Chapter 42

903 66 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

            *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"Life would be perfect if, some girls had mute buttons, some guys had edit buttons, bad times had fast forward buttons, and good times had pause buttons."

                4⃣2⃣

     Zuwa yayi wurin *ZYNAH* ya tallafo kumatun ta tareda kare mata kallo, hawayenta ya share mata sannan yace "ar u ok", kada mai kai tayi sannan yaja hannunta suka yi gaba suka bar wurin Sameer yabi bayansu, kowa a wurin  kallonsu ake ga KB a kasa yakasa tashi saboda naushin da yasha seda ya gode ma Allah, wasu ne sukazo suka kawo mai agaji suka kai shi asibiti. *ASHRAF* yana barin wurin bench ya samu suka zauna yace "me ya kai ki love garden, me kika je nema a wurin?", kwashe mishi yanda akayi taje wurin tayi ta fada mai yace "in kika ga girl din zaki ganeta", "eh zan ganeta", "gud, yanzo wurin HOD din mu zamuje, ki fada mishi duka abunda KB ke miki tun zuwan ki school dinnan saboda a mishi katangar karfe dake". Office din H O D dinsu sukaje, nan *ASHRAF* yace mishi karan KB ya kawo, komai seda suka fada mai gameda KB ba abunda suka boye, harda dukan da yama *ASHRAF* duka seda suka fada, sosai H O D din yayi mamaki, dan shi duk tunanin shi halin KB shayeshaye da zukanci da bribing lecturers ne kawai, ashe abun nashi yafi haka, abun nashi yayi tsamari, dole yama *ASHRAF* alkawarin ze dau mataki nan bada dadewa ba, godiya *ASHRAF* yayi sannan suka bar office din. Gida ya kaita tareda kwantar mata da hankalinki sannan ya bari ta shiga ciki.

      A ranan seda aka kira both teaching nd non teaching staffs meeting  akan case din KB inda cikin 100%, 70% din lecturers sunce abunda ya dace ayi shine ayi rusticating dinshi, inda wasu sukace  a'a (masu dogon baki da karban bribe kenan) a duba matsayin mahaifinshi kafin a zartar mai da hunkuci saboda haka a bashi warning first, nan dai kowa keta fadan albarkacin bakinshi, dama ance majority carries d vote saboda haka sun tsaida magana akan zasuyi rusticating dinshi, amma ganin yana last year dinshi kuma exam yakeyi yasa suka canza shawarar cewa a bari ya karasa semester dinshi tunda daga wannan shikenan ya bar school. Dukkansu sun amince amma da sharadin zasu kira mahaifinshi su gayamai abunda danshi yakeyi saboda yaba danshi warning, daga haka aka rufe meeting din.

    An kira mahaifin KB aka koro mishi abubuwan da danshi yakeyi a school amma ya rufe ido yaci musu mutunci wai sharri akama danshi, shi yasan danshi baya neme nemen mata amma yana shayeshaye (Allah ya rabu da iyayen da suna ganin laifinmu amma suyi kaman basu gani ba da sunan sonmu sukeyi nan kuwa suna cutarmu ne "Ameen"), haka mahaifin KB yabar school din ranshi a bace wai ana aibata mishi yaro dan sun ga ya musu zarra (daurewa karya gindi), KB kwana daya yayi a asibiti yace shi a sallameshi ya tsani warin asibitin, ba yanda nurses din suka iya dole suka kyaleshi ya bar asibitin, guest house din shi yaje SMART yazo ya sameshi yana tambayarshi abunda ya faru, be boye mishi komai ba ya fadawa SMART duka abunda ya faru sannan ya kara da cewar "zan musu shiru yanzu, bazan kuskura inkara bi takan yarinyar nan ba amma kuma ba wai na hakura bane a'a, kumin daren dadewa, ko shekaru nawane zan dawo, bazan taba barinta ba harse na cimma burina akanta", shidai SMART shiru yayi yana tunanin karfin hali irin na oganshi. Yana Kallo KB ya dau waya ya kira Humaira, dauka tayi tace "hello", "inaso kisani, komin daren dadewa *ASHRAF* naki ne karki fidda rai akanshi, ni KB na miki alkawarin wannan, amma inaso duk sanda na nemi hadin kanki toh ki bani, koda nan da shekara biyar nan, karki goge number na a wayanki kaman yanda bazan goge naki ba saboda zai mun amfani kaman yanda kema ze amfane ki nan gaba", dif ya kashe wayan batare da tace komai ba, kallon wayan ta tsaya yi a yayinda tunani kala kala suka fara bijiro mata na hanya KB kalau yake, ganin ba amsa yasa ya ajiye wayan taci gaba da hada kayanta.

*WASHEGARI*

     Koda *ZYNAH* taje school ta hadu da KB amma ko kala bace mata ba, in fact bamayi kaman ya santa ba, sosai taji dadi dan a tunanin ta ya hakura ne, ranan kowa ya ganta yasan tana cikin jin dadi da farin ciki, karfe biyu ta bar school din saboda Fahad zeje ya dauko Momsie, Islam da Humaira daga airport, shi Daddy se ana gobe birthday dinta zezo saboda yanaso a fara tada ginin asibitin *ZYNAH* (anzo wurin🤔), tana zuwa gida wanka tayi ta shirya cikin peach kimono da black veil sosai tayi kyau, kasa ta sauko Ammi tace "Anty zumudi ai jirginsu be isa sauka ba tukun", murmushi tayi tace "zamuje mu jirasu", gaba dayansu dariya suke mata ganin yanda take zumudin zuwa tarbo yan uwanta, Fahad ne yace "toh muje, semu jira su", ai kafin ya gama magana harta miki, sosai ta basu dariya sunata zolayanta, ita kuwa murna ganin en uwanta kawai takeyi, ji take dama tazama tsuntsuwa dan ta kai airport din cikin en mintina abunta, cikin mota se janta da hira Fahad keyi ita kuma dayake bawani sakewa tayi dashi ba daga "eh" se "a'a", da haka suka karasa airport din.

     Koda sukaje airport din seda sukayi zaman jira har wurin 15min sannan jirginsu ya sauka, tana hangosu ta karasa wurin su da gudu tareda kaiwa Momsie wani wawan hug, dariya Momsie tayi tace "karya ni ki huta", dariya tayi a yayinda ta rungume Islam sannan ta rungume Humaira, sosai taji dadin ganin su, Fahad ne ya karaso har kasa ya tsungunna ya gaishe da Momsie saboda kallon sirikar shi yake mata (lol), "kaine Fahad", Momsie ta tambayeshi ya amsa mata da "eh", tace "Allah yayi albarka", ya amsa da "ameen", sannan yayi leading dinsu zuwa wurin mota, wannan karon Islam ce ta zauna a gaba itakuma *ZYNAH* tana nan ta makale jikin Momsie wanda lokaci lokaci Fahad ke satan kallon ta mirror. Suna kaiwa gida en gidan suka fito suka tarbesu, sosai Momsie taji dadin tarban da aka musu, a part din Ammi aka ba Momsie masauki, itadai Islam tace dakin *ZYNAH* zata kwana Humaira ma haka, dukkan su parlour suka fito suka zauna badan iyayensu dasuke part din Ammi suma suna nasu hiran, Haidar na shigowa gidan yaci karo da baki, amma still be bar shakiyancin shi ba, zuwa yayi wurin Basma yayi wani magana ko wani yare zance, Basma tace"na'am", yace "gaisuwa nakeyi", tsaki taja saboda ya kullar da ita sannan ya kalli Islam  yace "Basma wannan fine girl din fa?", kallon shi tayi tace "Kanwar *ZYNAH* ce", mika mata hannu yayi yace "Am Haidar Sagir by name aka coolest kid", Basma ce tace "hmmmm coolest kid indeed", kallonta yayi ya basar ya maida hankali shi kan Islam "Am Islam Muhammad by name bt sorry i don't shake hands wit boys", gabadaya parlour dariya suke mai saboda yanda ta reject kin shaking dinshi, basarwa yayi yace "no big deal", nan yata janta da hira itama tana biye mishi har lokacin sallah yayi suka tashi dan suyi sallah.

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now