dacewa pg 60-61

9.6K 678 74
                                    

*_DACEWA_*
     _(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*_Viawattpad@mamuhgee_*

*60-61*

Direct gidansa dake qarshen street 'dinsu ya nufa

A gigice mai gadi ya bu'de masa gate sbd jin horn 'din dayake a masife.

Ko kashe motar beyiba ya fito ya bu'de boot ya jawota kamar kayan wanki ya nufi bq ya bu'de ya jefata batareda ya warware mata zanin gadonba ya rufe qofar ya juya yabar gidan da mugun speed.

Koda ya isa gida qin fitowa yayi daga motar ya kwantarda kansa jikin seat tareda rintse idanuwansa yanajin zuciyarsa na quna har lokacin.

Ya 'dau tsowon minti goma sha biyar kafin ya bu'de idanuwansa da har time 'din basu dawo daidaiba ya bu'de motar yafito.

Part 'dinsu ummi yakalla jikinsa na saki sbd ba abinda yake qaunar gani yanxu sama da neesah.

Kai tsaye can ya nufa batareda la'akari da menene time ba.

A rufe yaji qofar palon ya lumshe ido cikin damuwar kasancewar qofar a rufe.
Part 'dinsa ya nufa yashiga bedroom tareda tu6ewa yayo wanka ya zube a gado zuciyarsa na qara azalzala da tsananin buqatar ganin neesah duk da yasan Abu ne mai wahala ta manta komai dan ya lura da tanada kafiya akan abu.

Da qyar yaga gari ya fara haske bayan sallar asuba ya fito yashiga motarsa ya fice.

Koda ya isa a kwance ya tarar da ita tana nishi hawaye nabin fuskarta data kumbura,,

Qafar ya kalla ta kumbura sosai sbd har lokacin bullet na cikin qafar,,

Cikin tsananin tsoro take kallonsa sbd ganin sa6on 6acin rai a tattared dashi.

Saiti da gurinda bullet 'din ke ciki ya taka da qarfi ta saki wata razananniyar qara tareda qara sumewa daga zaunen.

Ruwan qanqara ya kwara mata a gigice ta farfa'do yakuma taka qafar da qarfi nanma saidata kuma sumewa ya kuma zuba mata ruwan qanqara.

Tana farfadowa ko motsi bata iyayi sbd azaba...

'Daga qafa yayi zai kuma takawa cikin kakkausar murya yace,

Tell me su waye partners 'dinki?

Girgixa kai tayi cikin wasu irin azababbin hawaye sbd ko bakin bazata iya bu'dewa ba sbd galabaituwa.

Wani mahaukacin naushi yakai mata a baki saiga haqoranta biyu sun fa'do tareda jini cikin 'daga murya sosai yace,

Bazaki fa'daba kenan?

A wahalce tace,

Ni ka'dai ce.

Takaici da baqin ciki yasashi rufeta da duka da yana tattaka qafarta.

Saidaya tabbatarda bata motsi ya fice kayansa duk jini ya 'dan ta6asu.

Koda ya isa gida part 'dinsa yaje yayi wanka ya shiryo kafin ya nufo 6angaren.

Ummi da inna Rabi ne kawai a palon suna fira mama kuma na kan dining tana cin abinci.

Gaida ummi yayi kafin inna Rabi dan baima lurada mama ba.

Bedroom 'dinta ya nufa kai tsaye yashiga tareda rufowa.

Bai gantaba amma yaji motsin ruwa a toilet..

Bakin window yaje ya tsaye tareda zuba hannuwansa a aljihu ya lumshe idanuwansa.

'Daureda 'dan qaramin towel ta fito sai wani qaramin a hannunta sbd hadda wankan tsarki tayo na period data gama.

DACEWA✅Where stories live. Discover now