15- Heart Transplant

603 90 4
                                    


Jin ta take baki daya a wata duniya, duniyar farin ciki, duniya mai cike da walwala. A rayuwarta, idan aka cire yarintarta, ba za ta taba tuna ranar da ta shiga farin ciki irin wanda take a kansa ba yanzu. Sai kuma ta runtse idonta, tana kokarin tuna silar komai, silar yi mata dashen zuciyar da tun da aka yi mata shi ta kamu da tsananin soyayyar Ishraq Sulaiman.

Flashback...

Da karfi take jawo numfashi, tana yi tana huttai, tana jin wani irin nauyi a tsakanin kirjinta. Ita kadai ce a dakinta, da tsakiyar dare kimanin karfe ukun dare. Sosai ciwon ya ci karfinta, ta yunkura domin ta dauko maganinta amma ina, ta kasa, ji take jikinta ya mata tsananin nauyi, nauyin da ta kasa ko da motsa gangar jikin nata.

A hankali ta kokarta daga hannunta, ta jawo side lamp (fitilar gefen gado) da ke girke bisa side drawer din ta, cikin cijewar labba, ta buga side lamp din da karfi, yanda ta tabbatar da dole sai an jiyo karar.

Cikin sa'a kuwa tamkar a mafarki Mommy ta jiyo, sai dai ta rasa takamaimai daga ina wannan kara ta fito, haka Aliyu ma ya yi saurin fitowa daga dakinshi, har suka yi kicibus da Mommy tana tambayan lafiya yana tambayan lafiya.

"Wata kara na jiyo mai karfi Aliyu. Ban san daga ina ta fito ba.

"Ni ma ita ta fito da ni..." kafin ya kai aya a zancenshi, suka jiyo huttan da Mahboobah ke yi, da karfin gaske.

A hanzarce duk suka isa dakinta, a halin da suka same ta sun gigita matuka, ganin ta unconscious ba karamin razana su ya yi ba.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Shi Mommy ke maimaitawa a bayyane, yayin da hawaye mai gumi ke sintiri a bisa fuskarta, ya wanke duk kumatunta.

"Aliyu, maza dauke ta mu tafi asibiti."

Da hanzari Aliyu ya ciccibe ta, Mommy kuma ta yi gaggawar fita ta dauki makullin mota, sannan ta biya ta dakin Fareedah ta tashe ta suka fita tare. Tsabar gigicewa gidan ma a bude suka bar shi. Halin da Mahboobah take ciki, dukkanin wanda yake da dison imani a tsakanin kirjinshi sai ya tausaya mata. Ga wanda ya taba ganin fitar ran wani mutum, to zai iya rantsuwa da Allah cewa rayuwar Mahboobah ce ke kai da komowa, take neman rabuwa da gangar jikinta.

General hospital suka wuce kai tsaye, inda take ganin likitanta. Sai dai a rashin sa'a, ba su same shi ba a lokacin, ba ya ma garin, ya je Potiskum wani aiki.

Ganin halin da Mahboobah ke ciki ya sa likitan da suka samu ya tausaya mata, ya ce zai hada su da Doctor Sadeeq wanda yake cardiologist ne, wato likitan zuciya. Sai da ya fara ba ta first aid (taimakon gaggawa), kafin ya latsa kiran Doctor Sadeeq. Duk da yake tsakiyar dare ne, amma hakan bai hana bugu guda Doctor Sadeeq ya dauka ba.

Da sallama suka gaisa, sannan ya ce "Doctor Sadeeq taimakon nan dai da ka saba yanzu ma shi za ka yi. Patient gare ni unconscious, kuma likitan da ta saba gani Doctor Kabir ya yi tafiya. Ka taimaka ka zo ka duba ta, in da rabon ci gaba da rayuwarta, ka ceto ta, Allah ne kadai zai biya ka."

Ajiyar zuciya Doctor Sadeeq ya sauke. "Yanzu haka ina asibiti tare da iyalina, labour take tun da yamma ga shi har yanzu ba ta haihu ba, hankalima ya gaza kwanciya Doctor Khamis."

"Taimakawa za ka yi Doctor Sadeeq. Ni dai nan I did my very best (na yi bakin kokarina). Am not a cardiologist you know (ka sani ni ba likitan zuciya ba ne), ban san komai ba a kai sai abin da ba za a rasa ba. Na dai ba ta nitroglycerin. Idan a yanzu ta farka ba ni da sauran idea na abin da zan mata."

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now