Chapter 14

1.1K 74 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

QUOTE:- "It's a very dangerous state. You are inclined to recklessness and kind of tune out the rest of your life and everything that's been important to you. It's actually not all that pleasurable. I don't know who the hell wants to get in a situation where you can't bear an hour without somebody's company."

     _I dedicate dis page to my cutest nd lovely bt unbearable twins so far *Hassana (Boss😜)* nd *Hussain (Al gosh😂)* karki damu zanzo na mulmula goshin ko ya ragu😂. I so much luv u my twins. Hrt u babes❤_

                 1⃣4⃣

     Sun gama komai suka wuce hotel dinsu bayan sunyi sallama da Ashanty suka sanar da ita suda dawowa se lectures ya kankanma. Da shigarsu hotel din wanka suka farayi saboda su rage gajiya dan gajiyan yau daban ne, suna gama wanka sukaba cikinsu hakkinsa dayeka sun riga sunyi sallah kafin su dayo. Bayan sun gama cin abinci sun nutsu Uncle yace " *BEAUTY* tunda mungama abunda ya kawo mu kuma yau Wednesday, gobe se muwuce Kano wurin granny kinga zamu iya mata kwana biyu ran Saturday se mukoma gida" cikin tsananin jindadi tace " Hakan za'ayi, bari naje nafara harhada kayana" yace " tsaya tukunnan kira mana granny mu shaida mata, tunda wannan ne first zuwanmu a motan haya in mun sauka bamusan ina kuma zamu nufa ba"," gaskiya Uncle bari na kirata" ta dau wayanta ta kira bugu biyu aka dauka tace " Ranki ya dade tsohuwa  me ran karfe" ta daya bangaren akace "tareda dana naki kishiyar zamani" dariya sukayi gaba dayansu sannan *ZYNAH* tace "granny ina wuni","lfy lau, se yau aka tuna dani er jikalle, kwana biyu ba waya","wlh granny nayi busy ne ina registration din school dinda na samu"," haka mahaifinki yace wai a Zaria ko","eh granny","toh da kyau yanzu kun gama","mun gama yau,gobe zamu shigo Kano nida Uncle","a'a'a kice zanyi manya baki Allah ya kaimu","Ameen,amma in mun sauka tasha ina zamuce ma me taxi zamu daga nan","ai bazama kukai tasha ba, motan haya zaku biyo","eh" ,"toh , in kunshiga mota kuce ma drivern ya sauke ku a sani brothers Na'ibawa kinsan mu bamu shiga can ciki ba, inyaso da motan ku ya tashi se kimin waya zansa a dauko ku daga nan"," ok Sani brothers ko","eh","toh ba matsala tsohuwa se goben","Allah ta kaimu" da haka sukayi hang up call din ta fada ma Uncle abunda Granny tace, yace "shikenan ba matsala se goben".

     Tashi tayi ta kuma dakinta ta kira Daddy ya dauka "Mamana kashe in kira" abunda yace kenan ya kashe wayan ya sake kiranta alokacin suna zaune da Islam a parlour Momsie kuma na kitchen Islam duk ta cika tayi pam zata fashe cikin zuciyan ta tace "wato ma kartayi  waste din call card dinta shi ze kira, tsaki taja a fili amma Daddy kwata kwata hankali sa be wurin ballantana yasan da mutum. Cike  da takaici ta tashi ta bar parlourn ta koma kitchen tana taya Momsie da Jummallo hada dinner. "Daddy mungama komai cikin sauki amma se Thursday zamu dawo saboda zamuje Kano muyi kwana biyu wurin Granny" *ZYNAH* kenan tanata korowa babanta sharhi "Toh da kyau, Allah ya miki albarka ya baki ladan ziyara","Ameeen" haka sukaci gabada hira har seda taji kiran sallah sannan sukayi sallama suka kashe wayoyinsu, yanata zuba murmushi shi kadai, shidai harga Allah besan iyakacin kaunan da  yakema *ZYNAH* ba dan tunda aka haife ta yake mata  wani irin son da besan adadinshi ba. "Kai da wa wannan murmushi haka" Momsie ke tambayanshi ganin yana cikin farin ciki yace "yanzu nagama waya da Mamana" shiru tayi ta juya ta kalla Islam take jera kololi kan dining sannan tace " Ya take, yau bamuyi waya ba","wai tana lfy sunma registration ran Saturday zasu dawo saboda zasu biya Kano"  tasssssssss sukaji karan fashewar plates daga hannun Islam wanda saboda maganan da Daddy yayi na dawowan *ZYNAH* yasa plates din faduwa dan harga Allah bataso *ZYNAH* ta dawo. "Lfy, ya akayi haka, ba kiji ciwo ba" Daddy ke tambayar ta tace "a'a banji ba" Momsie kaman zatace wani abu se kuma tayi shiru ta kira Jummallo ta gyara wurin. Sukuma suka wuce dakunansu dan gabatar da farilla.

