45- Boobahn Ishraq

603 58 32
                                    

Mommy na ganin Mahboobah na kuka bilhakki duk sai ta kidime. Hankalinta ya tashi, gudun kar a koma 'yar gidan jiya, ga shi ta ma likita alkawarin za su kiyaye shiga yanayin damuwa da take yi.

"Boobahna me kuma ya faru?"

Gyada kanta ta yi tana kallon Mommy. "Ba zan iya sake komawa gidanshi ba, ba zan iya ba Mommy."

Daram! Ishraq ya ji gabanshi ya fadi. A wani baren na zuciyarshi kuma tsananin tausayinta yake ji, yana tuna wahalhalun da ta sha a gidanshi, kyara, tsana da kuma tsangwanar da ya rinka nuna mata, dole ne ma Mahboobah ta ce ba za ta koma gidanshi ba.

"Ya isa haka to daina kukan kin ji. Babu wanda zai yi miki dole, in dai ba kya son shi ba za ki koma gidanshi ba. Mu da muke fatan ki samu sauki zuwa gobe a sallame ki shi ne kuma kike kuka. Kwantar da hankalinki, matukar ba kya son Ishraq to ba za ki aure shi ba. Wanda kike so shi za ki aura." Mami ce ta yi wannan maganar, duk da a ranta tana jin babu dadi, su ga samu su ga rashi. Amma ba ta da zabin da ya wuce ta fadi haka, ba ta son zama mai son zuciya. Mahboobah abar tausayi ce, baki daya rayuwarta abun a tausaya mata ce.

"Ina son shi, amma ba zan iya komawa gidanshi ba, har yanzu ba ya so na, yanda bakinshi ya furta k'i a kaina, duk yanda ya so kiyayyar nan ta koma So ba zai yiwu ba."

Har kasa Ishraq ya sunkuya a gabanta. Bai ko ji kunyar Mommy da Mami ba, ya share gumin da ke tsatssafowa daga goshinshi, ya ce "Tuni na karyata wannan zancen na Hausawa Mahboobah, cewar bakin da ya furta k'i ko ya furta So karya ne, to wannan zancen ba gaskiya ba ne. Ni dai na furta miki k'i a baya, ga shi kuma yanzu kaunarki ta yi kawanya a zuciyata. Babu wata mace da nake son kasancewa da ita bayan ke Boobah. Babu macen da zan iya rayuwar aure koma-bayanki. Ki amince ki share mini hawayena, na yi alkawarin share miki naki hawayen, na baya, na yanzu, da kuma na gaba wanda ba na ma fatansu, zan kokarta yaki da su ta yadda za su nisance ki, ke da hawaye sai dai na farin ciki, da izinin Ubangijin al'arshi mai girma."

"Ba zan iya ba Likita." Mahboobah ta samu furtawa, cike da rauni, tana jin cewa ba gaskiya ba ne kalamanshi.

"Hajiya Mariya ina ga ko mu ba su wuri su tattauna." Mommy ta fada, tana karbar Baby Hoodah daga hannun Mahboobah.

"Ba a yi haka ba Maman Fareedah, don Allah kar mu tauye wa yarinyar nan 'yancinta. A bar ta da ra'ayinta."

Mommy ta yi murmushi tana kallon Mami, "Babban 'yancin nata shi ne mu bar su su yi magana a tsakaninsu. Ita ba yarinya ba ce, Ishraq bai isa tursasa ta ba idan ba ta yin niyya ba. Don haka mu ba su wuri din. Ku hanzarta kafin likita ya zo second roundup."

Daga haka Mommy ta fice, Mami ma ta mara mata baya.

"To Baban soyayya sai a san yanda za a yi a shawon kan kanwata, banda kuma kalaman yaudara." Dariya Ishraq ya yi yana kai wa Noor duka a kafada.

"Ai ni ma kanwata ce." Ishraq din ya fada yana murmushi. Muhammad Saddam dai dauke kanshi ya yi daga gare su, wani irin kishi ke ratsa shi, yana jin ba zai iya jurar wannan lamarin ba.

"Bari in fita, zan jira ku a waje."

Noor ya kalli Muhammad Saddam da fadin. "Ai ba za ka bar ni a nan ba ni ma, tare za mu wuce." Suka kama hanyar fita daga Dakin.

Daga gefen Mahboobah Ishraq ya zauna, yana duba karin ruwan da ke rataye, tunda ya kare wata nurse ta ce a bar ta ta huta tukunna har zuwa anjima.

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now