forget to#vote#follow#and comments via wattpad@mamuhgee_

DACEWA✅حيث تعيش القصص. اكتشف الآن