19- First night

692 64 4
                                    


A cikin mayafin lapayarta ta dukar da kanta. Misalin karfe takwas da rabi ke nan na dare, Haneefa da Saleemah suka taimaka mata ta shirya cikin riga da zani na atampa purple, sannan ta nada lapaya fara mai digo-digon purple. Ta yi matukar kyau sai wani irin ni'imtaccen kamshi ke fita daga jikinta.

"Taba kirjina ki ji bugun zuciyata Sally. Am afraid...wallahi ina jin tsoro." Ta fada jikin Saleemah hade da fashewa da kuka, cike take da rauni. Tsoro da fargaba sun taru sun cunkushe a duniyarta. Yanayin da take cikinsa, ita kanta ba ta san a wane mizani za ta ajje shi ba. Ba ta san a wane hali take ciki ba. Na farin cikin mallakar burin zuciyarta? Ko kuwa na bakin cikin kurkukun da ta kawo kanta da kanta? Fargaba take, tana kara hasko yanda duniya za ta murde mata, ta juye mata tamkar yanda ake juya waina. Duk farin cikinta take ji yana dunkulewa a wuri guda, yana neman barin zuciya da ruhinta, yana rikida izuwa kunci da bakin ciki.

"Haba MB! Muradin zuciyarki ne fa kika aura. Kukan na mene ne to? Yanzu lokacin farin cikinki ne. Sam kuka bai cancanci amaryar da ta auri burin zuciyarta ba."

Jin maganganun Saleemah take tamkar tana qara rura darma, wuta na fartsatsi a tsakanin kirjinta. Kirjin nata ya mata nauyi, ya za ta yi da shi? Ya za ta yi ta sauke wannan nauyin da take ji tun daga gefen haggu har zuwa gefen dama na zuciyarta?

"An miki kwalliya amma kukan farin ciki ya sa kina neman bata ta ko?" Haneefa ta fada a daidai shigowar ta dakin, ta gama turara turaren wuta a duk gidan.

"Hanee kin san fa abun is not easy. Rabuwa da gida ba wasa ba ne. Fadawa sabuwar rayuwar kanshi abun kuka ne. Idan ba za ki iya rarrasarta ba ki mana shiru ni zan iya."

Tabe baki Haneefa ta yi bayan ta ajje burner ta hau gyaggyara kan dressing mirror. "To Allah ya bada ikon rarrashi kin ji. MB zan kawo bucket a cika mun shi da hawaye kafin wayewar gari."

Duk da cikin kuncin da take hakan bai hana ta yin dariya ta kai ma Haneefa dukan wasa ba. Haka suka hau gyaran gidan har ya zam tas, sai kamshi yake bad'ad'awa.

Karfe tara suka ce za su tafi. Cikin kuka ta jawo hab'ar rigar Saleemah "Me ya sa za ku tafi ku bar ni ni kadai?"

"Saboda ba za mu iya zaman jiran dawowar mijinki ba. Waye ya san sai yaushe zai zo? Gwara mu koma gida mu adana tsufanmu. Akwai gajiya ke ma kin sani." Haneefa ta fada cike da tausayin yanda kawarta ke kuka bilhakki.

"Ki yi hakuri Boobah. Dare ke yi ga shi gidajenmu ba kusa ba. Na tabbata ba da jimawa ba angon zai zo..." kafin Saleemah ta rufe baki ta jiyo sallamar su Khaleed. "Yauwa Alhamdulillah! Kin ga ga 'yan halak din nan ma. Hanee mu wuce ko?"

Kuka sosai Mahboobah ke yi, tana kallon su suka fita, ta qara qarfin kukan nata tamkar karamar yarinya.

Fitar su parlor sukaci karo da Khaleed zaune Ishraq a tsaye suna magana.

"Kawayen amarya ya na ga har kun fito tun ba a sa ango daki ba?"

Kallon junansu suka yi, kafin Haneefa ta dan murmusa. "Dare ke yi ne abokin ango. Ga mu duk mata ban san wa zai taimaki wani ba idan muka hadu da abun tsoro a hanya. Gwara ma ni a kan wanna farar kurar." Ta kalli Saleemah tana dariya.

Dariya Khaleed ya yi sosai har da dafe ciki. "Kin gan ki da tsokana. To yanzu dai jira za ku yi mu fita tare. Duk da na ga da motarku a waje sai in zama dan jagora ina gaba kuna biye da ni."

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now