🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
*ZYNAH*
(An Interesting Love Story 2017)
By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)
QUOTE:- "Some people pass through our lives in a shorter time frame than we had hoped to teach us things they never could have taught if they stayed".
_I dedicate dis page to my lovely aunt *Anty Sadiya(Iyan Ummima)*._
0⃣8⃣
Duka familyn *ZYNAH* ne zaune a parlour suna jiranta ta sauko sutafi airport, sunyi zaman minti uku sai gata ta fito sanye da blue jallabiya tayi rolling kanta da pink veil. Tayi kyau sosai sai faman jan trolley takeyi. Uncle Yusuf ne yaje ya taimaka mata suka sauko shi ya wuce da bag din mota itakuma tazauna kusa da Daddy tana gaishe su duk suka amsa sannan Momsie tace"kingama shiryawa,baki manta da komai ba","eh ban manta ba".
Nan suka mata dan guntun Nasiha sannan suka fito suka shiga mota. Uncle Yusuf, Islam da *ZYNAH* mota daya sai driver ,Momsie da Daddy suma mota daban da driver dinsu. Suna fitowa se ga Humaira, parking tayi suma sukayi parking tafito taje ta gaida su Momsie sannan ta koma motansu *ZYNAH* ta gaida Uncle Yusuf ya amsa mata suka kama hanyar Murtala Muhammad Airport suna zuwa Uncle Yusuf yaje ya musu processing komai duk suna zauna kafin a kira su.
Fifteen minutes to twelve ido yafara rena fata nan Humaira ta rungumeta tace" take care of urself wen u get der " kwallan da take boyewa ne sukayi nasarar zubawa tace "i will Bestee" sannan suka saki juna ta rungume Islam tace" take care of Daddy nd Momsie ok" tace "ok sis" sannan taje wurinsu Daddy ta rungumesu tayi musu sallama itada Uncle Yusuf suka shiga departure . 12 on dot aka soma kiran suna duk suka shiga jirgin suka zazzauna. Jirgin be tashi ba sai 12:25pm , sai alokacin su Daddy suka koma gida cike da kewar ýarsu.
Yau an wayi gari en gidan Allah Sagiru Fillo sun tashi cike da farin ciki da murna saboda yau mahaifinsu zai dawo daga dogon tafiyan da yayi zuwa Ghana amma daga Lagos jirginsu zai tashi zuwa Kaduna.
Ummi da Ammi ne a babban kitchen din gidan tareda masu aiki ta fannin girke girke, sai girki sukeyi, su dora wannan su sauke wancan a yayinda Minal da Basma ke kaiwa dinning suna jerawa, kowa kaga fuskanshi zakasan suna cikin tsantsan farin ciki sai kai da komawa sukeyi.
*ASHRAF* ne ya shigo fallon da saurinshi yana kallon agogon hannunshi kirar I-watch na kampanin I phone wanda ana iya kira koma ayi receive dashi. Su Minal yagani zasu fito suka gaidashi ya amsa tareda tambayarsu "ina su Ummi" Basma tace "suna babban kitchen" nan ya nufi kitchen din yaga sunyi busy sunata aiki ya gaishe su suka amsa.
Cike da mamaki Ummi ke cemasa "Babana har yanzu baka tafi dauko Abbanku ba? kai da na cema 2:00pm jirginsu zai sauka". Wlh Ummi na makara ne bantashi da wuri ba amma yanzu zan wuce koma In Sha Allahu i will meet up". Ammi tace "a dai yi driving a hankali banda gudu kaji son" yace "toh sai na dawo tareda fita daga kitchen din ya nufi parking lot ya dau motarsa sai Kd.
Tsaki yaja ya kalli agogon hannunshi yasake jan wani tsakin kaman tsaka ganin har 1:42pm tayi amma hold up din Kaduna ya rikeshi, shi dinda yake sauri saboda ko kadan baya son Abbanshi yayi zaman jiranshi saboda ba girmanshi bane, yafi son shi yaje ya jira akan ace Abbanshi ne ke jira.
A hankali motocin ke tafiya har yasamu hanya ta bude sannan ya fara sharara gudu saboda ya kai kan lokaci. Yana isa yayi parking tareda duba lokaci yaga 2:19pm da sauri ya fito ya shiga daga ciki sai dube dube yakeyi ko zaiga Abbanshi amma ba alamunshi, nan yaje ya tambayi wani security guard ko jirgin Lagos ya sauka yace mishi a'a. Ajiyar zuciya yayi tareda godiya sanna ya nemi wurin zama ya ciro wayanshi yana latsa wa.
