08- Depression

618 66 2
                                    


A kan carpet din dakinta take zaune, ta hada kai da guiwa fuskart zuru-zuru. Gashin kanta duk ya barbazu a saman fuskarta babu gyara ko kadan. Rabon da ta gyara kanta tun bayan sallamarta daga asibiti, an fi wata daya ke nan. Lebonta a bushe duk ya farfashe ya tsage ta ko'ina. Idanuwanta sun zurma sosai, ga rashin kwalli sai abun ya kara lalace mata. Sannan k'ashi duk ya bayyana a wuyanta. Yatsun hannu da k'afarta duk akaifa ta yi zaqam-zaqam. Baki dayanta ta koma tamkar ba ita ba, gwara ma wata mahaukaciyar da ita, ko ba komai ita an san da ma can hauka take. Ita kuwa wannan da hankalinta, sai dai ta zauce, kallo guda za a ga bayyanuwar damuwa a saman fuskarta.

A inda take jona chaji ta nufa, wayarta na jone jikin chajin ta zaro ta koma asalin inda take zaune, gallery ta shiga, hoton Ishraq da ya zame mata abincin cinta ta hau kallo, murmushi hade da hawaye suna bayyana a saman fuskarta. Sai dai idan hawayen ya diga a saman fuskar wayarta, saman hoton Ishraq da take kallo, ta sa harshenta ta lashe, ta sake ci gaba da kallon shi.

Haka take yi tun daga ranar da ta daukar wa kanta, Ishraq da kuma Fareedah alkawarin fita daga rayuwar Ishraq har abada.
Ba ta cin abinci sai dai kayan marmari da take fita kullum ta dauko a fridge dinsu. Sai ruwan shayi mai lipton wani lokaci. Momy ta yi bakin kokarinta har ta gaji ta zira mata ido. Fareedah kuwa da ma tun ranan da ta yi mata maganar karshe na cewa sai sun gwammaci gwara lokacin da take son Ishraq a kan yanzu, ba ta sake nufarta da zancen ba, ko tayin abinci ba ta mata, haka Yah Aliyu ma.

"Assalamu alaikum." Haneefa ta yi sallama, hade da shigowa cikin parlorn.

"Wa alaikumussalam. Haneefa ne da Saleemah. Sannunku da zuwa. Ku iso." Momy ta fada hade da gwada musu wurin zama.

"Yauwa Momy. Ina wuni?"

"Lafiya lau fa. Ya su Mamanku?"

"Lafiya wai a gaishe ku."

"Ina amsawa sosai. Ina ta tunanin ganin ku ai shiru, na ce hala ko kawar taku ce tai muku wani abu."

Saleemah ta yi karfin halin murmushi. "A'a Momy. Muna ta shirin fara jarabawa ne so ba zama sosai. A makaranta muke wuni karatu sai yamma muke dawowa gida."

"Allah sarki! To Allah ya bada nasara ya sa a samu sakamako mai kyau. Ita dai waccan an bar ta a baya." Ta furta hade da share guntuwar kwallar da ta fito mata.

"Abin da ma ya kawo mu ke nan Mommy, mu ji ko ba za ta iya zana jarabawar ba tun wuri a sanar da Level Coordinator dinmu, sai a san yanda za a yi ko deferring semester (jingine semester) din ne sai ta yi."

Mommy ta gyada kai tana kallon Haneefa da ta yi maganar. "Ina fa Mahboobah za ta iya zana wata jarabawa a yanzu Haneefa? Ku shiga dakinta dai ku gan ta. Ni ba ni ma da tabbacin Mahboobah na da cikakken hankali fa. Kamar kwakwalwarta ta tabu."

Cike da mamaki Haneefa da Saleemah suka zaro ido. "Tabuwa dai Mommy?"

"Toh, tabuwa mana Saleemah. Ko magana fa ba ta yi. Ba ta gyaran jikinta. Ba ta fitowa cikin mutane. Ba ta cin abinci sai kayan marmari. Sai haukar kuka da dariya. Ko dazu na leka dakinta har na gama tsayuwata na fito ba ta san da wanzuwata ba a dakin, idonta na kan waya tana kallon hoton Ishraq tana hawaye tana dariya. Toh ina hankali yake a nan?"

"Innalillahi! Ashe abun har ya kai haka Mommy. Ya salaam!"

Da kuka su duka biyun suka doshi dakinta. Sun same ta bacci ya dauke ta a kasan carpet din. Ga wayarta a gefe guda, gashi duk ya rufe mata fuska, hawaye ya bushe a saman fuskarta. Duk ma ba wannan ne ya fi rikita su ba, ramar da ta yi ce babban abun ji. Rama ta jiki da ta fuska, kamar ba ita ba.

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now