Chapter 55

1K 76 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻


              *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"When you focus on problems, you will have more problems. When you focus on possibilities, you will have more opportunities. Dream, Wish, Make it happen."

                 5⃣5⃣

      Daddy da Uncle ne a compound din gidan a tsaye Daddy ya dau waya ya kira Abba ya shaida mishi sun iso suna gida, Abba yace yana station amma gashi nan zuwa, duk yanda Daddy yayi da Abba akan ya bari yazo station din Abba ya kiya yace suma yanzu zasu dawo, dole Daddy ya hakura Ummi tasa aka bude musu parlour Abba suka shiga aka kawo musu kayan marmari amma su bashine a gabansu ba, karfe uku su Abba suka dawo gida tareda DPO, suna zama suka gaggaisa sama sama sannan DPO yace a kira sauran en gidan saboda kome za'ayi ayi a gabansu, dukan su sun hallara harda baba mai gadi inda DPO ya fara da "baba mai gadi kace kaga fitanta da gabanin magrib da zata fita ta rike wani abu a hannu ko kuwa", shiru baba mai gadi yayi kaman me son tuno wani abu sannan daga bisani yace " tabbas naga wayanta a hannunta, dan tanama dannawa ne tana tafiya", kallon Humaira Ummi tayi tace "amma kince min bata fita da waya ba", nan kowa idonshi ya dawo kan ta nan ta fara kame kame alamun rashin gaskiya, Ummi tasake cewa " dake fa nake", tace "eh Ummi nida na fito daga wanka naga wayan a kan gado", DPO yace " ya isa", sannan ya kalli baba yace "kuma bakaga shigowan ta ba, kila ta dawo ta ajiye wayan ta sake komawa", wannan karon yana magana ne yana kallon Humaira dan yafara tunanin tasan wani Abbu, baba yace " bangani ba, dan har na tafi masallaci bata dawo ba", DPO yace "shikenan baba mun gode, zaka iya tafiya", baba ya tashi ya fita sannan DPO ya juyo wurin Daddy yace " kaine mahaifin yarinyar koh", Daddy yace "eh nine", " toh karkusa damuwa a ranku, kuma cin bakin zaren wannan almari saboda koyaya akayi wannan kidnappers din ba kudi sukeso ba, dan da kudi sukeso da yanzu sun tambaya, ka ganin baka da wani abokin harka dakeso yaga bayanka", Daddy yace "babu", ya juya wurin Abba yace " kaifa", shima yace "babu", ajiyar zuciya DPO ya sauke yace " a miko min wayanta ingani", tashi Humaira tayi da nufin zuwa dauko wa amma DPO yace tayi zamanta sannan yace Basma taje, kan dressing mirror Basma taga wayan ta dauko ta mika wa DPO ya karba ya kunna yashiga call history amma last call dinta shine wanda *ASHRAF* ya kira batayi pick ba, kiran da Humaira ta mata kuwa duk ta goge shi daga wayan, DPO ganin bega abunda yake nema bane yasa ya mika musu wayan ta sannan yatashi ya ce zai tafi amma har yanzu sunanan kan bincike saboda haka ze iya dawowa at any tym sannan suka mishi sallama ya fita.


     *ASHRAF* ne ya mike ze fita, amma se gani sukayi ya dafe kirjin shi wurin zuciyanshi dake harbawa kaman ze tsaga kirjin ya fito, Fahad ne yayi sauri ya karasa wurin shi ganin yana neman faduwa aikuwa ragwab ya zube jikin Fahad yana numfashi sama sama ga idon shi yana neman kafewa, ai kuka nan parlour matan suka sake dasa sabon kuka, Uncle ne ya taimaka ma Fahad suka dagashi aka sa shi mota se asibiti inda su Abba suka bi bayansu (Allah sarki ciwon so😭), kuda sukaje asibitin oxygen aka fara sa mai saboda yayi supporting numfashin shi sannan suka fara bashi taimakon gaggawa, Fahad ne yaja Uncle suka fita compound din hospital din sannan yace "akwai abunda nakeso na fadama a matsayin ka na criminologist",  Uncle yace " inajinka", Fahad yace "nifa ina suspecting Humaira akan wannan case din", nan da nan Uncle yace " haba haba haba Humaira fa kace, kasan yanda suke, kawar *ZYNAH* ce fa tun suna yara", Fahad yace "nasan kawarta ce amma ban yarda da ita ba", Uncle yace meyasa kace haka", " saboda na daya, a ranan da *ZYNAH* ta bata ni na hadu da Humaira a gate tana shigowa nikuma zan fita zuwa masallaci dan lokacin har an kira sallah, kuma d way i saw her she was panicking, na biyu cikin zancen baba mai gadi be kawo cewar yaga fitan Humaira ba bare shigowan ta, sannan na uku Humaira tace tana wanka sanda *ZYNAH* ta fita, kuma *ZYNAH* ta fita gabanin magrib whereas Humaira ta shigo gidan ana sallan magrib, na hudu Humaira tace *ZYNAH* bata fita da wayan ta ba amma baba maigadi  yace yaga waya a hannun *ZYNAH* to waze dawo da wayan", shiru Uncle yayi yana nazari yace "gaskiya kanada clue dayawa amma meyasa baka fadawa DPO ba kake fadamin", " saboda inaso mu kamata red handed ne tukun", Uncle ne yace shikenan kaga ni yanzu banzo da laptop dina ba saboda haka da naka zamuyi amfani, in dan mun koma gida akwai wani bug (wani karamin camera ne wanda tsabar kankantar shi za'a iya ajiyewa kusa da kai amma bazakabgani ba) zakaje ka makala jikin jakanta dan nasan yanzu komai zatayi batayi a idon mutane ba se a daki saboda haka inkasa mata wannan bug din komai takeyi zamu gani", Fahad yace "shikenan, bt i pray ba hannunta ciki saboda i lyk dat girl", kafadan shi Uncle ya daka sannan yaja hannunshi suka koma cikin asibitin.


ZYNAHWhere stories live. Discover now