42- Ciwon So

552 65 23
                                    

Wayarta da ke hannunshi ya ji ringing dinta. Ya duba ya ga an rubuta LOML❤️. Kamar kar ya dauka da ya ga sunan, sai kuma ya ga ya kamata ya dauka din, saboda makusantanta su san halin da take ciki.

Ya dauka da sallama a bakinshi, sai ya ji muryar dattijuwar mace ta amsa sallamar. Ya gaishe ta cikin girmamawa ta amsa. Tana kokarin tambayar Mahboobah don ita a tunaninta ma ko shi ne Muhammad Saddam, ta ji ya ce

"Dazu ne a kan hanyata daga Hunkuyi zan tafi Kaduna, a kan express Zaria na ga mai wannan wayar zube a kasa, mutane kowa yana tsoron tinkararta. Shi ne na faka motata na isa inda take, na kanga kunnena na ji bugun zuciyarta. Sai na dauke ta na kai ta asibiti. Yanzu haka tana karkashin kulawar ma'aikatan lafiya ne."

"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un!" Mommy ta fada cikin kidimewa. "Na gode sosai da taimako bawan Allah. Kuna wace asibiti ne? Ga mu nan zuwa in shaa Allahu."

Cikin kwantar da hankali ya ce "Kada ki daga hankalinki Mama. Ciwon ba wani mai tsanani ba ne. Da yardar Allah ma kafin ku iso ta gama warwarewa. Yanzu ma tana barci ne. Zan tura miki text na address din asibitin."

Sai kuma Mommy ta samu kanta da tsorata. Idan fa wani macuci ne ya cutar mata da Mahboobarta kuma yake son hadawa da danginta? Ba ta san sadda hawaye ya hau sintiri a saman fuskarta ba. Ta ma rasa ta inda za ta bullo ma lamarin.

Fahimtar ta tsorata da ya yi ne ya sauke ajiyar zuciya, tuna cewa asibitin sanannen asibiti ne, duk wanda ya san Zaria to ya san Almadinat Hospital.

Ya tsinke wayar yana tura mata sunan asibitin hade da address dinshi.

Aliyu ta kira a waya, ta ci sa'a daidai zai shigo gida sai bai dauki wayar ba, jin muryarshi kawai ta yi yana sallama.

A tsorace ta isa gabanshi tana labarta mishi komai. Shi din ma hankalinshi ya tashi.

"Zuwa Zaria ya kama mu Aliyu." Ta fada cikin kuka.

"Ki daina kuka Mommy in shaa Allahu za ta samu sauki. Ki dauki abin da za ki dauka mu tafi."

Purse dinta kadai ta dauka da ma wayarta na hannunta. Suka fice daga gidan.

"Lokacin tashin Ameerah daga makaranta ya yi. Mu biya mu dauke ta Mommy?"

A yanda ta matsu ta yi tozali da Mahboobah ji take idan aka tsaya daukar Ameerah an bata lokaci. Cewa kawai ta yi ya kira Ishraq ya dauke ta sai ya wuce da ita can wurin Mami, in ya so daga baya an dawo da ita.

Hanyar Zaria suka kama, bayan sun isa ta kira lambar Mahboobah mutumin ya dauka, ta ce ga shi nan sun shigo Zaria.

"To sai kun iso Mama." Ya fada yana komawa waje wurin parking space zaman jiran isowar su.

Da suka iso bai wahala ba wurin gane su. Ganin kamanninta da na marar lafiyar karara ya sa ya gane su ne. Ya isa gare su ya gaishe da Mommy, sannan ya mika hannunshi suka gaisa da Aliyu.

"Mun gode sosai bawan Allah. Mun gode da taimakon Mahboobah da ka yi. Allah Ya saka da alkhairi Ya biya ka dukkanin bukatunka na alkhairi. Thank you so much."

Da murmushi a saman fuskarshi ya amsa da amin, sannan ya yi musu jagoranci zuwa dakin da Mahboobah take. Har a lokacin bacci take yi ba ta farka ba. Saboda likita ya ce har da karancin barci ne ya assasa mata ciwon kai, ciwon kan kuma ya yi silar girdewarta ta fadi.

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now