dacewa pg 52-53

9.2K 547 23
                                    

*_DACEWA_*
     _(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*_Viawattpad@mamuhgee_*

*52-53*

_wannan page 'din na ta'aziya ne daban hakuri ga masoyan Ahmed da zukatansu suka ta6u_🙏

Zaune take tsakiyar gadon ta kwantarda kanta kan qafafunta idonuwanta qure kan qofa ko qiftawa batayi saidai sun ka'da jajir  duk ta qara zabgewa duk Wanda ya ganta saiya tausaya mata sbd ta canxa kamar ba neesah ba.

Mamy zaune riqeda remote tana ragewa Ac 'dakin sanyi sbd jin jikin neesar kamar da zazza6i.

Ummi ce a gaba kafin mama sai khadija.

Gurin neesah ummi ta nufa ta zauna jikinta na 'qara sanyi hawaye na taruwa a idonta sbd fuskar Ahmed take gani data kalli neesah.

Mamy gaisawa tayi da mama kafin ta amsa gaisuwar khadija dake raku6e kusada qofa tana kallon yanda yau neesah 'yar gayu da class takoma banbancinta da mahaukata ka'dan ne duk sbd aikin maqiya.

Rintse idanuwanta tayi wasu hawaye masu 'dumi suka gangaro mata ta lumshe ido tanajin damuwar rayuwar data tsinci kanta aciki Wanda sai yanxu take tabbatarda Allah ya hanata Jamaal ne sbd wannan azabar da neesah ke ciki ba qaddararta bace dan qila da ita'dince to da tuni su zeey 'din sun kasheta.

Shiru ya ratsa 'dakin na 'dan wani lokaci saiga Jamaal yashigo tareda ayeesha data biyosa damin ganin 'dakin da neesah take.

Kallon tuhuma mama ta watsawa ayeesah kafin ta saci kallon gefen Jamaal dake duba magungunan daya Dr kudi 'dazu da safe asiya tai fuskar mamaki tana fadin,

Meyasa ayeesah 'dazu kikayi mamakin da'akace neesah na raye harkina cewa bazai yiyu ace wani ya rayu a wutar nan ba?
A maganarki sai inaga kenan kina tsaye abin yafaru ko?

Dukkaninsu a bazata zancen yashigesu suka 'dora idanuwansu akan ayeesha don jiran mezatace ita.

Jikintane ya'dau rawa wani mugun zufa ya karyo mata ta kalli Jamaal taga ya kafeta da idanuwansa qasa qasa ai nan dabara ta fara kwance mata tana rawar murya tace,

Um..um...am..nazo wucewa ne dana dawo daga asibiti naga.....

Katseta mama tayi da cewa,

Wow wat miracle harkin iya fita keda kikai 6ari kuma idan ban mantaba a ranar aka dawo dake daga asibiti ina fatan dai ba wata matsalar ce tadawo miki ba harkika fita zuwa asibitin.

Wani yawun ta ha'de tana Neman abin cewa saikuma taji maman tasake cewa,

Kuma Kinga qanwarki nan khadija kwanakin nan tana fama da rashin lapia amma taqi zuwa asibiti sbd tsoron shiga mutane ne da ita kozaki fa'damin sunan asibitin dake hanyar barin gari saina kaita.

Cikeda baqin ciki da takaicin mamar daya cikata tace,

Nibansan wata asibitin bayan gariba.

Zaro ido mama tayi tace,

Aa kuma kikace zaki asibiti ne kikaga ha'darin a bayan gari?

Zaro ido tayi sbd shaf ta manta da haka tafada da farko.

Ummi da mamy takalla taga kowaccensu tayi nisa cikin nazarin maganganun a ranta tace nashiga uku wannan tsinanniyar matar zata kaini karshe na tona asirina da kaina dole nayi gaggawar sanar da zee a 'dau mataki akanta.

Jamaal kuwa ficewa yayi a 'dakin yana jujuya zancen mama da yanayin da ayeesha tashiga akan tambayar.

Wani mugun kallo ayeesha tabi mamar dashi tana qissima irin mummunar kisar dazatai mata.

DACEWA✅Where stories live. Discover now