Chapter 2

1.6K 101 12
                                    

FLASH BACK

Abdul-kareem lawwan shine sunanshi yanada shekara 28 mahaifansu suka rasu dukka dan haka rikon kaninshi (Ibrahim) seya dawo hannunshi wanda keda shekaru 24 dayake su biyu ne a gun iyayensu. Kuma Allah ya taimakesu iyayen nasu sun bar masu gado sosai dan haka har suka gama karatunsu suka fara aiki dukkansu basu sama wata damuwa ba. Asalinsu fulani ne gaba da baya

Abdul-kareem ya hadu da matanshi Hadiza dalhat a wani tafiya da sukayi ta fannin aiki NBTE buzuwa ce a Oxford tayi masters nata right now she's a writer, ita tun tana karama mahaifiyarta ta rasu tou babanta ne yayi raising nata.

Shekaransu biyu da haduwa sukayi aure a shekaran babanta ya rasu shima tayi kuka kaman tayi hauka.
Ibrahim shima dake aiki a NNPC ya hadu da Bilkisu ya aureta basu dade ba suka haifa yarsu Hawwatyy kyakkyawa yarinyan ga idanuwa tabarkalla

Bayan shekara biyu da haihuwan Hawwatyy. Hadiza itama ta sunbulo yarta wanda aka saka mata KHAMEELARH (kamilan mata) amma kwata-kwata bata dauko halin masu sunan ba.

--Khameelarh--

Yarinya ce fara tass jikinta wane idan kuda yahau za'aga tabo.
You guyx should imagine ace uba bafulatani uwa kuma buzuwa kawai ku hango inda yarsu zata kasance.
Ga gashi kuma gata shiririya ga tsayi amma duk shirantan ta Allah ya bata shape tabarkalla and ahe have this sexy eyes they are huge and this pink lips.
She's now 17 in 7months time zata shiga 18. And tun tana 14 ta fara drawing takalma harta kware se Ummu ta goya mata baya yanxin haka tanada store dinta Meleelarh's Kollection wanda takalma ne kawai baja-baja a ciki wand ita da kanta tayi designing nasu kuma ba karamin ciniki ake ba and is not a normal store shi babu me zama a ciki cus online shopping ne. Sede kudin a bank Ummu tace a ringa saka mata amma ita Khameelarh har yanxi bata yanke me zatayi da kudin ba wanda yanxin sun haura millions(what i aiint lying,well probably)
A yanxin haka tana SS3art first term ake amma school na uku kenan take ciki duk sauran expelling nata akeyi daman can home schooling nata ake se da zata shiga SS3 Ummu tace a sata a school kawai gashi tanata sawa anata expelling nata

Yanxin haka tana cikin Symarh Acedamy one of the best schools a Abuja. Well second best cus Lawiza Acedamy is the best it belong to the president sunanshi da sunan matanshi ya hada ya zama Lawiza be saka Khameelarh ana bane dan tunda tasan na babanta be iskanci ze karo

She's the captain of cheerleading and she is the popular one among all the student of the school kowa so yake ya zama friend nata amma ko fuska bata ba kowa idan kaga tana magana da student tou suna practise ne amma bayan nan bata shiga harkan kowa duk wanda yazo mata magana ma gwaleshi take

Kuma duk rashin ginta tanada kokari ba laifi. Shiyasa duk laifin da zatayi be cika batama iyayenta rai ba sosai dan sunsan kanta naja.
***

Babu wata shakuwa sosai tsakanin Khameelarh da Hawwatyy dan kowa yanaji da nashi kaudin tunda duk sunsan sunada kyau ga kuma iyayensu sunada kudi tou kowa naji da kanshi
Amma Khameelarh tana zuwa gun Uncle nata su sha hira amma bata cika shiri da Bilkisu(Matanshi kenan) ba
Khameelarh was 12 Abbu ta ya fara neman president kuma cikin ikon Allah ya samu so za'ace rabin girmanta suna cikin politics kenan amma ita kwata-kwata bataso though she enjoy begin popular dan an bata Nigerian's sweethrt tun sanda Abbunta yahau amma kuma anata kawo mashi hari dan yanxin shekaranshi na biyar kenan akan mulki ya gama shekara hudunshi harya sauka amma seya sake fitowa election shida Vice president Abubakar Muhammad suka ci dan a gaskiya kasan ana sansu bama kasan kadai ba hadda ketare
Dan Ex-president Mu'azzam Auwal ba karamin ta'addanci yayi ba a kasan sanda yake mulki ya cinye kudin kasan shida matanshi sannan ba'a nan aka tsaya ba ga boma-bomai dake tashi kulluma a kasan
Shine Allah ya kawo ma kasan dauki gashi yanxin ko ina an gyara, kasa ya zama kaman turai ga kwanciyan hankali ga kuma kudin kasa daya dawo shiyasa daya sake dawowa aka sake zabanshi

The Presidential Throne!Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang