DACEWA pg 14-15

8.6K 613 10
                                    

*_DACEWA_*
     _(when east meets west)_

_By_
_Mamuh geee_

*Balkeey Shuwerh I sincerely heart you*❤

*14-15*
Tun acikin daren take kuka shiyasa koda ta tashi da safe idanuwanta sun kumbura.

Fushi take da kowa a gidan dan haka ko breakfast bata fitoba.

Ummi taso zuwa ta rarrasota amma mamy ta dakatar da ita ta hanyar miqewa ta nufi 'dakin.

Zaune ta tarar da ita gaban mirror 'daure da towel alamun wanka ta fito.

Akwatinanta mamy tajawo ta bude wardrobe ta kashe kayan ciki tsaf ta jere matasu a akwati ta rufe akwatinan ta matsar gefe tareda zama bakin gado ta fuskanci neesah.

Hawayen datake dannewa suka gangaro mata ta 'dauke kai daga kallon 6angaren mamy.

Neesah,
Neesah hakan dakike qoqarin yi baida banbanci da abinda su taheer sukai mana na fasa auren 'yarmu a ranar 'daurin aure.

Mune iyayenki dasukafi duk wani mai sonki qaunarki amma kike qoqarin bijirewa buqatarmu akan wani dalilinki na banza,

Shi Jamaal 'din da kike rainawa kina masa kallon wanda kikafi qarfi tabban idan bakiyi ahankiba wataran saikin zubar da hawaye akansa illaima na sonsa illaima na qaunarsa.

Jajayen idanuwanta ta kalli mamyn dasu murya a karye tace,

    Mamy dan Allah Ku tausayamin kadaku yankemin hukuncin dazai lalata farin cikina wlh ba laifina bane dana kasa sonsa,

Nayi iya qoqarin dannewa amma na kasa kodan sbd ummi amma wlh mamy bana son ko sunansa naji ana fada amatsayin mijin danake aure.

Takaicin neesar ne yafara kama mamy amma sbd son ta rarrasheta saita dake tace,

Neesah ki daure kiyiwa iyayenki biyayya kodan yanda dadyn Jamaal yayi saving 'din abbanki daga humiliation 'din dasu taheer suka tanadar mana a idon mutane,

A 6angare 'daya haka zaki sakawa ummi da tsantsar soyayyar datake yi miki tun kina qanqanuwa,

Neesah ko kunyarta bakyaji na yanda kika fito kai tsaye kika nuna bakya qaunar 'danta datake matuqar so.

Hawaye suka gangaro a fuskar neesah batareda ta gogeba murya a qarye tace,
     
        Mamy har abada bazan qi jinin ummi ba amma wlh mamy bana sonsa amatsayin abokin Rayuwa.

Tsuke fuska mamy tayi tareda miqewa tsaye tace,

     Tunda lallashi baya yimiki sai ayimiki yanda zakifi ganewa,
Ki tashi ki saka kayanki 10:00 flight 'dinku zai tashi zuwa Lagos.
Kuma wallahi a matsayina na mahaifiyarki ban yafe ki ce komai ba akan tafiyar nan.

Ficewa tayi a fusace takoma Palo.


Baqin ciki da takaicin datake ciki bamai faduwa bane ta danne abinta cikin ranta tareda 'daukarwa kanta mugayen alqawaririka akan Jamaal dabaimasan tanayiba danshi tuni ya aje zancen auren a gefe ya maida hankali akan alamuran gabansa.

Abba sosai yayi mata nasiha hakama mamy duk da tana fushi da ita.

Nasir ma na gida a ranar sbd Saturday ce ba school
Sosai yashiga damuwar tafiyar antynsa duk da kullum sai sunyi fada sbd shegen son girmanta da rainasa datayi Wanda shi kuma bayason hakan dan yace so yake shima Idan ya qara girma yazama handsome cool guy kaman Jamaal.

Har suka iso Lagos batace qalaba hakama batai ko guntun hawayeba sbd alqawarin datai na bazata qara zubar da hawayenta a banxa ba.

Ahmed yazo 'daukarsu daga airport danshi tuni suka dawo tareda dady.

DACEWA✅Where stories live. Discover now