Chapter 35

1K 75 2
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"Life is never about the people who act true to your face It is always about the people who remain true at your back."

      _I dedicate dis page to *Aseeya(A B U)* tnx for d support swthrt, hrt u bae.❤_

                3⃣5⃣

     Karban file din yayi sannan ya musu sallama ya fita Daddy yabi bayanshi, suna fita   Uncle Yusuf yace "congrat *BUEATY* se akara himma aci gaba da maida hankali", Momsie kuwa kallon Islam tayi tace "toh kinga abunda nutsuwa da maida hankali akan karatu ya bata, kema inzaki maida hankali ki maida, in bahaka ba haka zakita zama da zukancin ba ci gaba", kallonsu *ZYNAH* takeyi dan ko kadan batason yanda suke tsangwaman Islam, tashi Uncle Yusuf yayi yace yanada wurin zuwa, sannan Momsie ma tace bari taje ta karasa girkinta. Daki ya saura daga *ZYNAH* se Islam, tasowa *ZYNAH* tayi tazo ta zauna kusa da Islam tareda riko hannunta tace "lil sis u need to change, change ur lyf style for d bst, abunda kikeyi bazeyi helping dinki ba, ya kamata ki gane cewar duk abun nan dasu Momsie suke miki ba dan komai sukeyi ba sedan ki canza, amma kinki ganewa, pls lil sis u hav to change for ur own gud, ke kinajin dadin abunda akemiki a gidan nan, eh", wani harara ta makawa *ZYNAH* tareda jan dogon tsaki ta tashi tafita, da gudu ta shige dakinta tareda fadawa kan gado tasa wani marayan kuka, tana fadin "laifina ne da bani da kokari kaman sister, ko kuwa laifina ne da ban da kaifin hada, ba laifina bane, y can't u guys understand me for once",(na dai nace laifinta ne dan tafi bama film din Barbie himma akan karatu),haka taci gaba da kukanta har ta godewa Allah dan bame lallashin ta.

     "Alhaji be kamata kabarma er ka wannan documents din a hannunta ba, it's risky, dats y nace kabani inyi photocopy dinshi, yanzu zanje nayi three copies of dis, zan ajiye original file din hannuna, sannan zan baka daya, ita semu bata fake documents din for safety purpose", Daddy ya kalli lawyer dinshi yace "it's okay, since u think dats d ryt tin to do". Nan lawyer yama Daddy sallama ya wuce, Daddy kuma ya koma cikin gida. *ZYNAH* na daki se murna takeyi Daddy ya siya mata fili, itama za'a gina mata hospital na kanta. Daukan wayanta tayi ta kira Humaira tana fada mata abun alherin da Daddy yayi mata, sosai Humaira ta tayata murna, suna cikin waya da Humaira *ASHRAF* ya kira, tayima Humaira sallama sannan ta dauka call din *ASHRAF* hira sukasha sosai shima ta fada mishi an siya mata fili, ya taya murna sosai shima, da haka suka cigaba da hiransu Islam dai ana chan bakin ciki ya hanata sakat.

*BAYAN KWANA HUDU*
     *ZYNAH* ana nan anata shirye shiryen komawa school, duk wani abu da tasan zata bukata seda ta tanade shi, ana gobe zata wuce  school Daddy yake fada mata cewar gidansu *ASHRAF* zata sauka in ta koma, bata musa ba tayi na'am da shawarar su ba dan komai ba sedan a ganinta zata iya dodging din KB, gobe ne tafiyanta wanda Uncle Yusuf ze rakata, Humaira ma tace zata rakata saboda sun gama exam, amma sati daya zatayi, whereas Uncle Yusuf kwana daya zeyi ya dawo saboda aikinshi, Islam ma ance ta rakata amma tace ita bazata iya ba. Ita dai *ZYNAH* tayi abunda zatayi an kuma bata documents dinta a hannu wanda taje ta bude wardrobe dinta na kayan Jallabiya, raba kayan tayi gida biyu seta ajiye documents din sannan ta dora sauran kayan akai, ba wanda ze kalla yasan da ajiya a wurin.

