04- Funny Ameerah

830 85 1
                                    


Flash back- 4th January 2010

"Wai Ameera wace irin nawa ce kike da ita? Tun dazu kowa ya fito mu kadai ake jira, sai aike ake mun in fito kamar kaina farau diya mace. Na ba ki minti biyar idan ba ki fito ba sai da ki neme ni ki rasa."

"Ga ni nan zuwa fa Mama. Allah kuwa na gama komai fitowa kawai zan yi."

"Fitowa dai ai ba wani aiki ba ne idan kin gama. Ni dai na fada miki..."

Ba ta kai karshen zancen ba sai ga Ameera ta fito rike da karamar Ghana most go. Kyakkyawa ce ma shaa Allah. Duka a shekaru ba za ta wuce goma sha biyar ba. Fuskarta ta shafa hoda kadan sai kwalli da ya kawata idanuwanta. Ta yi dan digo karami a tsakanin girar fuskarta. Ta saki sassanyan dariyar da har sai da hakoranta suka bayyana.

 Ta saki sassanyan dariyar da har sai da hakoranta suka bayyana

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

"To Hajiya Mama ga ni na fito."

Dukan wasa Mamanta ta kai mata. "Ban san me ya sa ba yarinyar nan baki daya kin mayar da ni Kakarki."

"Toh Mama barewa a daji da wa take wasa in ba da ya'yanta ba?"

"Kanki dai ake ji." Daga haka suka kama hanyar barin gidan.

A kofar gidan Kawu Badamasi suka hadu. Sun tarar duk yan tafiya kowa ya zo su kadai ake jira. Har motar da za ta dauke su din ma ta iso. Bayan an gaggaisa ana kokarin shiga mota Ameera ta noke. Mama ta kalle ta hade da bata fuska tana son sanin dalilin nokewar tata. Kafin ta ce komai ta hango Nura daga can nesa ya jingina jikin bango. Murmushi kawai Mama ta yi, ta ce "Ai sai ki je wurinshi. Kuma wallahi kina bata lokaci sai dai ki ga motar nan ta tashi, don babu wanda zai tsaya jiran ki kuma."

Ba ta ko tsaya ta karisa jin zancen Mama ba ta gaggauta isa inda yake.

"Yah Nura ina kwana?" Ta furta tana kallon kwayar idanuwanshi.

"Yan matan Mama sai tafiya. Ina ta sauri kar in tarar kun tafi ai."

"Yah Nura ai dan in samu mu gana din ne ya sa na yi ta shiririta, sai da na ga Mama na neman tafiya ta bar ni sannan na fito." Ta kwashe da dariya.

"Lallai ma yarinyar nan. Kin kyauta dai duk da haka. Amma kar ki sake yin irin haka don ba zan ji dadi ba a tafi a bar ki."

"Yah Nurah duk sun gama shiga motar bari in je." Har ta juya za ta tafi ya kira sunanta.

"Ameera, ki kula mun da halittar halittarki. Ki kula mun da zuciya da gangar jikinki. Ki kula mun da dukkan dukkanki. Ina kaunarki Ameera."

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now