29- Tsuntsun Da Ya Ja Ruwa...

537 63 15
                                    

Kafar wandon Ishraq ta kama, tana kuka mai cin rai, tana son gusar mishi da karairayin da azzalumi kamar yadda ta saka mishi suna ya shirya wa Ishraq din.

Fizge kafar wandonshi ya yi yana hada mata da mari mai zafi.

"Babu ta inda za ki iya karyatawa. Kin saba tambaya na za ki fita ki je gidanku ko wani wuri, amma kin taba ce min sai dare za ki dawo? Ba ki taba ba!
Wannan ma kadai wata hujja ce mai karfi.

Ban taba sanin mazinaciya ce igiyar aurenta ke rataye a wuyana ba sai yau. Na yi da na sanin aurenki, na yi da na sanin hada jini da ke Karfen Kafa!"

Jin maganganunshi take yi tamkar ya watsa mata tafasasshen ruwa. Tamkar an barbada gishiri a rubabben rauni ko kuma gyambo.

Fincikarta ya yi, yana jefar da ita can gefen kujera, fuskarta ta daki katakon hannun kujerar da yake royal ne masu cike da adon katako. Jin d'umi na bin fuskarta ya sanya ta sanya hannunta ta shafo, jininta ta gani kwance a hannun, tana kuma jin yadda yake barazanar shiga cikin idanuwanta.

Numfashi take saukewa da sannu da sannu. Idan da sabo ya ci a ce ta saba da bakaken maganganun Ishraq tun farkon aurensu har zuwa lokacin da ya daina yi mata su. A kullu yaumin ya yi mata wata bakar magana jin ta take sassanya a cikin zuciyarta. Komai zafin maganar da zai mata da sanyi take tarbarta. Sai dai a yau, a yau sabanin haka ne. Tukuki take jin zuciyarta na mata. Runtse idanuwanta ta yi tana mikewa, ta matsa a kusa da shi, ido cikin ido take fadin,

"Anya kuwa akwai zuciya a kirjinka Ishraq? Ka tuna da cewa kai namiji ne da ya kamata a ce ka tsaya ka binciki komai kafin ka zartar da hukunci. Ishraq, kafin ka kira ni da mazinaciya yana da kyau ka fara binciken gaskiyar lamarin. Da wuya idan kana tsoron Ubangijin al'arshi mai girma, wanda Ya shimfida adalci a tsakanin ma'aurata."

Da matsanancin tashin hankali da bala'i ya yo kanta. Wani marin ya sake dauke ta da shi.
Sai dai ba zafin marin ya shige ta ba sama da zafin kiranta da kalmar 'mazinaciya' da ya yi.

"Na sake ki saki daya, Mahboobah!" Uku ya so yi mata, da kyar ya iya kwabar zuciyarsa ya tsaya a dayan.

Kanta take gyada mishi. Tana son yin magana amma tana rasa ta inda za ta fara. Hawayen da take yi din kanshi ya kafe.

"Za ka yi da na sani Ishraq, a lokacin da da na saninka ba za ta amfane ka da komai ba. Sannu a hankali gaskiya za ta yi halinta. Na sani ba zan iya fitar da kaina ba, amma Allah'n da Ya halicce ni Shi zai fitar da ni. Ba zan ce ina nadamar aurenka ba Ishraq, domin kuwa ko a yanzu zan daga hannu a sama in gode wa  Ubangijin da Ya halicce ni, saboda Ya cika mini burina na aurenka Ishraq. Da na sani da nadama guda daya zan yi, shi ne na butulce wa maganar iyaye da dangina, na zabe ka a kan farin cikinsu, na zabi zama da kai duk da cewa ba su so."
Ta saki murmushin takaici, tana dorawa da "Alhamdulillahi da Allah Ya halicci Ameerah a tsakaninmu. Na gode miShi da Ya shimfida ta a tsakaninmu, rayuwar shekaru biyu da muka yi ba ta tashi a iska ba. Ko gobe zan yi alfahari tare da nuna ta a matsayin gudan jinina, gudan jininka, wadda muka haifa ta hanyar auratayya ni da kai.
Na sani Ishraq, na sani wannan video din da ka dauka don ka tallata ma duniya ni ne. Shi ya sa ka rinka yi kana daukar fuskata a daidai lokacin da nake rasa abun cewa. To ka sani, in dai mahaliccina Ya san gaskiyar abin da ya faru, bai zama dole sai duniya ta shaidi hakan ba. Karkarinta dai a ce zan rasa mijin aure ko? To ban damu ba. Aure ya shayar da ni giyar mamaki. Rayuwar aure ta karantar da ni darussa masu tarin yawa. Ko gobe ba na marmarin sake auren kowa har ranar da mutuwata za ta zo ta dauke ni."

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now