Chapter 53

962 62 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

               *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"No need for revenge. Just sit back and wait. Those who hurt you will eventually screw up and if you are lucky, you will get to watch."

                5⃣3⃣

       *ASHRAF* ganin shiru yanata kiran wayan *ZYNAH* amma shiru bata dauka ba yasa hankalin shi tashi, nan take jikinshi ya bashi ba lfy ba, Humaira ya kira ita kuma wayanta na daki, ganin itama bata dauka bane ya kira Basma, kallon su Ammi tayi tace "Hamma ne yake kira me zance mishi", Ummi tace dauka kisa a speaker, dauka tayi tace " Hamma ina wuni", yace "lfy lau, ykk, ya mutanen gidan", tace " duk lfy", yace "ina *ZYNAH* inata kiranta bata dauka ba", kallon Ummi tayi Ummi tamata alama da tace ta shiga kara, " Hamma tana kara", "bangane tana kara ba, dazu na kira ance tana wanka, yanzu kuma kara", " Hamma in ta fito zan ce ta kira ka", haushi ne yasa ya kashe wayan yana tunanin hanya ba abunda ake boye mishi kuwa, sukawa Abba ne yace " karfe goma in bata dawo ba, semi kai report police station, haka suka zauna kowa da abunda yake ayyanawa a ranshi, wayan Fahad ne yafara ringing, ganin *ASHRAF* ne yasa ya tashi ya fita, yana fita ya dau wayan tareda cewa "look *ASHRAF* bazan tsaya ina bata maka lokaci ba, i need u to calm down nd listen to me", *ASHRAF* ji yayi gabanshi na faduwa yace " bro tell me wats wrong am becoming restless", "cool down, *ZYNAH* ce ta fita tun magrib kuma har yanzu bata dawo ba, gashi ta bar wayanta a gida", in hankalin *ASHRAF* yayi dubu ya tashi, zufa kawai ke keto mishi yace " kanaso kace min *ZYNAH* bata gida", ya tambaya muryanshi na rawa, Fahad yace "yes, bt i don't want u to panick, calm down i will b updating u, in ba lbrn ta har gobe seka san yadda zakayi kayi squeezing tym dinka kazo dan zuwan ka will help shiyasa ma nayi informing dinka halin da ake ciki", cikin sanyin murya yace " shikenan bro, update me soon", da haka suka gama wayan inda *ASHRAF* ya rasa mekr mishi dadi, tashi yayi yayi alwalah yayi nafila raka biyu sannan ya zauna yana addu'an Allah yasa a ganta.


     A haka dai Abba ganin zaman baze fishesu ga lokaci na wucewa yasa Fahad ya kaishi station inda yayi dropping complain dinshi amma dayake matsiyata ne su wai sedai a jira har gari ya waye sannan susan abunyi, sosai Abba yayi musu tatas ya zagesu yace " hakki citizens din kasar nan yana kanku, amma baku daukeshi a bakin komai ba, saboda ba damuwar ku, amma inaso kusani wlh wani abu yasamu yata shina tabbata kuncire wannan bakin kayan da kuke takama dashi, shashashai kawai, wa'anda basu san aikinsu, DPO jin hayaniya yasashi fitowa daga office dinshi, ganin Abba yayi sauri ya karasa wurinshi ya mika mai sukayi musabaha sannan yace "Alhaji Sagir kaine da daddaren nan ince dai ko lfy", Abba cikin bakin rai yace " inafa lfy, yata ta fita tun yamma amma ace har shadaya bata dawo, kuma alhalin musan ba mai wayo bace, munkawo complain wa'annan useless boys din naka suna cemin ba abunda zasu iyayi yanzu in bari se gobe", kallon su DPO din yayi duk suka saukar da kai kasa yace "kunsan ko waye wannan kuka gaya mishi wannan maganar, oya ku bashi hakuri yanzu", hakuri suka ba Abba wanda ko kallo basu ishe shi ba saboda haushi yace " DPO yanzu ya za'ayi", DPO yace "Alhaji yanzu dai a magana gaskiya dare yayi saboda haka zaku bamu details akan yarinyar kaman hotonta, shekarunta da kayan da tasa lokacin da zata bar gidan inayaso gobe da anyi sallan asuba zamu fara bincike, kuma Insha Allah zamuyi nasara wurin nemota", nan Abba yace " shikenan, amma bamusan kalan kayan da ke jikinta ba da zata fita se mai gadi na, dan shikadai yaga fitanta", "wannan ba damuwa bane, kai iliya bisu gida a tambaye maigadin ka tabbata kayi jotting necessary tins seka dawo", nan su Abba suka mai sallama suka wuce tareda police man din, suna zuwa gida baba mai gadi yabata details din kayan da tasa sannan aka bashi hotonta ya wuce su Abba kuma suka koma parlour inda suka tarar dasu Ummi duk sunyi tsuru tsuru, nan Abba yace duk suje ka kwanta zuwa gobe za'afara cigiyarta, sun shiga dakunan su ne badan barci ba sedan basu da wani abunda zasu iya yi dan zaman ba abunda ze kara musu, Humaira na komawa daki ta dauki wayanta inda taga text in KB, tana gama karantawa ta kirashi amma switched off, kwanciya tayi tafara tunanin yata zata fita gobe ba tare da wani ya ganta ba.


