Chapter 57

957 69 1
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻


               *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"It's funny how you can do nice things for people all the time, and they never notice. But once you make one mistake, it's never forgotten."

               5⃣7⃣

     Fahad ganin abunda ke faruwa ne yasa hankalinshi ya tashi ya bude motan ze fito Uncle yayi sauri ya rikeshi yace "ina zaka?",  Fahad cikin tashin hankali yace " zan je inyi rescue dinta ne", Uncle yayi murmushi yace "ai she's already rescued, mu jira zuwan su DPO saboda yanzu idan muka fita zamuyi alerting dinsu ne kaga zasu samu daman guduwa tunda sun fimu yawa", Fahad kanshi ya dora kan steering yana tunani sukaji sirin din en sanda ai da sauri ya dago yace "sun karoso", fitowa sukayi daga motan a yayin da su SMART duk suka diriri ce dan sun san tabbas yau dubunsu ya cika, Humaira ma jin sirin din en sanda yasa hankalin ta yatashi a nan take ta kara kankame *ZYNAH* a jiki tana kuka tana cewa " plss forgive, nasan ban miki halacci ba, naci amanan ki, naci amanan ABOTA(litaffin Aisha M Mu'azzam), ban cancanci yafiya daga gareki ba amma ki yafemin min", kuka take sosai har da majina, duk abunda tace *ZYNAH* taji amma ba bakin magana sema kara sake jikinta da tayi saboda ta wahala, KB kuwa bayama cikin hayyacin shi bare yasan wainar da ake toyawa.


    SMART ne ya fito ze gudu yaji ance mishi "u ar under arrest, drop ur phones,drop ur wallet, don't move nd anytin u say will b use against u in d court of law", ai tuni cikinshi ya duri ruwa, ya ajiye duk abunda akace ya ajiye ya daga hannunshi sama sannan suka tasa keyanshi yamusu jagora zuwa cikin gidan aka kama su GIANT, Humaira jin alamun an shigo dakin da suke yasa ta kara sautin kukan ta Fahad yace " kukan me kikeyi", jin muryanshi yasa tayi saurin dagowa taga Uncle da Fahad tsaye a kansu tuni taji wani kunya  nan take taji ina ma kasa ze tsage tashiga ciki, KB ne ya dago idonshi da sukayi  jajur  yace "kukuma fa", Uncle da haushinshi ya gama kamashi besan sanda yakai mishi wani wawan naushi a hanci ba, nan hancinshi ya fashe Uncle yace " kasani in zakayi iskancin ka bada *ZYNAH*, ke kuma kin ban kunya, Allah ya wadar wannan halin naki", sunkuyar da kanta tayi tana kuka Fahad kuwa kallonta yake, kallon so ne, kallon tsana ne, kallon tuhuma ne, shi kadai yasan irin kallon da yake mata. DPO ne ya shigo yace Humaira da KB su tashi ba musu Humaira ta tashi tana kuka KB kuma ya tsaya yana musu gardama har da cewa "kun san kowaye mahaifina, wlh indan mahaifina ya sani seyasa kun cire wannan uniform din da kuke takama dashi", kasan bindiga DPO yasa ya makeshi sannan yayi shiru, DPO yace " koma waye ubanka muna jiranshi, nw move", dole KB ya fita Humaira tabi bayanshi DPO ya tasa keyansu, da gudu su Uncle suka karasa wurin *ZYNAH*, wacce ta dawo kaman wata matacciya saboda wahala amma kuma idonta biyu duk abunda akeyi tana jinsu, daukanta uncle yayi ya fita Fahad ya biyo bayanshi suka sata mota, KB ganin DPO nama su Uncle magana sauran en sandan kuma na wurinsu SMART yasa shi neman hanyar guduwa amma ina ya makaro, tuni DPO ya hangoshi nan ya harbeshi amma Allah ya taimake shi bullet be sameshi ba sedai yayi scratching dinshi a kafada, ihu yayi ya rike hannushi DPO ya tasa keyanshi suka sashi mota hannun na jini.


     Direct  station aka wuce dasu KB akayi detaining dinsu saboda dare ya riga yayi ba daman yimusu tambayoyi a lokacin, inda Humaira akace ta zauna a canter din en sanda saboda ita macece, tashin hankalin da nadaman da bata tabayi ba yau tayi shi, *ZYNAH* kuma direct hospital aka wuce da ita, suna zuwa a karbe su aka shiga da ita ER inda Uncle ya kirasu Daddy ya shaida musu duka abinda ya faru, sun so fitowa amma Uncle yace suyi zaman su saboda dare yayi subari in anyi sallan asuba se su fito, sosai mamaki ya kamasu  jin Humaira nada hannu a cikin abunda ya faru, nan dai sukayi godiya ga Allahnsu daya tona asirinsu tun abu be lalace ba. *ASHRAF*  tunda aka kwantar dashi yafara mafalki cikin dan baccin da yayi na wannan yarinyar daya saba mafarki da ita, wannan karon ma yanda yasaba haka tazo mai wato bayanta ya gani, amma fortunately for him daya ganta seya soma binta yana kiranta saboda ta tsaya amma taki tsayawa sema kara sauri da takeyi, garin sauri ta buge da dutse ashe katon rami ne a gabanta bata sani ba, bigewan da tayi seta fada cikin ramin shikuma cikin hanzari ya kamo hannunta se a nan yaga fuskanta *ZYNAH* sak, murmushi ya mata yace "don't worry u ar safe nw", itama murmushin tayi sannan yaci gaba da jawota amma seda yakusa fito da ita tsantsi yasa tasaki hannunshi ta fada cikin ramin, shikuma a razane ya kwala mata kira *ZYNAHHHHH!!!!!*  wanda yayi da tashin shi daga barci, wani irin gumi yakeyi ya kalli dakin da yake yaga a asibiti yake ya kalli hannunshi yaga drip a hankali yace *ZYNAH* se a lokacin ya tuna cewar *ZYNAH* fa ta bata, ai nan take ya cizge drip din da ta hannunshi ya fito a daddafe saboda jiri su Fahad ne suka ganshi da sauri suka karasa suka kamoshi amma ba abunda yake fada se *ZYNAH*, doctor suka kira wani doctor ne yazo yana zuwa ya banka mishi allura tuni yayi shiru ya koma barci suka maida shi daki aka sa mishi sabon drip.


     _kuyi hakuri da wannan nasan yayi kadan, banjin dadi ne, shiyasa tun safe kuka jini shiru, wannan ma saboda masu kirana nayi typing, esha manage😰_

     _TEAM ASHRAF# ZYNAH✌_

     _Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now