24- Rainon Ciki

564 57 4
                                    

Kamar yadda suka sanya kwanakin tafiya Saudia, haka kwanakin dawowar su kasar Nigeria ya juyo. Jin ta take tamkar a bisa gajimare, wani irin nishadi na lullube ta, yana daukar ta daf, yana ajiye ta a cikin duniyar nishadaddu. Sosai ta ji dadin zaman kasar Saudia, sun yi kwanaki hudu a birnin Madina, daga nan suka wuce Makka, inda suka sauke umrarsu. Sai dai dadin da take ji a yanzu da take zira kafarta daga cikin kofar jirgi, ji take tun da take a duniyarta sau daya ta taba jin irinshi. Kanta ta daga sama, ta kalli sararin samaniya, tana mai jinjina girma da buwayar Allahu gagara-misali, ta yadda Ya zana baiwa a cikin kwakwalwar mutumin da ya fara kirkirar jirgin sama. Kafin ta dawo da kallon ta ga mutanen da ke zagaye da jirgin, kowa yana jiran saukar dan'uwanshi.

Fuskarta ta shafa da tafin hannunta, tana bude idanuwanta da ke sauka ga mutumin da ta fi kauna a duk duniyarta bayan mahaifiya da siblings dinta. Gabanta take jin yana tsananta bugawa, tuna cewa ita kadai ce ke haukarta, kewarshi ta yi, sai dai ta tabbata shi bai yi ba. Matsawa ta yi kusa da shi, tana jin yadda zuciyarta ke ruruwa da wutar kaunarshi. Rashin ganin shi da ta yi na sati biyu, ji take tamkar an zarce watanni uku ne ba ta dora shi a idanuwanta ba.

Tun da suka tafi, ko sau daya Ishraq bai taba kiran Mahboobah da wayarta ba. Sai dai idan sun gaisa da Mami, yana cewa ta ba ma Boobah wayar, don ya san halin Maminsa, tana iya gane yanayin alakarsu, duk da a hakan ma ta sanya ma abun alamar tambaya. Sau daya da Mamin ta tambaye shi me ya sa ba zai kira Mahboobah ba a wayarta sai dai da tata, ce mata ya yi

'Duk daya ne Mami.'

Tun da yake waya da Mahboobah ko sau daya bai taba tambayar ta lafiyarta ba, ballantana ta abin da yake cikin cikinta. Abun yana mata ciwo matuka. Domin kuwa, ba ita ta dasa ma kanta cikin ba. Halittar Allah ce, Ishraq sanadinshi. Ita duk zaton ta yadda take ganin miji na ririta matarshi yayin da take da juna biyu a cikin fina-finai ko kuma littattafai, ta dauka ko rabinsa za ta samu a wurin Ishraq, duk da ta san yadda yake tsanarta. A wasu lokutan takan zubar da hawayen da ita kanta ba za ta ce ga dalilin zubar su ba. Sai dai ta san ba su rasa nasaba da rayuwar da ta tsinci kanta a cikinta, rayuwar da take da tabbacin a cikinta za ta dauwama, tun da ta zabi zaman aure da Ishraq Sulaiman.

Ranar farko da Ishraq ya ce da Mami ta ba ta wayar, bayan ta karba ce mata ya yi,

'Ki rinka kirkira maganar fadi idan a gaban Mami kike. Ko kuma ki rinka tashi ki bar wurin, ki yi shiru har sai lokacin da na ga dama na kashe wayar. Ba ni da shaawar jin muryarki KK. Ko kadan ba ki kasance a sahun mutanen da nake jin ko da motsin fitar numfashinsu zai shige ni ba.'

A ranar ta yi kukan da ta jima ba ta yi irinshi ba. Ko da Mami ta tambaye ta dalilin kukan, sai ce mata ta yi mahaifinta ta tuna. Mami ta yi ta mata nasiha, a karshe ta ce da ita ta dage da yi mishi addua.

"Sannunku da isowa Mamina. Na yi kewar ki sosai."

Maganar Ishraq ce ta dawo da ita a duniyarta. Tana matse idanuwanta guntun hawaye na sauka daga cikinsu. Hannunta ta sa ta goge, tana kirkiro murmushin da ko kadan bai da alaka da nishadi.

"Yauwa likita. Mun same ku lafiya?"

"Lafiya nake Mami. Mu karisa wajen parking, motar tana can." Har ya yi tunanin wucewa, sai kuma ya tuna tare suke da Mami kuma tana lura da yadda ko kadan bai mayar da hankalinshi kan Mahboobah ba, hakan ya saka shi kirkiro murmushin dole, yana kallon Mahboobah da ta tsare shi da idanuwanta, tana ganin yadda ya kara yi mata kyau.

"Sannunku da hanya Boobah." Kadai ya iya samun fadi. Duk yadda ya so ya matso wata maganar a gaba kasawa ya yi. Cikinta ya kara girma a kan yadda ya gan ta kafin su tafi. Fuskarta ta kara yin munin da shi kadai ke ganin shi.

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now