Zaman 10min yayi sannan yaji ana anouncing arrival din jirgin Lagos , kallon time yayi yaga 2:34pm, tsaki yayi cikin zuciyanshi yace "Nigeria will neva change, komai sai an mishi African time , jirgin da yakamata ya sauka tun biyu amma sai biyu da rabi , yanzu da mutum yana da appointment haka zaiyi miss, i don't knw wen Nigeria will change"(Ni ko nace in zaka iya ka canza mana).
Tashi yayi ya tsaya inda yasan Abbanshi zai iya hangoshi sannan yafara dube2 can ya hango shi da trolley din tura kaya lode da kaya a kai, da sauri yakarasa wurin shi ya rungume mahaifinshi tareda da fadin "welcome home Abba","thanks son","i miss u very much Abbana","I miss more son". Sannan suka saki juna cike da murnan ganin juna.
"Erm, *ASHRAF* inaso ka kai kayan nan mota, akwai wanda nakeso nagani wai yana zuwa yanzu, nan da fifteen minutes zamu gama abinda zamuyi sai muwuce". "Ba damuwa Abba, bari na tafi da kayan","yawwa". Ya kai kayan mota ya dowa ciki saboda Abbanshi be san ta inda yayi parking ba. Wayanshi yayi ringing ya tsaya ya dauka Sameer ne mai kiran, nan yasa wayan a kunne sannan yaci gaba da tafiya yana waya.
Tafe take ta bude jakan hannunta kaman wacce ke neman wani abun arziki nan ko cewing gum takeso ta ciro. Daga sama taji tayi karo da mutum jakanta ya fadi duka kayan tarkacenta suka zube, ita bata yunkura da niyyar kwashewaba haka zalika kuma bata dago ba ballantana taga wanda ya buge, shima kuma haka be kwashe ba koma be dago ba. A zuciyanta kuwa cewa take "waye wannan arrogant person din da ya buge mutum kuma ko sannu gashi kuma beda niyyar dauko abunda ya zubar" shikuwa a nashi bangaren cewa yake "wannan kuma ji kayan da take yawo dashi saikace yarinya kuma wai ta tsaya kikam kaman an shuka bishiya maimakon ta kwashe". A tare suka dago da niyyar balbale juna amma me wani shock sukaji gabayamsu marar misaltuwa, a zuciyanshi ya "Wat a beauty" itama tace "ashe dai kyakyawa ne shiyasa yake da girman kai amma zan gyara mishi zama".
Cike ta tsiwa ta bude baki tace "Mallam hala sanda kake school ba'a koya maka five magic words bane da zaka bige mutum amma koma ko sannu bare a je ga maganan tattara abunda ka zubar" shiko ba abunda yakeyi sai kallon red lips dinta, sai da ta gama sannan yayi murmushi yace " Mallama ba'a koya min ba ko zaki koya min" bata kai ga bude baki ba ya hango Abbanshi zuwa kawai sai ya wuce, a hankali tace "so arrogant" yajiyo yace mata" i heard u" sannan ya wuce ,sosai mamaki ya kamata saboda batayi zaton zaiji ba kawai sai ta tsugunna ta fara tattare kayanta.
Muryan Uncle Yusuf taji yana cewa " *ZYNAH* keda nace kijira in nemo taxi ina kika shiga" tace "Uncle na shigo ne saboda in zauna dan nagaji sai kuma wani ga bugeni shina na tsaya dauke jakata","naji muje me taxi na jira a waje" nan suma suka fita suka shiga taxi din tareda cema me taxi din "Zaria zaka karasa damu" yace " yallabai saidai na kaiku tasha inda zaku samu motan Zaria","ok muje ba matsala". Nan ya kaisu tasha suka shiga motan Kaduna to kano amma zasu sauka a Zaria. *ZYNAH* cikin ranta tace "tunda nake ban taba shiga mota haya ba amma yau Allah Allah kawo ni na shiga duk na takure kuma wai kudi za'a biya a hakan".
_Toh readers yau ga *ZYNAH* a hanyar Zaria Zazzau, ku biyo danjin yanda wannan lbr zata kasance nan gaba_
_Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_
YOU ARE READING
ZYNAH
Mystery / ThrillerHere is a story of a teenage hausa girl Zynah who happens to come from a wealthy nd peaceful family but was hated by her younger sister whom she loves a lot, nd betrayed by her bestfrnd whom she tells all of her secret, nd unknowingly fall for a gu...