20- Hatred

667 62 15
                                    


Kunci, bakin ciki, fargaba da bacin rai su ne cunkushe a zuciyar Mahboobah Bukar tun da aka daura musu aure watanni hudu da suka gabata. Tsakaninta da Ishraq ta yi mishi girki ya kwasa, saboda Mahboobah gwana ce a girki, yayin da Ishraq kuma ya kasance gwani a bai wa ciki hakkinshi. Da sassafe yake fita, ba ta ma ganin shi. Kuma ba zai dawo ba har sai sadda ta yi bacci. Iyaka ya je dining table ya zuba abinci ya ci. Kwanonin ma a nan zai bar su har safe ta sake kwashewa. Idan wani cefane ko nama ya siyo zai ajje mata a fridge, washe gari ta gyara ta mayar a fridge din. Cika irin wadda amare ke yi sam babu ita ga Mahboobah. Ta rame sai zallar kashi, kamar wacce ta shekara rabon da ta ci abinci.

Hawayen fuskarta ta share. Yau sati biyu ke nan rabon da ta sanya shi a idanuwanta tun ranar da suka yi zuwan karshe gidan Mami.

Ta tashi da matsanancin zazzabi mai zafi hade da ciwon kai, ga shi ko kwayar pain reliever ba ta da ita hakan ya sa zazzabin ya kwantar da ita sosai ko sallah da kyar ta iya tashi ta yi a zaune. So take ta tashi ta girka mishi abinci kamar yanda ya umurce ta da ba ya son fashin girki. Sai dai ba za ta iya bah. Ba ta da karfin ko mikewa a saman kafafuwanta balle na shiga kitchen ta girka abinci. Sai dai kuma me, tana tsananin tsoron tashin hankalin da zai iya doso ta a lokacin da Ishraq ya zo bai samu abinci ba.

Yunkurin mikewa ta yi amma jiri ya mayar da ita. Jikinta tauna yake yi sosai ruwan hawaye sai kwarara yake yi mai tsananin gumi. A haka ta samu wahaltaccen bacci ya dauke ta.

*
Kamar yadda ya saba koyaushe, ya paka motarshi ya bude kofa ya shigo. Yunwa yake ji sosai don shi a ka'idarshi ba ya cin abincin waje, sai dolen doliya. Da farko ya tsiri komawa wurin Maminsa ya ci, zuwan shi biyu ta taka mishi burki. Ta ce ya koma ya rinka cin na matarshi tun da dai ba ta da naqasu wurin iya girki. Ta kawo mata ta ci ta ji ta iya ba sau daya ba ba sau biyu ba. Wannan dalilin ne ya sa ya tilasta wa Mahboobah yi mishi girki.

Briefcase dinshi ya kai daki, ko kayan jikinshi bai rage ba ya fito parlor tare da zarcewa dining area. Wayam ya gani in banda canister set da ke girke a tsakiyar table din na su sugar da sauran kayan tea. Da mamaki ya kariso isowa, da gaske babu komai a kai. Ya nufi kitchen a tunaninshi ko ta yi ne ta manta ba ta kawo mishi ba. A can din ma babu. Ya tsaya tunanin matakin da zai daukar mata, yana hasko yanda zai shaki wuyanta ta fada mishi me ta taka da yau ba ta mishi girki ba duk yunwar da ya kwaso?

A cikin wahaltaccen baccin da take yi ta jiyo hargaginshi. Bai cika daga murya ba ko masifarshi zai mata cikin sassauta murya yake yi. Sai dai wannan ya sha bamban. Daga muryarshi yake yana fadin "Ke! KK! Baccin uban me kike? Waye ya ba ki damar yin bacci ba tare da kin girka mun abinci ba? Ko kuwa kayan miyar da aka saba kawowa daga gidanku ne suka kare? Ehh, daga gidanku mana. Don in da ni na siyo na kawo ai ba za ki qi yi mun girki ba."

Yanda zazzabi ya ci jikinta ba ta jin ko magana za ta iya yi mishi. Ta dago fuskarta ta kalle shi, idanuwanta sun kada sun yi jajur saboda azabar ciwo da ta kuka.

"Ki tashi KK! Ki tashi ki dora mun abinci ko kuma in fitar da ke daga gidan nan ki kwana a kofar gida shi ne hukuncinki! Idan kika bari na sake magana sai dai ki ji saukar yatsu a fuskarki."

A cikin dukkan tashin hankalin da ya mamaye Mahboobah, ta rasa wane ne ya fi dan uwanshi ciwo. Zafin ciwon da yake addabarta? Ko kuwa zafin bakaken maganganun da suke fita a tsakanin labban Ishraq Sulaiman? Kanta a kasa, zuciyarta na dokawa da dukkan karfinta a kowacce gaba ta jikinta. Muryarta a raunane, ta dago ta kalle shi a karo na biyu,

"Ba zan iya ba Likita." Ta share sabon hawayen da ya fito mata.

"Yanzu ke har kanki ya yi kwarin da za ki kalle ni cikin ido ki fada mun wai ba za ki iya ba? Tukunna ma, wai waye ya ba ki damar kwanciya ba tare da kin gama aiwatar da aikinki ba? Kitchen dinki kanshi ba ki gyara shi ba. Daki babu inda kika share amma kin zo kina bacci. Wa ya ba ki wannan damar KK?"

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now