03- where it all began

1K 108 22
                                    


"Yah Boobah ki fito mu ci abinci an gama ke kadai muke jira."

Ba ta ko dago kanta ta kalle ta ba ta zaro guntuwar magana daga qasan makoshinta, "Na koshi."

"Kin koshi?" Fareeda ta tambaye ta cikin mamaki.

"Kin ji me na fada Reeda, me ya sa da tsiya kike so in maimaita?" Fuskarta da ta wadatu da ruwan hawaye ta dago tana sauke kallon ta a gefenta.

Ajiyar zuciya Fareeda ta sauke hade da isowa bakin gadon ta zauna. Ta kama hannun Mahbooba cike da tausayi ta ce, "Yah Boobah wai me ya yi zafi ne shi ba wuta ba? Wannan wace irin rayuwa ce kike neman jefa kanki a ciki? Yaya idan ke kin gaji da rayuwarki mu ba mu gaji da ke ba. Ba mu gaji da ganin ki ba. Don Allah kar ki kashe mana kanki. Ki cire son zuciya mu ma ki faranta mana. Ki yi kokarin rungumar kaddarar da mai kowa mai komai ya jefo a saitin duniyarki."

Kukan da ya zame mata abinci ta kara fasawa, "Rayuwata ba ta da amfani Reeda. Ban so ba, ban so na kasance wata abar da za ta jawo muku abun kunya ba. Yes, abun kunya. Bibiyar Ishraq da nake kadai wani katoton abun kunya nake jawo ma ahalin gidan nan. Sai dai ina so ku sani, ba da son zuciyata ba ne. Ni ma kaina na so na daina, tun farko ma na so kar na zurfafa, sai dai kuma abun ya ci tura. Duk bayan daqiqa sai kaunar Ishraq ta qara girmama a kaf ilahirin zuciyata. Ko kadan daraja da soyayyarshi sun kasa raguwa, wulakanta nin da yake ya kasa yin tasiri. Kaunarshi nake da dukkan zuciyata Reeda. Da dukkan jinin da yake gudanya a halittar tsokar zuciyata." Ta fada jikin Reeda tana kuka sosai.

"Wannan jarabta ce Yaya. Ban taba ganin soyayya irin wannan ba. Yaya don Allah ki saukaka ma kanki. Ki tuna duka ba ki fi sati uku ba da sallama daga asibiti. Ki tuna larurin da ya addabe ki tun kafin a haife ni that's tun kina yar karama. Sai yanzu da muke ganin ciwon ya warke sai ke kuma kike neman kiran shi da kanki? Kike neman siyanshi da kudin da Allah ya mallaka miki? Na sani ba ke kika dora ma kanki ba. Amma kuma ki sani Allah madaukakin sarki da kanshi Ya ce ba a kallafa wa bawa sai abinda zai iya dauka. Ba don mu ba, ko don Momy, halin da take shiga a duk sadda jikinki ya taso, wannan kadai ya ishe ki. Ki kokarta tumbuke wancan malalacin likitan daga zuciyarki, ko ba kya so, tun kafin abun ya yi tsananin da tumbukewar za ta yi wahala."

Da shesshekar kuka ta ce, "Ki je ki ci abinci Reeda, ba na jin yunwa."

Ganin tana kokarin canza topic din da suke a kai ya sa Reeda daukan wayar Mahbooba

Oops! Ang larawang ito ay hindi sumusunod sa aming mga alituntunin sa nilalaman. Upang magpatuloy sa pag-publish, subukan itong alisin o mag-upload ng bago.

Ganin tana kokarin canza topic din da suke a kai ya sa Reeda daukan wayar Mahbooba. Ta ci sa'a datanta na bude, whatsapp ta shiga ta lalubo group chat dinsu ita da Haneefa da Saleema, group video call ta latsa kuma duk suna online. Bayan duk sun dauka ta juya back camera suna kallon yanda Mahbooba ke kuka sosai kamar ranta zai fita. Suna kallon yanda hawaye ya wanke fuskarta wanda mutum zai iya rantsewa da Allah ruwan alwalla ne bai bushe daga fuskar ba. Sai dai yanayin shesshekar da take fitarwa ne zai ankarar da mutum cewa kuka ne take yi da iya karfinta. Hankalinsu duk ya tashi sosai suna ta faman tambayan ya aka yi, ta mayar front camera ta ce,

Bakuwar FuskaTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon