DACEWA pg 16-17

9.1K 808 19
                                    

DACEWA
(when east meets west)

By
Mamuh geee

Viawattpad@mamuhgee

Thanks mum AbdulAhat,,,

16-17
Da safe qin fitowa khadija tayi koda ummi ta tambayi lafiya sai cewa tayi kantane ke ciwo kuma yau batada lectures a school.

Neesah kuwa lafiya lau tai baccinta dan kusan rabin 6acin ran datazo dashi ya tafi sbd anan ne tasan ummi zatai mata duk abinda takeso bamai hanawa ciki kuwa harda raba wannan qaddararren auren zubar mata da girma.

Kodata fito Palon guraren 11 bakowa sai inna Rabi dake kaida kawon ayyukanta.

Zama tayi a sofa suna gaisawa da inna Rabin ta'dora da cewa,

Inna ummi fa?

Ummi takoma sama bayan fitar alhaji.

Ok, to Ahmed fa shima yafita ne?

Aa bai fitaba tukun dan baima shigoba yayi karin safe,
Yau alhaji da ummi kawai sukai kari,
Ke,
Ahmed da khadija duk kun musu tawaye yau.

Murmushi tadanyi tana duba kiran daya shigo wayarta tace,

Ammnnnn Inna pls kibani breakfast 'dina a 'daki Idan kuma Ahmed yashigo kice yasameni ina nemansa.

Tana gama fada ta miqe tai bedroom tareda amsa wayarta.

Sunkuyar da kai khadija tayi cikin nauyin zuciya sbd fitowarta kenan ta tarar da neesah da innar a palon suna magana.

Bayan shigewar neesah bedroom kasa qarasawa palon khadija tayi sbd 'dan guntun qarfin zuciyarta da ganin neesah ya wargaza.,

Juyawa tayi batareda taje taci nata breakfast 'dinba takoma 'daki tana danne hawayen dake qoqarin gangaro mata ba.

Koda Ahmed yashigo palon saida yaci abinci kafin ya nufi 'dakin ummi gurin neesah,

Zaune take gaban mirror har lokacin waya take dasu amirah.

Katse wayar tayi tajuyo gurinsa tace,

Ahmed so nake ka kaini gurin da zan samu lafiyayyen gyaran kai a garin nan.

Ajiyar zuciya ya sauke yana cewa,

I thought wani laifin nayi danaji kiran nan.,
Ok to kishirya nan da 50 minutes zan dawo nakaiki yanxu zan kar6o saqo wani urgent saqo ne.

Dan Siririn tsaki tasaki tana 'daure fuska tace,

Karka kuskura ka shanyani.

Daria yasaki yana ficewa yace,

Insha Allah Anty neesah.

Ko 50 minutes 'din bai cikaba yadawo har lokacin ummi na sama sai kawai sukai ficewarsu.

A wani babban saloon daya hadu matuqa suka Parker ta fito tashiga tana yaba gurin ba laifi yayi.

Kasancewar weekdays ne babu mutane agurin sbd aiki
Mutum 'daya ta tarar a gurin ana mata gyaran kai itama.

Kallo 'daya neesah taiwa gurin ta 'dauke kai tareda kallon 'daya daga cikin 'yan matan shagon tayi mata bayanin abinda za'ayi mata.

Kusan atare atare suka miqe bayan an kammalawa ko waccensu abinda yakawosu.

Tsaye suke gaban tangamemen mirror 'din gurin..

Siririn gyalen data yafo batareda 'dankwaliba neesah ke gyarawa,
Ita kuwa 'dayar powder ta qara shafawa tana gyara zaman hot red jambakin dake lips 'dinta.

DACEWA✅Where stories live. Discover now