*WASHEGARI*
     Tun karfe goma Humaira ke gidan dan jirgin twelve zasubi, kafin eleven duk sun gama abunda zasuyi sun sukaje airport, ba dadewa jirgin su ya tashi se Kaduna, karfe biyu da en mintina suka sauka a Kaduna, numbern *ASHRAF* *ZYNAH* take kira yace mata ai yana waje, direction din inda yake ya musu, sukaje suka sameshi, yakasa boye jin dadinshi na ganin *ZYNAH* dan ji yake kaman yaje ya rungumeta, bdan ba ita kadai bace da ba abunda ze hanashi rungumeta ba. Zuwa  yayi ya musu iso zuwa inda yayi parking, shiga motan sukayi suka zauna, Humaira se sake sake takeyi a zuciyarta saboda *ASHRAF* ya gama tafiya da imaninta (tirkashi). Gida suka wuce straight, en gidan duk sunyi maraba da zuwan su aka basu masauki, Uncle Yusuf dakin Fahad ya sauka, se su Humaira ta sauka dakin da aka ware ma *ZYNAH* wanda dakin yayi kyau sosai, wallpaper aka samata, combination of purple nd pink, dakin yayi kyau sosai kaman dakin sauran yaran gidan, suna hutawa aka kawo musu abinci sukaci, Ummi ce takira Minal tace ta kaiwa Uncle Yusuf abinci, dauka tayi ta tafi, da sallama tashiga dakin, daga ciki aka amsa sannan aka bata izinin shigowa, yana kwance akan gado yana danna waya ta shigo, "wai ga abinci nan, kaci", amsa wa yayi da "toh" tareda dagowa, freeze yayi ganin wacce ke gabanshi, har ta kai bakin kofa sannan ya farka yayi sauri yace "dan Allah dan tsaya kiji", juyowa tayi tareda cewa "kana bukatan wani abu ne", "a'a, ammmm, uhmmm, dama", haka ya tsaya yana kame kame, ya rasa me zaice mata, kwata kwata yakasa mata magana kuma shi yasan ba haka yake ba, kai tsaye yake tsara mace, saboda yasan dole tayi fall, amma wannan karon seya rasa me zaice mata, zama yayi tareda cewa "in bazaki damu ba dan zauna akwai maganan da nakeso muyi", cike da mamaki tace "wani irin magana zamuyi, da bazamu iya yinshi a tsaye ba", kallon ta yayi dan yasan inda ta dosa yace "kinga ba wani abu bane, magana ce da bazata wuce ta minti uku zuwa biyar ba", "naji yi magananka inaji", "bazaki zauna", "a'a nan ma yayi", ganin batada niyyan zama yasa shi ya tashi ya matso kusa da ita sannan yafara magana "abunda nakeso na fada miki, ba komai bane illa, tun randa na fara ganinki a hospital kika shiga raina, dan tun ranan har yau nakasa manta ki, se kuma gashi yau Allah ya sake hadani dake a cikin gidanku, wannan kadai na nuna akwai abunda Allah ke nufi damu", murmushi tayi tace "ayhhh, ai nan ba gidan mu bane, er aiki ce ni anan gidan", dariya yayi ganin tana neman ta raina mai hankali yace "naji ke er aiki ce, amma ai naga kinyi kamada en gidan sosai, musamman *ASHRAF*, da gani daki daya kuka fito", "a'a tsananin dadewa da nayi ina aiki a gidan yasa kaga kaman nayi kama dasu, amma ai bama kama", gyara gashin kanshi yayi da hannu tareda shafa gemu sannan ya kalleta yace "kinsan dai ni ba yaro bane, koma kema ba yarinya bace, saboda haka ki bari mudaina wasan yara, let's face reality, tsakanina dake abu daya ne, shine inaso ki, nd believe me if i say it was love at first sight, ni ba takura ki nazoyi ba, gobe da yamma zan wuce, saboda haka zan baki daga yanzu zuwa gobe, kije kiyi tunanin da zuciyarki, nd i promise wat ever ur decision is, i  will respect it", ganin yanda yayi serious yasa tace "naji, zanje nayi tunani amma don't expect me to say yes ryt away", "sure, take ur tym", batace komai ba ta fita shikuma ya koma kan gado ya kwanta tareda tsurawa ceiling ido.