**********
          *Zaria 8:30pm*
*Gidan Alhaji Sagiru Fillo*

     Zaune suke kan dining suna cin abinci, Juwairriya tace "Abba jiya Hamma *ASHRAF* yajamun kunne wai saboda Anty tace inada tsokana" kowa kallonta yake, *ASHRAF* a zuciyan shi yace kaga munafuka zan kama ki. Abba yace "Bari mu gama cin abinci zan hukunta shi, amma yanzu kiyi shiru ba kyau cin abinci ana surutu kinji" ta kada tana jindadi ta kalli inda *ASHRAF* ke zaune suka hada ido ya balla mata harara tace "Abba" Abba yayi saurin sa hannun shi abakinta alaman tayi shiru dayake kusa dashi take zaune. Ai kuwa tayi shirun amma ta daure fuska ita bata yadda ba fushi takeyi(lol). Sun gama cin abinci suka koma parlour aka bude shafin hira amma banda gimbiya Juwairriya wacce take ta kallon Abbanta taga wani mataki  ze dauka akan *ASHRAF*, ganin yayi shiru bema dauko  zancen ba yasa tace "Abba kace zaka hukunta Hamma *ASHRAF*" kafin Abba yayi magana Ummi ta rigashi da cewar "karki bari in saba miki yanzun nan, dan tsabar rashin kunya shi ba wanki bane, be isa ya hukunta ki in kinyi ba daidai ba, in karajin kin kai karan wani kuma, in akwai sa'anki anan kya fada mun" kuka take sosai harda jan main, suko yayyenta duk sunji dadin yadda Ummi ta sulle ta dan dama ko wannensu na ciki da ita banda Haydar dan shi da  ita  5&6 ne.

     Abba ma yaji dadin tsawata mata da akayi amma saboda a samu tayi shiru yace " Ummi kinsan yarinya ce a dinga sassautawa" dayake Ummi ta gane nufinshi se batace komai ba, Ammi tace "toh kukan ya isa kinji" tayi banza kaman bataji ba, Abba yace "taho kyalesu" ai kaman jira takeyi ta dane cinyar Abba ya lallashe ta tayi shiru da haka barci ya dauke ta sukaci gaba hiransu. Duk sunyiwa Abba sallama zasuje su kwanta yace "Allah  ya bamu alheri, kai Haydar dauki Juwairrya kaita daki, Fahad da *ASHRAF* ku sameni daki" sukace "toh Abba" kowanen su ya kama gabanshi. Tareda Abba suka shige daki ya  zauna bakin gado sukuma suka zauna kasa suna jira suji me ze ce musu. Seda yayi gyaran murya sannan ya dubesu yace "yau da asuba da zanje masallaci na biyo ta bangaren ku amma se naji hayaniyar ku, ganin kun tashi yasa ban shigo ba, yanzu ina so inji dalilin hayaniyar" tsayawa yayi yana kallonsu yana jiran yaji ta bakinsu, Fahad duk yagama shan jinin jikinshi yana gani *ASHRAF* ze fadama Abba yayi shaye shaye  ne a daren jiya amma se  yaga akasin haka. *ASHRAF* ne ya daure yace "Abba ba komai dama akan na karar mishi da kudin waya ne" Abba ya nisa sannan yace "toh ku kula kunga kune manya a gidan nan yanzu, u need to lay a gud example kunji ai" Fahad yace "munji Abba In Sha Allahu zamu kiyaye","da kyau, Allah Allah ya muku albarka" suka amsa da "Ameen" sannan ya sallame su, suka  mai  seda  safe  suka  fito. Fahad yace "tnx  for  covering up for me"," Don't thank me nw cus d day i  will  get  tired  of covering up for u i  will  have no choice bt to open up" yana gama maganinshi ya kara gaba ba tareda yajira me Fahad din zece ba, shima bayanshi yabi kowannen su ya shige dakinshi.

     _Wai hannuna typing is nt easy._

       _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now