Chapter 30

997 68 1
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

            *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"Some people will pretend to care just so they can get a better seat to watch your struggle. Every helping hand is not always there to help."

     _I dedicate dis page to my luvly sisters *Hassana nd Hussaina, nd lastly d trublsum of all Halima (Limanbaby)* i luv u all❤😍_

               3⃣0⃣

        *One week later*
   
     Abubuwa da dama sun faru cikin sati daya, wanda akwai C.A dinda su *ZYNAH* suka fara har sun kusa gamawa saboda ana rushing dinsu ne, *ASHRAF* be samu rubuta ko daya daga ciki ba amma saboda lecturers din sunsan halin da yake ciki sunce kar ya damu zasu mishi make up test wanda badan komai sukayi haka ba se dan sunsan yana kokari shiyasa.  *ASHRAF* ya fara samun sauki dan yanzu yana tsayawa amma wit d help of walking stick  dan doctor ma yace za'a sallame shi nan bada dadewa ba, KB na chan ya takurawa *ZYNAH* da shegen nacin shi dukda ita *ZYNAH* ko kulashi batayi, amma kullum in zata lectures ko zata dawo seta hadu dashi kuma seya tsayar da ita yana jaddada mata son da yake mata alhalin chan kasar zuciyarshi ba son da yake mata illa tsantsar sha'awa, Fahad ya koma Kaduna inda yake service dinshi amma tunanin *ZYNAH* ya addabeshi, yama kanshi alkawarin in yasake komawa Zaria zema *ASHRAF* magana inyaso se ya karba contact dinta, Uncle Yusuf shima yana chan tunanin Minal yasashi gaba ba dare ba rana, *ASHRAF* da *ZYNAH* kuwa lbr ya chanza dan yanzu sun shaku sosai dukda basu fito sun fadawa juna sirrin zuciyansu ba amma dey ar close sosai dan kullum setaje ta gaishe a hospital saboda she feels guilty, tana gani kaman saboda ita yashiga wannan halin, sannan kullum suna waya kafin su kwanta.
        _Wannan kenan_

     Yau ya kama Sunday wanda a ranan akayi discharge din *ASHRAF* daga hospital amma ze dinga komawa akai akai ana dubashi, ya koma gida kuma yaji dadin dawowan shi dan a ganinshi yanzu ne lokacin da ze iya takurawa Abba harse yaga ya dawo da *ZYNAH* gidan, ba wanda ya fadawa plan dinshi banda Abba wanda har yanzu be bashi hadin kai ba. "Abba plss do dis for my sake, i want protect dis girl frm getting harmed" ,"toh kai  *ASHRAF* ka tambaye ta kuma tace ma zata dawo nan din?" ,"a'a Abba amma nasan itama zataso dawowan", Abba ganin *ASHRAF* beda niyyar barin wannan maganan yasa yace "toh naji, ka karbo min number mahaifinta muyi magana ta fahimta dashi tukunnan" wani dadi *ASHRAF* yaji yace "shikenan Abba na gode". A ranan *ASHRAF*  ya kira *ZYNAH* sukasha hiran su yake ce mata gobe zeyi resuming ze dawo school amma be fada mata abunda yake shirin yi ba na  dawowanta gidan.

*WASHEGARI*

     Yau yakama Monday, *ZYNAH* da wuri ta tashi saboda yau zasu fara exam, tayi abunda zatayi ta shirya cikin peach english gown da gold veil tayi kyau dukda ba makeup tayi ba dan dama batayi fancy dinshi ba. Ta fito tana sauri saboda saura 40min a fara paper din, bata lura ba taga mutum tsaye a gabanta yana mata murmushi "baby girl har za'a shiga exam hall" ko kallonshi batayi ba yace "anyways am here to wish u good luck" ,"i don't need ur good lucks, so get d hell out of my way", murmushi yayi yace "sure, am letting u go cus i don't want u to b late, so all d bst", wani harara ta maka mishi tareda jan wani dogon tsaki sannan ta wuce, shikuwa kallo ya bita dashi kaman tsohun maye yace "yarinya zaki gane kuranki". Tana shiga hall ko 20min batayi ba aka fara exam. Shima *ASHRAF* da wuri ya tashi saboda bayan exam dole ya tsaya yayi test dinshi kuma yanason ganin *ZYNAH*, ya gama abunda zeyi ya tashi da sandan shi a hannu yafito, part din Ummi ya shiga ya gaisheta sannan ya zauna a dinning Minal ta kawo mishi abinci yaci sannan ya dau wayan shi ya kira Sameer "hello bros kana ina na gama" ,"Ok gani nan zuwa". Cikin minti uku Sameer ya karaso gidan *ASHRAF* ya fita ya shiga mota suka kama hanya.

     Sun gama paper din ranan ta koma hostel dan ta huta saboda ta gaji Dan paper din yayi tough. *ASHRAF* kam bashi ya gama abunda zeyi ba se 4 na yamma saboda bayan papern da ya rubuta seda yayi test uku sannan yasamu kanshi, waya ya dauka ya kira *ZYNAH* wacce cikin barci taji ringing din wayarta ta tashi ta dauka batare da ta duba sunan ba, jin muryan *ASHRAF* yasa barcin da takeji ya wassake, ta tashi zaune "hello *ZYNAH* kina ina", "ina daki", "dan zo cafeteria ina jiran ki", "ok gani nan zuwa". Tashi tayi ta shirya ta dau wayanta tafito , cafeteria ta nufa direct,  chan baya ta hango ta nufeshi fuskan ta cike da murmushi, zama tayi kusa dashi tareda cewa  " Yaya ina wuni", "lfy lau, ykk,ya exam?", "ina lfy, exam kuma alhmdllh" ,"toh yayi kyau Allah ya bada sa'a", "Ameen, ya jiki", "well jiki yayi kyau", "Allah ya kara sauki", "Ameen, kinci abinci dan nidai yunwa nakeji", "a'a yaya", "toh me zakici", "abunda Yayana zeci shi zanci", murmushi yayi yace "angama ina zuwa", tashi yayi yaje ya karbo musu jollof rice da fried chicken da drink ya dawo tareda zama, cikin minti uku waiter ya kawo musu abincin, sunaci suna hira abinsu gwanin sha'awa, " *Lil sis* muga wayanki" dauka tayi ta mika mishi ya karba ya shiga contact dinta ba tareda tasani, number da yaga an rubuta _Luvly dad_ ya dauka yasa a wayanshi, tace "me kakeyi da wayan", "kira nakeso nayi amma numbern ma be shiga, so forget it", ya ajiye mata wayan suka shi gaba da hiransu har suka gama suka fito, ta rakashi har bakin mota inda Sameer ke jiranshi sukayi sallama ya shiga mota, seda taga wuce wansu sannan ta koma daki. "wai yaushe zaka fito ka gayawa yarinyar nan sonta kakeyi?", Sameer ke tambayan *ASHRAF*, "wen d right tym comes i will open up to her", "i wonder wen dat right tym will come", shi dai *ASHRAF* kala be kuma cewa ba har suka kai gida.

       _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHOn viuen les histories. Descobreix ara