38- Love❤️

639 61 7
                                    

Ringing din wayarta ta ji, tana dubawa ta ga Muhammad ne. Ranta a bace yake, zuciyarta babu sanyin da za ta iya yin magana da kowa a yanzu. Ta kifar da wayar tana juya kanta. Gama ringing din ke da wuya ta sake ji yana kira. A wannan karon ma kin dauka ta yi tana tsinkewa ta ji karar shigowar text message...

'Mamanmu ina wuni? Ya aka ji da fama da mu? Ina kanwata Ameerah? Ina gaishe ta. Fatan dai lafiya kuke.'

Dariya 'Mamanmun' da ya kira ta da shi ya ba ta. Ta saki murmushi a ranta tana jinjina barkwanci irin na Muhammad kamar ba dan gidan sarauta ba yadda ya fada mata. Don yan sarauta an san su da kamewa da shan kamshi, ga kuma miskilanci.

Ba ta mishi reply ba sai data da ta kunna tana ganin yadda sakuna ke rige-rigen shigo mata kasantuwar ta jima rabon ta da hau whatsapp, tun kafin ta fara jarabawa. Sallamar Ameerah ta ji ta daga kai ta kalle ta. Duk ta marairaice sum-sum ta zama kalar tausayi.

"Ameerah what is your problem?" Ta tambaye ta tana bude hannuwanta duka biyu alamun ta zo ta shiga jikinta. Kin zuwa ta yi Ameerah sai ma kwakkwabe baki da take yi.

"Zo mana ina wasa da ke ne?" Ta fada cikin sigar fada. Da gudu Ameerah ta shiga jikinta tana fasa kuka.

"To ya isa haka yi shiru, kin san ba na son kuka. Fada min me kike wa fushi?"

Sai da ta dago daga jikin Mahboobah sannan ta ce "Ba ke ba ce ba kike ma Daddyna fada..." Ta sake fashewa da wani kukan.

Har ga Allah ba ta san cewa Ameerah na cikin dakin ba sadda take mayar wa da Ishraq magana. Ita dai ta ga sadda Mommy ta kore ta da wayarta ta ce ta je daki ta yi game. Amma ba ta san sadda ta dawo ba da ba ta yarda ba ta yi a gabanta, tun da halin yara akwai su da riko, kuma suna jin ciwon wani sashe daga cikin iyayensu ya kuntata ma wani sashen.

"Ameerah, abin da na ma Daddynki wallahi ko rabi-rabin wanda ya yi min a baya ban yi ba. Amma ki yi hakuri ki yafe min kin ji, ba zan kara ba."

Murmushi Ameerar ta yi tana kara shiga jikin Mahboobah, a wannan karon rungume ta yi.

"Happy?" Mahboobah ta tambaye ta ganin ta saki.

"Yes." Ta ba ta amsa tana daukar wayarta.

"Ammi ina son yin waya da Mamama." Ta fada tana mika mata wayar da nufin ta kira mata Fareeda a waya, ashe mistakenly ta latsa recent call kiran Muhammad ya shiga. Kafin Mahboobah ta yi gaggawar kashewa tuni kiran ya isar ma Muhammad, da gaggawar shi sai ga shi ya kira ta.

Duk da ba ta so dauka ba amma dole ta daure ta dauka suka gaisa.

"Mamanmu ina ta kiranki in kwashi albarka amma ba ki dauka ba."

"Muhammad Saddam." Ta fada tana dariya. "Ba ka gajiya da tsokana. To Ameeran ma ba Mama take kira na ba ai."

Dariyar ya yi shi ma yana jin dadin muryarta. "Okay fada mun me take kiran ki da shi?"

"Ba zan fada ba..."

"Ammi ba za ki kira mun Mamama ba ko?"

"Shi kenan ma na ji. Haba Ammi ashe ma kina tare da kanwar tawa shi ne ba za ki hada mu ba mu sada zumunci a matsayinmu na Yaya da Kanwarsa."

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now