30- Bilkisu Imran

544 56 9
                                    

Kamar yadda Mahboobah ta yi kwanan kunci, haka Ishraq ma ya yi shi. Kai tsaye ma ba zai ce ga dalilin kuncin nashi ba. Sai dai idan ya yi wani nazarin, yana ganin kamar yardar da ya yi da Mahboobah ta ci amanarshi ne silar shigar shi damuwa.

Ya yi juyi mara adadi kafin ya mike ya hau sintiri daga bangon toilet zuwa bangon da gado yake. Ya kasa zama, kamar yadda barci ya yi kaura daga idanuwanshi.

Ya fi karfin minti talatin yana sintiri, kafin ya zauna, yana manna tafukan hannunsa da kumatunshi. "Allah Ya isa tsakanina da kai..." ya fada a bayyane, yana kuma son gyara maganar tashi 'Da ke' ya kamata ya ce a ganin shi, saboda ita ce ta ci amanar tashi ai. Da a ce ba ta ba gardin dama ba, da komai bai faru ba.

"Ai shi ne katon dan iskan, mai bin matan mutane."

Bayyanannen tsaki ya saki. Miye kuma nashi a ciki. Me ya sa zai damu don wani kato ya so karfen kafa da ba kaunarta yake yi ba dama can. "To ai kuma matata ce." Ya sake fadi yana kwanciya hade da yin ruf da ciki.

Kamar wasa ya fara jiyo assalatu. Ashe har lokaci ya kai haka. Mikewa ya yi ya shiga toilet, alwalla ya dauro ya yi nafila sannan ya yi karatun Al'Qur'ani da ya mance yaushe rabon da ya yi shi idan ba a cikin sallah ba. Sai da ya ji kira sannan ya tashi ya nufi masallaci.

Washe gari bai samu zuwa asibiti ba saboda kanshi da yake jin yana sara mishi. Gidan Mami ma yake son zuwa amma ba ya jin zai iya yin tuki. Babur ya tsayar ya kwatanta mishi gidan Mamin tashi.

Yana zuwa ya same ta a falo zaune da wani mutumi da ya ba shi baya keyarshi kawai yake iya gani. Duk da ya so ya shaida ko wanene amma a hakan ya tako ya shigo cikin dakin. Sallama ya yi, yana kallon Khaleed Zannah da ke sanye da farar shadda da light brown din hula. Kamar ba shi ba. Rabon da ya saka shi a ido an fi wata hudu. Ganin shi da Khaleed din ya yi ya sa ya mika mishi hannu suka gaisa. Duk da bai yi niyyar tafiya ba a daidai lokacin amma ba ya jin zai iya ci gaba da zama saboda zuwan Ishraq.

"Mami ni zan koma in shaa Allah. Sai kuma wani lokacin idan na zagayo."

"Na gode sosai Khaleed , Allah Ya yi maka albarka. Ka gaida iyalin. A ce da Junior tunda dai ba ya kawo toshi tabbas zan canja sheka. Wani mijin zan nemo."

Dariya Khaleed ya yi, zai fita ke nan ya ji muryar Ishraq yana kiran sunanshi.

"Ka dawo mu yi magana."

Ba tare da ya juyo ba kawai ya gyada kanshi yana fita daga kofar. Da saurin Ishraq ya sha gabanshi. Da tsiya ya janyo shi ya dirar a tsakiyar falon da ke shimfide da babban carpet.

"Lafiya kake likita? Ya kake jan shi haka kamar wani karamin yaro?"

"Ba lafiya ba Mami. Matar da duk ku biyun nan kuke fushi da ni ta silarta nake son tabbatar muku da mummunan halinta gara ko'inkular da nake yi da ita. Mami..." ya fada yana jin kanshi na tsananta sara mishi. "Mami ashe mazinaciya na aura..."

"Ya ishe ka haka Ishraq! Ahir dinka da kulla wa diyar mutane sharri. Wato kiyayyar har ta kai ga dora mata mummunan kazafi haka ko? Kar in kara jin magana ko mai kama da wannan."

Idonshi ya matse, yana jin kamar kar ya gwada musu videon, kamar gwadawar wata fallasa ce ga Mahboobah. Sai kuma ya tuna, akwai abu mafi muni sama da matar aure ta rinka bin maza a waje? Ya bude security din wayarshi. Videos ya shiga, ya kunna, yana saita wayar ga Mami da Khaleed da har yanzu ya kasa cewa komai.

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now