     *ASHRAF* duk abunda ke faruwa Fahad na gaya mishi, wanda a halin yanzu in kunga yanda *ASHRAF* ya koma sekun tausaya mishi, shi ba kuka ba shi ba tunani ba dan yarasa tunanin me zai yi, se kanshi dake uban sara mishi kaman ze tsage biyu, a cikin daren ya dau waya a kira MD din company dinsu ya shaida mishi baze samu zuwa office gobe ba saboda gida zaije akan wani dalili da ya taso MD din be musa mishi ba saboda yana son *ASHRAF* kuma ya yarda dashi saboda haka ya mishi fatan alheri, nan ya kira Sameer ya shaida mishi halin da ake ciki Sameer yace "in zaka dauki shawara na toh ku fara bincika KB dan na tabbata yanada hadi da bacewar *ZYNAH*, se a lokacin *ASHRAF* kanshi ya kawo wuta ya tuna da KB ai kuwa in KB nada hannu a ciki kashe kawai ne bazeyi ba, nan ya kwanta kaman wani mara lafiya banda tunanin *ZYNAH* ba abunda yakeyi, itakuwa *ZYNAH* tana can banda aikin kuka ba abunda takeyi, idonta duk ya kumbura yayi ja tsabar kuka har wani zafi zafi yake mata, ko abincin da Faiza ta kawo mata kinci tayi haka Faiza ta fita ta kulle kofan ta barta nan zaune a kasa hannu da kafa duk a daure ga gashinta nan duk ya hargitse saboda buga kanta data ringa a kan gado, a haka har akayi kiran sallan asuba idonta biyu ko rintsawa batayi a halin yanzu ta gaji da kukan banda hawaye da ajiyan zuciya ba abunda takeyi.


     *ASHRAF* na idar da sallan asuba ya kama hanyar Zaria wanda gudu kawai yake shararawa a titi kaman ze tashi sama, idonshi yayi ja jijiyoyin kanshi duk suntashi tsabar tashin hankali, cikin awannin da basu wuce uku ba ya kai gida wanda sosai su Ummi sukayi mamakin ganin, Abba na ganin ta kalli Fahad dan yasan aikinshi, seda ya shigo yaga yanda kowa yayi tsuru tsuru ya sannan ya tabbatar da lalle da gaske ne *DAMSEL* dinshi ya bace, zuwa yayi gaban Abba yasa mishi kuka kaman karamin yaro yana cewa "Abba dan Allah a dawo min da *ZYNAH* gidanan, Abba banaso na rasata, Abba ina sonta, wlh Abba inna rasata nima zaku rasani", Abba ne ya dafa kafadar shi cikin rawar murya dan tausayin danshi yace " bazaka rasata ba *ASHRAF*, na maka alkawarin zan dawo maka da ita gidan bazaka rasata", yanzu kaman dukansu kuka sukeyi harda Humaira, hatta Fahad seda zubada kwalla, ko Abba seda hawaye ya taru a idonshi, bame lallashin wani, sallaman mai gadi ne ya katse su ya shaida musu ga yan sanda nan a waje Abba yace "shigo dasu", yana fita Ummi cikin sheshekar kuka tace " baka ganin ya dace a kira mahaifinta", Abba yace "abunda zanyi kenan, da yakamata ya sani", daukan waya yayi  a yayin da en sanda ke shigowa aka basu wuri suka zazzauna, Abba ya kira Daddy, bugu biyu Daddy ya dauka, cikin kwantar da murya Abba ya shaidawa Daddy halin da ake ciki bayan en gaishe gaishe,Daddy halin da yashiga baya misaltuwa yace "mamana ta bace, ina zata shiga", Momsie dake kusa dashi tace " lfy , meya faru", nan ya lbrta mata abunda ake ciki, hannu Momsie ta dora a ka tana kuka tana ta shiga uku, Daddy waya ya dauka ya kira Uncle shima sosai hankalinshi ya tashi ya shaidawa Minal wacce take take fama da dan karamin cikinta na wata uku, itama kuka ta sa mai da kyar ya lallashe ta yace ta tashi ta shirya suje gidan. A ranan Daddy ya tabbata yamusu hanya sum samu sit hudu dan Islam zasu barta wurin granny dan basuma fadamata halin da ake ciki ba.


     KB bashi yaje gidan ba se karfe 10 lokacin *ZYNAH* in mutum ya ganta baze gane ta ba saboda yanda ya rame har wani baki tayi ga idonta duk ya kankance tsabar kuka, ban da Allah ya isa ba abunda take jawa Humaira, yana zuwa seda yafara tambayan Faiza ko taci abinci ta shaida mishi a'a, tace banda kuka ba abunda takeyi tun jiya, abinci ma takici, kada kai kawai yayi ya shiga dakin inda ya ganta zaune a hargitse, kallo daya ya mata ya dauke kai ya tsugunnan a gabanta yace "dama ki daina wannan kukan ki kici abinci da ya fiye miki", dagowa tayi kalleshi tace " dan Allah kwance inyi sallah, rabona da sallah tun la'asar din jiya" ba musu ya kwance ta da kyar ta mike ta shiga toilet tayi alwallah ta fito, hijabi ya mika mata ta karba tayi sallah, ta dade tana kwararo adduo'i sannan ta tashi daga wurin, abinci ya ajiye gabanta yace "ci abinci", amma dagowa batayi ba balle ta kalla plate din abinci, ganin bazata kulashi ba yasa ya kamo hannuta ya sake daure ta ya daure mata sannan ya mike yace " banda magana dake yanzu har se Humaira ta zo", fita yayi ya kulle kofan ya barta wurin tana faman zubda hawaye.


     _Yau banyi editing dinshi ba saboda ina sauri zani unguwa, duk wani kuskure da kuka gani kumin afuwa, luv u wujiga wujiga😘, waiting for comments._

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon