27- Gudan Jini

550 64 9
                                    

Jerangwama take yi Mommy, daga bakin tv zuwa 3 seater, hannuwanta duka biyun dafe da bayanta, fuskarta shimfide da bayyananniyar damuwa.

"Mommy, dole ne a san abun yi. Ba zai yiwu ba mu zira ido muna kallo soyayya ta nemi nakasta zuciyar Boobah. Wallahi sam mutumin can ba mutumin kirki ba ne. Na yi da na sanin biye wa Mahboobah tun tashin farko har aka daura aurensu."

Gyada kanta ta yi Mommy, "Rubutaccen al'amari ne Aliyu. Da ma can Allah Ya zana alkalamin kaddarar auren Ishraq a rayuwar Mahboobah. Ko mun so ko mun ki dole sai an samu rabon Ameerah a tsakaninsu. Amma ni ina ganin, abin da ya aikata muku yau bai yi girman daukar masa hukuncin da kake da niyyar yi ba. Hakuri..."

"Mommy..." Ya fada yana takowa kusa da ita. "Har sai yaushe ne kalmar 'hakuri' za ta fice daga bakin iyaye yayin da aka cuzguna wa ya'yayensu a gidan aure? Mommy har sai yaushe ne za a rinka bin hakkin mataye? Me ya sa kalmar 'hakuri' ta zama tamkar abar ado ga iyaye?"

Ajiyar zuciya ta sauke Mommy. Yaro yaro ne, ta fada a zuciyarta. "Hakuri abu ne mafi girman daraja a duniyarmu Aliyu. Hakuri shi ne jigon zaman aure, hakuri yana sama da dukkan komai, hakuri na sama da soyayyar da ake ganin dominta ake gina aure." Ta dafa kafadarshi. "Ko ka taba ganin a nasihar aure an ce a je a yi ta zaman soyayya? Ba a fadin haka Aliyu. Sai dai a ce a je a ci gaba da zaman hakuri, saboda an san shi ne ginshikin rayuwar auren dukkanta, shi ne jigon zaman aure. Matukar aka ce za a zabi zaman aure babu hakuri, to ina mai tabbatar maka da cewa ba zai yi karko ba. Laifi kadan za a rinka daukar zafafan hukunci ga juna. Amma idan aka yi hakuri, sai ka ga an zauna lafiya."

"Amma Mommy wani hakurin da shi gara babu shi. Mommy kina ina ake yin hakurin da ake kuntata wa zukata? Sai ki ga an maka abu ka shanye, ka yi hakuri, amma yana nan a cikin zuciyarka zaune daram. Irin wannan hakurin ne ke illata zuciya. Irinshi ne sai dai a wayi gari ki ga mace da cutar hawan jini, ciwon zuciya, ko kuna kawai ta girde ta fadi. Irinshi ne depression ke kama mata."

"Haka ne. Na yarda da duk kalamanka. Sai dai kuma yawaitar hadisan da suke magana a kan muhimmancin hakuri ya take wannan maganganun naka Aliyu. Ka yi hakuri kawai Mahboobah ta koma gidan mijinta. Tun farko ita ta ji za ta iya ta zabi zaman aure da shi duk da ta san ba ya son ta. Da zurfin ciki irin nata kuma duk abubuwan da suke faruwa a gidan aurenta daidai da rana daya ba ta taba samun wani da su ba. Don haka tashi za ka yi ka mayar da ita. Ta je ta ci gaba da zaman hakuri tun da haka ta ga ya fiye mata."

Runtse idanuwanta ta yi Mahboobah. A duk kalamansu babu wanda ta tsinta sai maganar Mommy ta karshe cewa ya tashi ya mayar da ita. Wani irin dadi ta ji ya sauka a kasan zuciyarta, wanda ta kasa boye shi har sai da ya bayyana a saman fuskarta. Ta saki murmushi tana dan cije harshenta.

"Ka gani ko. Kalli fuskarta ka ga dadin da ta ji don na ce ka mayar da ita. Alamun duk kukan nan da take yi don ka ce ba za ta koma ba har sai an tattauna da dangin Ishraq ne. Sai ki tashi ku tafi ai." Mommy ta fada tana mayar da dubanta ga Mahboobah.

Sai kuma ta ji wata irin kunya ta tsarga ta, ta lullube ta. Ba ta san yadda aka yi ta yi murmushin ba. Da ta san sadda zai fito da ta yake shi ya tsaya a cikin zuciyarta. Kasa motsawa ta yi saboda kunya.

"Ki tashi mu tafi." Fareedah ta fada cikin sanyin murya tana mika Ameerah ga Goggo da ke zaune ake komai a gabanta. Babu musu ta mike, ta rayata baby bag din Ameerah, sannan ta je dakinta ta kira su Haneefa suka fice.

*
"Ka ji tsoron Allah Ishraq. Ka sani cewa hakkin Mahboobah ba zai taba barinka ba. Duk yadda kake ganin ka ci bulus don ka zalunci marainiyar Allah to wallahi ba ka ci ba. Matukar ba ka nemi gafararta ba kuma ka gyara kuskurenka to wallahi sai Allah Ya bi mata hakkinta."

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now