13- Love Story💙

637 63 4
                                    

Flashback...20th April 2010 (Komawa Baya)

Hawaye share-share kwance a saman fuskarta, ta saka dogon hijabinta sannan ta dauko 'yar jakar kayanta. Ta fito tsakar gida, ta samu Abbanta tsaye, Mama a kusa da shi. Ta dire jakarta a gaban Abbah, sannan ta rungumi Mama.

"Mama za mu tafi..." kuka ya ci karfinta, ba ta ko kai karshen zancen nata ba.

"Allah ya tabbatar da dukkan alkhairanSa a rayuwarki Ameerah. Allah ya sa wannan tafiyar ita ce silar farin cikinki. Allah ya yaye miki duk wani kunci ya musanya miki shi da alkhairi. In shaa Allahu zan kawo miki ziyara. Allah ya ba ki miji na gari. Allah ya yi miki albarka." Ita ma ta ji hawayen yana sauko mata.

Ameerah ta kirkiro murmushi, "Ka ga Hajiya Mama ana hawaye za a rabu da 'yar auta. Ashe dai za a yi kewar Ameerah sarkin kiriniya."

Dukkansu sun san dariyar nan tata ba ta kai ciki ba, yake ne kawai. Ita kokari take na ganin ta saisaita damuwarta, ko dan hankalin iyayenta ya kwanta. Sai dai ba ta sani ba, damuwar wanda bai cika saurin damuwa ba sam ba ta boyuwa. Duk yanda ta so pretending ba ya taba yiwuwa dole sai an gane mata.

"Mu je ko?" Abba ya kalli Ameerah yana kokarin daukar jikkarta.

"To Mama, saduwar alkhairi. A yayyafe mu." Ta yi saurin goge hawayen da ya sauko mata.

"Ba ki mun komai ba sai alkhairi Ameerah. Ku je, ki kula da kanki, ki kula da ibadarki, ki ji tsoron Allah a duk inda kike."

Ta jinjina kai hade da bin bayan Abbanta.

Kamar an ce su fita Mama ta duke a wurin tana kuka sosai. Tun da ta haifi Ameerah ko kadan ba ta taba yin nisa da ita ba. Koyaushe suna tare, su yi fada su yi dadi. Tana tsananin kaunar Ameerah, da ma su biyu ne ta haifa ita da Yayanta, wanda ya rasu sanadiyyar cutar sickler.
Ta shaku sosai da Ameerah, tana mata kaunar da ita kanta ba ta san adadinta ba. Hakan kuwa bai rasa nasaba da yawan kyautata mata da take yi, duk damuwa da kuncin da za ta shiga sai Ameerah ta yi kokarin warware mata, ta saka ta nishadi. Ameerah mutum ce har da rabin mutum. Yarinya karama mai zuciyar manya. Yau ga shi dalili ya yi dalilin rabuwa da tilon diyarta, ta tafi inda za ta jima ba su sake haduwa ba. Ameerah da wannan garin kuwa sai dai ziyara, kawunta ya ce a mayar da ita can dindindin, ko za ta samu sassaucin zuciyarta.

"Ya zan yi da kewar Ameerah?" Ta sake fashewa da wani kukan.

Da azahar suka isa garin Kaduna. Sun sauka a Kawo, daga nan suka hau keke napep ta idasa isa da su cikin Sabon Kawo. A cikin napep din ma sai da Abba ya sake yi mata nasiha. "Ki kokarta ki rage wa kanki damuwa Ameerah. Ki sani cewa dukkan bawa ba ya tsallake wa kaddararsa. Kuma kowanne mutum da kike gani akwai jarrabtar da Allah zai iya aikowa a saitin duniyarshi. Ki dauka cewa rabuwa da Nurah wani yankin jarabawa ne daga cikin jarabawoyinki na rayuwa. Ki ci gaba da addua tare da rokon zabin alkhairi. In shaa Allahu za a zana miki jarabawa. Idan ta yi kyau Yaya Mukhtar zai nema miki karatu, ki ci gaba da yi har Allah ya kawo miki mijin aure. Ina alfahari da ke Ameerah."

Ta saki murmushi. "Na ji dadi sosai Abba, ashe ni ma ina da rabon yin karatun nan da ban taba kawo ma raina yinsa ba."

Ya mayar mata da murmushin shi ma. "In shaa Allahu kuwa Ameerah."

Daga haka suka iso gidan. Abbah ya ba mai napep kudinshi sannan suka isa cikin gidan.

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now