Chapter 7

1.3K 83 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

*ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*Thousand tnx to my beloved fans for giving me support, ILYSM❤*

QUOTE:- "Bridge between souls, stands on pillars of trust! It reflects united self and creates a path to reach each other's hearts".

_I dedicate dis page to my frnd nd loved ones._

0⃣7⃣

Shirye shiryen tafiyanta takeyi sai faman zuba kaya a trolley takeyi kaman wadda zatayi tafiyan wata daya. Ta gama zuba duk abunda tasan zata bukata sannan ta rufe trolley din ta ajiye gefe sannan ta shiga wanka , wanka tayi ta wanke kanta sannan ta fito daure da towel a kirjinta da koma wani karami tana goge jikinta , gaban dressing mirror ta zauna tayi drying kanta tareda shafa masa mai me dadin kamshi ta kama sannan ta shafa mai a jikinta da powder 'jordan' da lipstick sannan ta tashi ta nufi wardrobe dinta. Wani English gown ta dauko mara hannu army green in colour tasa sannan ta Dora white boyfrnd jacket a kai da white veil da takalmi me dan tsini amma ba sosai ba tasa sannan ta dauko army green chained bag ta zuba kudi da atm dinta da sauran tarkacen sweet( wanda bata rabuwa da su dukda an hanata sha) ta rataya bag din a kafada, kallon kanta tayi a mirror tayi murmushi saboda tasan tayi kyau sannan ta dauko phone dinta kirar Samsung S6 edge ta fito sai zuba kamshi takeyi.

Kasa ta sauko taga Momsie zaune kan three sitter Islam na kwance kan kafanta suna kallon film din Barbie _PRINCESS CHARM SCHOOL_ wanda Islam ce tace dole shi za'a kalla. Momsie na ganin ta tace"har kingama?" tace"eh Momsie nagama,zan wuce saboda Humaira na jira na tare zamu","ok sai kun dawo kuma dan Allah a duba titi da kyau banda rough driving kinji","In Sha Allah Momsie sai na dawo","a dawo lfy". Har ta kai bakin kofa ta jiyo muryar Islam tana cewa"kisiyo min chocolate cookies kinji" juyowa tayi tareda cewa"kedai kenan , kullum chocolate cookies baya isarki","Sista please now"ta fada tareda marairai cewa "toh naji zan siyo"sanan ta fita .

Wurin motanta ta nufa tayi warming motan saboda tayi kwana biyu bata fita dashiba sannan ta fito mai gadi ya bude mata gate ta fita sai gidansu Humaira. Horn tayi aka bude mata gate tashiga ta samu wuri tayi parking, Da sallama tashiga parlourn kannen Humaira suka amsa mata tareda rungumeta suna mata oyoyo tace "my twins kwana biyu ya kuke"suka amsa mata da "lfy lau muke", sannan Hassan yace "Yaya *ZYNAH* kinyi kyau sosai","thank you" in a Bestee dina take?","tana dakinta"inji Hussaini , "Mommy fa","ta fita tunda safe","ok toh, ina zuwa " sannan tayi hanyar dakin Humaira, tana shiga Humaira na fitowa nan sukai karo "awchh" kowaccen su tace sannan sukai dariya suka fito Humaira tace"wat a coincidence" *ZYNAH* tace"yeah".

Suna zuwa parlour suka tarar har yanzu en biyu wasan su sukeyi , Humaira ce takira mai aikinsu tace "Dan Allah ki kula da en biyu zan fita na dawo","toh ba matsala sai kun dawo" sannan sukama en biyu sallama tareda alkawarin kawo musu sweet sannan suka fita. Motan *ZYNAH* suka shiga suka wuce , Humaira tace "Swthrt can i ask u a question ?" ,"go on am all ears"sai da ta gyara zama ta fuskanci *ZYNAH* da kyau sannan tace "wai me zakije kisiya a mall bacin kinada komai koma ba a wannan tafiyan zaki fara lectures ba ballantana kice provisions zaki siya". Dariya tayi sosai sannan tace "amma Bestee kin ban kunya , sai kace baki san ni ba , ni da bana rabuwa da kayan zaki , su zanje na siyo ,saboda banason naje garin basuda wanda nikeso , shiyasa nakeson na siya wat ever it is dat i will need". kallon mamaki Humaira kemata sannan tace " Allah ya yaye miki wannan jaraban na shan kayan zaki , dan ni tunda uwata ta kawo ni duniya ban taba ganin sweet addict irinki ba , gashi koma ko wani month in zakiyi menses kaman ki mutu amma wannan bai hanaki ki rage sha ba". Murmushi tayi batare da tace mata komai ba taci gaba da tukin ta amma cikin zuciyanta ta yarda da maganan Bestee dinta 100%.

Sun kai mall din tayi parking suka fito suka shiga ciki , *ZYNAH* sai kwasan kayan zaki takeyi, ba abunda bata dauka ba acewar ta ai sati daya zatayi saboda haka kayan sati daya take diba, ita dai Humaira tayi magana har ta gaji ta zuba mata na mujiya amma cikin zuciyarta mamakin yanda *ZYNAH* bata tsoron kayan zaki takeyi duk da ko wani wata sai anyi admitting dinta a hospital saboda ciwon mara.

Sun gama siyan abunda zasu siya suka biya kudi suka fito suka shiga mota sai gidansu Humaira , ta ajiye Humaira gida tareda mika mata kayan da tasiyo wa twins, itama ta kwasa kayanta tareda mata alkawarin In Sha Allah zatazo gobe tayi rakiya zuwa airport itama sannan sukayi sallama ta shiga gida sannan *ZYNAH* ta dau hanyar gida itama.

Sallama tayi tareda tura kofan parlourn , wani wawan ajiyan zuciya tayi ganin ba kowa parlourn saboda tasan in Momsie taga abunda tasiyo to kashin ta ya bushe dan sai ta kwace . Da sauri ta nufi dakinta ta ajiye kayan tareda rage kayan jikinta ta shiga bathroom tayi wanka tayi alwallah tazo tayi sallahn la'asar tayi addu'ointa sannan ta koma kan bed dinta ta dauko wayanta tafara duba social media dinta su IG,snapchat,twitter da sauransu.

Sallaman Islam ce ta kaseta, dagowa tayi tareda amsa sallaman sannan tace "Islam dama kina gida? naga banji motsinki ba ","ina nan bacci nake yanzu na tashi","ok, na siyo miki cookies dinki" cikin tsananin jindadi tace "yana ina","dauko nylon din can" tafada tareda nuna mata ledar da zata dauko. Dauko wa tayi tazo ta zauna tareda bude ledan, dadi taji ganin chocolate cookies har biyar da maltose , bounty da sauransu kuma wai duk nata ne , godiya tayi sannan ta ajiye gefe ta kalli ýarta tace "sista gobe Sunday zaki tafi ki barni all by myself wen am already used to being around u" tafada a marairaice kwalla na neman taruwa a idonta. Itama *ZYNAH* kasa tayi da idonta sannan tace "Islam i am nt going for gud, sati daya kawai zanyi na dawo nd i promise u kullum zan dinga kiranki muna video call so u won't miss me dat much kinji Lil sis" kada kai tayi tareda rungumeta tace "promise me u will take care of urself" kara rungumeta *ZYNAH* tayi sosai a jikinta sannan tace "I promise".

_keep following so u won't miss_

_Mzz Daddy💋_

ZYNAHWhere stories live. Discover now