11- Heart Breaking💔

615 68 5
                                    

Wishing myself a joyous birthday full of God's amazing blessings. My being alive and healthy today is as a result of none other than the almighty God. I'll forever be grateful to you, God. Happy birthday to myself.😻🥳🥳

Flashback...18th April, 2010 (Komawa Baya)

Da kuka ta farka, ta sa hannunta tana sharar ruwan hawayen da ya gama wanke mata fuska, tana cicije labbanta, da kyar ta samu ta bultso magana daga tsakanin labbanta,

"Mama...Mama don Allah ki fada mun mafarki ne nake yi. Ki fada mun ba gaskiya ba ne ba."

Mama ta taso ta iso bakin gadon da Ameerah take kwance. Ta dafa ta cike da soyayyar uwa da diya. "Ba mafarki kike ba Ameerah, dukkan abin da kika san ya faru to da gaske ya faru din. Sai dai ina so ki kwantar da hankalinki. Ki kokarta yaki da zuciyarki ta hanyar fatali da soyayyar Nurah, duk da na san ba abu ne mai sauki ba. Ki daure Ameerata."

"Ta yaya Mama? Ta ina zan fara zare soyayyar da jini da
zuciyata suka saba da ita? Ta yaya zan iya fatali da Yah Nurah bayan tarin shakuwar da zukatanmu suka yi? Wayyo Allahna, Mama ya zan yi?"

Kuka take sosai kamar ranta zai fita, tana wata irin shessheka mai ban tausayi. Mama ma sai ta ji hawaye na fito mata. Tun da ta haifi Ameerah idan aka cire kukan yarinta to ba ta taba ganin ta a irin wannan halin ba. Ba ta taba jin muryarta na irin wannan kukan ba. Yarinya ce mai kokarin boye damuwarta, mai kokarin danne kunci da bacin ranta. Duk yanda aka mata abu don ta hasala, ko alama ba za ta nunar ba. Za ta bi mutum da murmushi, a karshe har da barkwanci. Ta taba rasa Yayanta, ya rasu, amma ko a lokacin ba ta yi kuka irin wannan ba. Ta yi kuka sai dai iya ruwan hawaye ne, ita ta koma rarrasar Mama a wancan lokacin.

"Ameerah kina
raunata mini zuciya da wannan kukan naki mai cike da zallar ban tausayi. Kina kashe mini dan sauran kwarin guiwar da nake ganin ina da shi zan iya rarrasarki in kwantar miki da hankali. Na sani da ciwo. Da ciwo sosai Ameerah. Dole za ki yi kuka, ko don shakuwar da take tsakaninki da Nurah, tun kafin soyayya, tun a iya Malamin islamiyya da dalibarsa kawai. Amma duk da haka ba zan fasa ba ki hakuri ba. Ba zan fasa rokonki ki yi shiru ba, kar ki jawo ma kanki wani ciwon kina zaman zamanki."

Kokarin tashi zaune ta yi amma ta kasa. Mama ta kama ta ta tasar zaune, ta jingina da gadon asibitin da ya tsufa yake wata irin kara kamar zai karye.

"Ga fura nan Abbanki ya siyo miki kina bacci. Ya ce ki daure ki sha sai ki sha magunguna ga su nan tun dazu ya siyo da aka rubuta."

"Na koshi Mama..."

"Wane irin kin koshi kuma? Kwananki daya da rabin wuni a haka, ba ki ci komai ba. Na tabbata dole kina jin yunwa, dole. Daurewa za ki yi ki cuccusa ta haka nan ko ba dadi, don dai ki samu ki sha magani."

Ta gyada kanta wani hawaye na sake fitowa. "Mama Yah Nurah ya san ba ni da lafiya? Ya zo duba ni?"

Mama ta sauke ajiyar zuciya bayan ta share guntuwar kwallarta. "Ba na tunanin ya sani Ameerah. Kuma ma ko ya sani din ba lallai ba ne ya zo."

"Me ya sa?" Ta tambayi Mama cikin kuka.

Mama ta dan yi jim, kafin ta ce "Saboda an masa iyaka da ke. Iyayenshi sun zaba mishi wata a birni."

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now