     Minal dakinta ta wuce tana tunani, wani irin amsa yakamata ta bawa Uncle Yusuf, itadai tasan yana daya daga cikin irin mazan da takeso, toh amma bata sanshi ba, bata san ya halayenshi yake ba, gashi bataso tace mishi a'a saboda taga alamun seriousness a tattare dashi, gashi itama ko ba komai lokaci yayi da yakamata ace tanada tsayayye wanda ko yaushe akace ta fito da miji zata fito dashi dukda bawai ta rasa samari bane, a'a tana dasu sedai duk yara ne, en 23 24 itakuma tafison ta aura wanda ke cikin late twenties dinshi ko kuma early thirties dinshi, gashi ta gama schooling dinta, ta gama koyan catering, ta gama koyan bead work, tana last stage dinta na gama koyan dinki, toh yanzu me abunyi???  Abunda ta tambaye kanta kenan, kwakwalwarta yabata da taje wurin *ZYNAH*, zatasamu amsoshin tambayarta. Tashi tayi ta nufi dakin da *ZYNAH* take tayi sallama tashiga, taga Humaira na barci, whereas *ZYNAH* kuma na revision saboda a goben zaka koma school, karasawa tayi wurinta tace " *ZYNAH* karatu like?", "eh adda Minal(haka taji su Basma na kiranta)", "gashi kuma wurinki nazo", "da abunda kikeso nayi miki ne", "eh toh magana nakeso muyi in bazaki damu", juyowa *ZYNAH* tayi sosai tace "ba damuwa, fill free", kallon Humaira Minal tayi sannan tace "Humaira na barci, muje garden kar mu tashe ta", ba musu *ZYNAH* ta tashi ta dau mayafin abayar ta tareda bin bayanta suka fita.

     Direct garden suka wuce, inda suka samu wuri suka zauna sannan Minal ta fuskanci *ZYNAH* tace "maganan nan da zamuyi dagani sai ke, banson kowa yaji", kulle bakin *ZYNAH* tareda jan hannu alamun tayi zipping din bakinta sannan Minal tace "Uncle dinki yazomin da wata magana, kuma he's serious abt it amma kuma ni i don't knw wat say to him", damm gaban *ZYNAH* ya fadi a zuciyarta tace "kardai Uncle yana nema yayi playing adda Minal ne as well, indai hakane toh ni bazan bari ba, komai ta tambaye ni akanshi fada mata zanyi" dawowa tayi tace "wani magana kukayi dashi", "cewa yayi yana sona", a zuciyarta tace "nasan a rina", Minal tace gabada "kuma bansan me zance mishi ba, gashi i don't want to let him down", kallon tausayi *ZYNAH* tawa Minal sannan tace "ni me kikeso nayi miki yanzu", gyara zama Minal tayi sannan tace "so nake ki bani lbrn shi duk wani details nashi, karki bar komai Dan dashi zanyi judging case dina dashi", gyara zama *ZYNAH* tayi tace indai wannan ne ba matsala, da farko dai Uncle Yusuf kenin mom dina ne frm same parents, he is 28yrs getting close to 29 amma he is a bad guy", Minal ji tayi gabanta ya fadi, ganin yanayinta yasa *ZYNAH* tace "kwantar da hankalinki, abunda yasa nace he is a bad guy saboda maganan gaskiya tsakani da  Allah my uncle is a player, in kinga yana soyayya da mace toh na lokaci kadan ne, amma ur case is different saboda keda kanki kince he was serious while talking to u, kuma ni na san uncle dina, he never gets serious wit girls", Minal ji tayi gabadaya gabobin jikinta sunyi sanyi tace "kar dai nima playing dina yakeso yayi", *ZYNAH* tace hanya daya ce kawai dazaki iya gane haka, Uncle dina baya bin mace sau biyu, idan yace yanason mace tayi rejecting dinshi toh ya barta kenan, saboda haka ki nuna mishi bakya yi dashi, idan yaci gaba da bibiyarki toh da gaske yayi", "godiya Minal ta mata sannan ta tashi zata shiga ciki, *ASHRAF* ta hango yana tahowa, Minal ta tabo *ZYNAH* tareda nuna matashi, barin wurin tayi shikuma ya zauna tareda jan ta da hira. (Manya abun nema yasamu.)

      _Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now